← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 180 OF 269

Sashe 180

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A firgice ya waigo idanun sa cikin nata da yake iya hango ƙiyayya da tsana masu ɗinbin yawa , ji yayi kamar ya durƙusa guiwa biyu ya roƙeta kadda ta fasa sirrin dake tsakanin su a yanzu . 

Da sauri ya mayar da ganin sa ga Falmata wacce ya ga ta sunkuyar da kan ta yana iya hango bayyanar wani irin yanayi a tare da ita ,

"Na'am Fatima yace ,

Falmata wacce ƙiran sunan sa da Yakaka tayi ya ankarar da ita tare da tuno mata da matsayin Youssouf ɗin Na asali ga Yakaka , jikin ta yayi sanyi da tasowar wani yanayi mai suffar tsoro-tsoro daga ƙasan ranta , cikin dabarbarcewa tace ,

" un daman nace ga Maman Mama fa ? Baku gaisa ba ? Zaka fita da Mama bata gaishe da Maman ta ba ,

Da sauri ya saki hannun Mama , bai yarda ya dubi fuskar Yakaka ba , yace

" sannu dai ,

Da sassarfa ya ƙarasa barin falon Mama ta ƙara da gudu ta bi bayan sa duk ita zuwan Yakaka ya takurata ,

Kallon tsanar da Yakaka ta bi Youssouf da shi akan idanun Hajja wacce ta kasa ta tsare tana bin duk wani motsin Yakaka da ido ,

MoÉ—e baki tayi kafin ta ce ,

" ke Yakaka tashi mu shiga daga ciki , ita Falmata ta bi sawun Mijinta tunda dai bata bar shi shi kaÉ—ai ba , wannan zaman naku na ke kuka ita juyayi baya haifar muku da É—a mai ido ba ,

" Abunda ya wuce ya riga ya wuce a bar tuna shi ana koke-koke kun ji ko ?

Daga Yakaka har Falmata babu wacce ta amsa mata saboda kawo yanzu hankulansu ya dawo jikin su daga ruÉ—anin murnar da suka shiga na sake ganin juna ,

Kowacce kuma ƙwaƙwalwarta ta fara aiki cikin gaggawa da fuskantar ƙalubalen dake gabanta ,

Ga Yakaka yadda zata tunkari Youssouf yaso ruɗata da ta ga ya ƙara girma da haiba , ƙwarjinin sa yana neman tsorata ta sai dai daga ta tuna shi da munanan ɗabi'un sa sai ta ji duk ya koma fanko a idanunta ,

tafi shiga damuwa akan yadda zata fayyacewa Falmata gaskiyar kome , yadda ta hango nutsuwa a fuskar Falmata ta san zuciyarta zata yi baƙi idan ta san gaskiya wataƙila ma ta tsaneta ita da kan ta da ita kuma bata fatan hakan, ita yaya zata yi ne ??

Falmata kuwa wani irin tsoro ne ya cika zuciyarta tare da zullumi , bayan murnar dawowar Yakaka , zuwa yanzu abunda zai biyo baya takewa Fargaba .

na farko tsoron rabuwa da Mama , Allah ya shaida bata fatan rabuwa da Mama ko na yini guda , sai kuma ga Allah ya dawo da Mahaifiyarta , ta san dole Uwar ta buƙaci 'yar ta , Yakaka zata rabata da Mama ne ko zata barta ta cigaba da riƙon Mama ? Tsoro take ji.

Tare da zullumin rabuwar su da Baban Mama ,  mutumin da Alkhairin sa ya yawaita ya tunbatsa a gareta , mutumin da tarin Alherun sa da haƙurinsa da ita ya huda tattaurar zuciyar ta tare da kafa soyayyar sa a ciki ,

Mutumim da ya zama tsani na samuwar ganin haske a idanunta , mutumin da sanadin sa ta samu ilmin boko da na addini dai-dai gwargawdo, 

mutumin da ta riga ta mallakawa gangar jikinta ya tarɓeta da so mai tsanani cike da tausayi da tausasawa  ,

mutumin da ta riga fara gina rayuwar ta da shi ,mutumin da wani ɓangare na jikin sa yake a cikin ta yana rayuwa ,

Wani irin narkewa ta ji dukkanin lakar jikin ta na yi ,

Lokacin da ta tuno yiwuwar rabuwar ta da shi , tunda daman rashin Yakaka ya kawo yiwuwar auren su har ta kai su da rayuwar aure tare yanzu kuma da ta dawo , dole ita zata matsa kenan  , zata tafi kenan , za su rabu kenan ina ma ina ma ?

Sanyi ta ji ya fara kaÉ—a ta duk kuwa da cewa a zahiri zafi ake yi ,

Hannun ta da yake cikin na Yakaka ta dunƙule , jin haka ya dawo da Yakaka daga tunanin da ta nausa a ciki , da sauri ta riƙe hannun Falmatan ,

"Falmata kun dawo baku ci abinci ba ke da Mama ? Mun yi muku girki fa , kuma ma na kawo miki tsaraba ban san ko Mama ma zata iya ci ba , ƙuli-ƙuli ne mai sugar irin naki kina so  ?

"ina so Yakaka kawo mun zanci , na daÉ—e ban ci ba , kamar kin san yana raina , yanzu na cewa Bab...

Sai tayi shiru bata ƙarasa ba , ji tayi tana tsoron ƙiran sunan sa a gaban Yakaka ko me yasa ?

Yakaka ta miƙe a hankali , ta nufi ɗakin da suka yi masauƙi ,

Hajja wacce tayi jugum a zaune tana binsu da kallon tsanaki , tace

'Uwarɗakina kar fa ki sanya kan ki cikin damuwar kome ko domin abunda kike ɗauke da shi a jikin ki damuwarki hatsari ne maigirma , da yardar Allah haƙuri tare da ƙaunar ki ta gaskiya da riƙo da zumuncin da kika yi basa bari ki tozarta ba , ke dai ki cigaba da yin kome domin Allah kin ji ko ?

GyaÉ—a kai kawai tayi ,

"nayi muku tuwon shinkafa da miyar kubewa , ga kuma farfesun dantsen sa , akwai dafadukar shinkafa 'yar uwar ki ta mata sarrafawar turawa a ciki wacce zaki ciki ?

Ƙarasowar Yakaka ya sa bata amsa ba , hankalinta ya koma kan Yakaka da take tahowa , ƙewar 'yar uwar ta tare da wannan ƙaunar mai tarin yawan suna taya ta binne duk wata damuwar ta tare da ƙarfafa mata ,

"Yakaka ashe kina da tsawo haka sosai , ga ki kuma fara sol Yakaka mai kyau da ke tubarakallah ,  bani labarin kamannin Maman mu da Baban mu da wa ni nake kama a tsakanin su ?

Yakaka wacce take sunce ledar ƙulin ta gama kuncewa ta ɗibo biyu a hannun ta , tana murmushi ta kai ɗayan bakin Falmata da ta ga tahowar hannun Yakaka ta buɗe baki ita kuma ta jefa mata ƙulin ,

" Da Baa kike kama Falmata sak ma kuwa kawai tsawon sa ne baki samu ba , ni kuma da Maman mu nake kama sak kawai ban kaita haske ba ,

Ƙurus-ƙurus ku-rus , Yakaka ta taune ƙulin da ta jefa a nata bakin , ta cigaba da cewa

" Daman an raba , ni da Bulama kamar mu ɗaya ke kuma da Baana kuma kamar ku ɗaya (sulum fut ) baƙaƙe siɗik , ta ƙarasa zancen da sigar tsokana ,

Yamutsa fuska Falmata tayi , kafin ta ce ,

"Amma ai Baa kullum yana cewa fararen mutane basu da ƙarfi da dauriya , mu baƙaƙe mun fi ku , Yakaka kin tuno da karon mu da Biri a gonar Baa ?

Wata sassauƙar dariya suka kwashe da ita lokaci guda , Yakaka wacce ta fi Falmata dariya muryar ta cike da amon dariyar da take yi ta ce cewa za kiyi ranar da kika sumar da ni a garin dukan Biri ,

Wannan karon hatta Hajja da take kallon su sai da ta murmusa , sannan ta ce tayaya ta sumar da ke Yakaka daga dukan Biri ??

Siririyar Muryar Falmata cike da dariya ta fara cewa ,

"Hajja lokacin girbi ne Baa ya kai mu gonar sa domin muyi masa gadi , muna zaune yin gadi da rana tsaka , sai wani ɗan Biri ya shigo gona , Yakaka ita ta gan shi ta dunga binsa da wata sandar da Baa ya bamu tana son doke shi amma Birin nan sai tsalle-tsalle yake yana gudu yaƙi barin gonar , ƙarshe dai yayi tsalle ya hau kan Yakaka char ya tsaya atsakiyar kan ta , Sai yakaka ta ce

"Falmata nace "Na'am ,tace Birin nan yana tsaye akaina ga sandar nan zan wurga miki , inda kike jin muryar ta za ki doke ta sama kaɗan ki buga masa da ƙarfi ɗan iskan Biri ɓarawo ,

Nace "to Yakaka , ta kuwa wurgo min sanda na É—auka ,

"Hajja na faɗa miki da na ɗaga sanda kin san dai ba gani nake yi ba a lokacin, na ɗaga ta da ƙarfin gaske , lokacin da. naji Yakaka tana cewa kai-kai-kai amma na riga na wulwula sanda sai kawai na rafka a zatona alama take min na inda zan bugawa sandar watau a kanta ,

ÆŠif na ji Yakaka tayi shiru ,

"Hajja ashe Yakaka na rafkawa sandar Biri kuwa tuni yayi tsallen sa , Yakaka kuma ta some ,

Ta ƙarasa bada labarin tana sakin shisshiƙar dariya tare da kwanciya bisa kujerar da take kai , ba Yakaka ba hatta Hajja , dariya take yi sosai ,

Yossouf da yake tsaye ta bakin ƙofar falon saboda hankalin sa da ya kasa kwanciya a zaman sa a falon sa , cikin duk daƙiƙa guda zato yake yi Yakaka zata sanar da Falmata kome ,

Da shi kuma ko kusa a yanzu bai shiryawa tarɓar tashin hankalin da zai iya biyo bayan hakan ba .

Baya yayi yana dariya da haƙoran sa kwarai labarin wannan ƙatoɓarar da Falmata ta yi ya bashi dariya ,

Yana shiga Falonsa wayar sa da take ajiye akan kujera ta sake É—aukar kiÉ—a sunan Tafeeda ne ke yawo akan fuskar wayar ,

Ji yayi damuwowin sa sun sake yi masa rubdugu , zama yayi daga kan kujera ya ɗau wayar ya riƙe , ya akayi ma Tafeeda yasan dawowar sa, ?  duk ƴan mintoci kenan da sanya layin sa na nan a waya ,

Shi a yanzu baya buƙatar ƙarin wasu damuwowi , yasan Tafeeda ƙudirinsa shine ya raba shi da Falmata da shi kuma ba shiryawa hakan yayi ba , ba kma ya jin zai taɓa shiryawa har abada,

Danna wayar yayi ya sa a silent saboda Mama da ta samu bacci kar ƙaran waya ya tadda , tagumi ya rafka da hannunsa biyu yana jin yadda cikin sa ke ƙugin yunwa amma ba damar cin abinci ,
Chapter 180 · 0% Book details