Sashe 115
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gudu take bata ko dub Inda take jefa ƙafar ta ,
  Da ƙarfi ta tura ƙofar ɗakin tana shiga ta zuɓe a tsakiyar ɗakin tana sakin wani irin kuka marar sauti da yake tuƙowa daga ƙasan ruhin ta ,
  Cikin wata irin murya ta fisgo kalmar ,
  ALLAH NA TUBA , NA TUBA ALLAH , BAZAN SAKE BA ,ALLAH NA TUBA KA YAFE MIN ,
 Kuka take tana maimaita kalmomin nan jikin ta har tsuma yake ,
Ashe haka ne girman laifin da ta aikata batare da ta sani ba ? Ashe ita É—in me tarin zunubi ce ? Ashe baza ta samu wani alkhairi ba arayuwar ta tunda tayi zina ,
Ta jima a zaune a wajen tana kuka har duhun dare ya shigo , zuciyar ta ta tsorata iyaka , neman yadda zata yi Allah ya yafe mata take yi , sai dai bata san yadda zata yi Allah ya karbi tuban ta ba , ji take kamar zata mutu ,
Tashi ta sake yi tana gama hanya saboda kukan da ta É—auki lokaci tana yi yasa kan ta sarawa tare da fara jin jiri ,
tana gama hanya ta fito , bata ko dubi ɗakin samy baɓy da kiɗa ke tasowa ta cikin sa alamun da ke nuna ta dawo gidan ba , ta sake fita ,
hanyar gidan malama maryam ta sake ɗauka ,
 tana so ta san yadda zata yi Allah ya yafe mata , tana so ta san yadda zata yi ta gyara kuskuren ta ,
a falo ta tarar da malama maryam tare da iyalan ta suna cin abincin su na dare ,
  Babu sallama ta rakaɓe daga bakin ƙofar gami da sakin kuka me ciwo ,
hankali tashe malama maryam ta tsame hannun ta daga abincin da suke ci ta miƙe , ta zo ta kama yakaka ,
  Tambayar ta take lafiya ?meye ya same ta ? Ko wani abu ya samu antyn ta ? Daman yanzu take so idan ta gama cin abinci lubna ta raka ta gidan nasu ta duba ta domin É—azu ta fita bata cikin nutsuwar ta yanzu kuma ta dawo tana kuka , shin menene yake damun ta ?? Â
  Cikin muryar ta da kuka ya fara disarwa , tace nayi ZINA malama maryam , ki taimake ni ki faɗa min yadda zan yi Allah ya yafe min , ban sani ba malama maryam wallahi ban sani ba ,
 Ta shi , ta shi mu shiga ɗaki ki nutsu ki min bayani yadda zan fahimce ki ,
  Ta kama hannun ta zuwa ɗaki ta zaunar ta bakin gado , ina sauraran ki me kike son faɗa min yakaka ?
Tiryan tiryan , yakaka ta fara bada labarin tun daga farkon haɗuwar ta da yarima har yanayin yadda abubuwa suka kasance har zuwa yadda alaƙar ta da samy baby da yadda ta yaudare ta ta zo da ita garin abuja ta baro ɗanyar jaririyar ta tare da makauniyar ƙanwar ta, bata idasa ba malama maryam ta katse ta ,
Kin yi kuskure yakaka , kin yi kuskure , kin yi kuskure ,! Kaicho Â
  wani irin tausayi chakuɗe da bacin rai take ji cikin ran ta , tamkar wata makusanciya a gareta ce ta aikata abubuwan da yakaka ta aikata ,
tun farkon fara koyar da yarinyar ta fahimcin tana da raunin sani sosai da sosai game da addini , kusan ma bata san kome ba , shiyasa ta É—aura aniyar ganin ta kawo sauyi ta fidda ta daga duhun jahilci , cikin rashin sanin ta ashe jahilci tare da rashin wayon yarinyar har ya kai haka ( Bata san menene zina ba ) ? Ta yadda aka yi amfani da jihilcin aka cutar da ita cuta mai tsanani irin haka ?
Kukan da yakaka take ya tsansnta ganin shirun malama falmata ya É—au lokaci tare da bayyanuwar matsanancin tashin hankali bisa fuskar ta ,
 ALLAH zai yafe miki yakaka , muddin kika nemi yafiyar sa tare da niyyar baza ki sake komawa ga aikata saɓo irin wannan ba , ALLAH me yawan gafara ne ga bayin sa ,
Duk da cewa akwai bayanai daga malamai game da mutumin da ya aikata saɓon Allah alhalin bai san cewa sabon nan me girma bane da zai iya kai me shi ga shiga wuta ,ko kuwa bai ma san saɓo bane baki ɗaya, akwai hukunce hukunce , hukunci na farko shine , Shi JAHILCI ba'a uzuri da shi, sai dai cikin wannan hukuncin akwai bayanai da suke nuna akan karbi uzurin JAHILI , idan ya kasance gurin da ka tashi babu addini , babu malamai masu koyarwa ,ko kuwa an hana ka damar fita neman ilmin kuma ba'a koyar da kai ba a gida , to za'a iya yi maka uzuri da wannan , amma idan gurin da kake akwai addini akwai malumma , sai kaƙi fita ka nemi ilmi kasan hukunce hukuncen addini kayi zaman ka cikin jahilci to wannan baka da uzuri a addini , jahilcin ka ba uzuri bane ,
to amma idan ka rasa damar samun ilmi ne , akwai hadisin manzon Allah sallalahu alaihi wa sallam da yake cewa :
   Allah ya ƙetarar da Al'umma ta abu uku , ma'ana ya yi musu afuwa akan abu uku , na farko shine mutum yayi abu cikin rashin sani , na biyu mutumin da ya aikata wani kuskure akan mantuwa , sai na uku wanda aka tilasta ma sa aikata saɓo, !
To idan aka yi duba ga wannan hadisin za'a yiwa mutumin da duk ya aikata wani saɓo cikin rashin sani , uziri a sassauta masa , sannan shi kuma yayi tuba zuwa ga Allah , tsarkakaken tuba ,
Manzon Allah yana cewa : duk wanda yayi tuba na gaskiya to zai kasance kamar bai taɓa aikata wannan Zunubin ba , amma wanda yake tuba alhali yana komawa ga aikata zunubin sa to tamkar yana yiwa Allah izgili ne .
kiyi Tuba na gaskiya yakaka tare da niyyar baza ki sake kusanta kan ki ga aikata ZINA ba a rayuwar ki , Allah zai yafe miki ya wanke ki a idanun Al'umma domin Laifin shi kika yiwa ,
Sannan , ki tashi ki nemi ilmi ki kuma yi aiki da shi idan dama ta samu gare ki kome ƙanƙantar sa ki koyar da ilmin da yake gare ki domin sauran Al'umma su amfana ,
shiriya ta zo miki hasken ilmi ya zo miki ki sa hannu biyu ki karɓe su ƙwarai akwai falala tare da samun dacewa a cikin su , ki manta da rayuwar baya ki himmantu wajen neman gafarar ubangiji akan saɓon da kika wanzu kina aikatawa , da fatan kin fahimce ni ??
bata amsa ba illa hannu da ta kai ta rungume malama maryam , idanun ta na zubar ƙwallar da ita kaɗai ta san dalilin sauƙar su a daidai wannan lokacin
Godiya ta dunga jerowa malama maryam har lokacin da ta sanya ƙafar ta tana barin gidan lokacin dare ya fara shiga karfe goma saura ,
kan titi babu kowa garin ya sake ɗaukar sanyi , a hankali take tafe iska yana ɗaga hijabin ta , tayi zurfi cikin tunani , daki-daki take tuno kome da ya dunga faruwa a rayuwar su ita da ƙanwar ta ,
tana so ta zargi iyayen su akan killace su a gida da suka yi suka hana su neman ilmi , sai dai so irin na tsakanin ɗa da iyayen sa ya mata dabaibaiyi yaƙi bata dama , ji take suna da wata hujjar su , babu shakka akwai dalili ,
tunanin falmata da baby mama yayi mata dirar mikiya , wata irin kunyar falmata ta ji tana nuƙurƙusar ta , yaya zata Ji ranar da duk ta san irin kuskuren da tayi har ta samar da baby mama ta gudu ta bar mata ita ? Wataƙila daga ranar zata fara tsanar ta ,
tsoro take ji tsoron girma ya zowa baby mama ta samu sani akan irin ta hanyar da aka samar da ita , ? Me zata cewa waÉ—annan bayin Allah biyu ??
Lalle wajibi ne a gare ta ta nemi ilmin addini ko domin ta samun ƙarfin guiwar da zata iya fuskantar su tare da tarin hujjoji da bayanan da addinin ya tanadar domin ta gamsar da su ta kuma wanke kan ta a idanun su su san cewa ta aikata kome ne cikin DUHUN JAHILCI ,!
Ko zasu fahimce ta ? Ko falmata zata yadda ta cigaba da riƙe ta a matsayin ƴar uwa masoyiya ? Ko baby mama zata yadda da ita a matsayin uwa ?? Yaushe wannan ranar zata zo ? Zata zo nan kurkusa , ko sai bayan shuɗewar tsawon wani lokaci ? Abun da ta riga ta sani muddin su na raye wannan ranar zata zo ,
YARIMAN MARAÆŠI ,
Zuciyar ta ta auno mata da sunan sa da kome da ya wakana cikin rayuwar ta a wannan gaɓar shine sanadi ,
bata gan shi ko kusa tare da duhun jahilci makamancin nata ba , kome da shi yayi mata yayi ne cikin ilmin sa ,da sanin sa ya aikata Zina da ita ,
zuciyar ta take ji tana wani irin buÉ—awa da sabon yanayin da yake shigar ta akan sa da sabon matsayin da ya kamata ta ajiye shi tun farko a ran ta ,
Tunowa ta fara yi filla filla da farkon haɗuwar su har zuwa ranar ƙarshe da ya kore ta daga motar sa a tsakiyar titi tana kuka , yayi tafiyar sa ya bar ta har yau bai sake waiwaiyar ta ba ,
tabbas shi macuci ne azzalumi agare ta bai chanchanta da samun soyayyar ta ba ko kaÉ—an ,