← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 269

Sashe 63

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru tayi tana jin yadda zuciyar ta take faman bugu da wani irin tsananin tsoro da ya kama ta makamanci da na mutumin da ake shirin raba sa da gudan jinin sa .

wannan cikin bashi da wani amfani a wurin ki illa ya jefa ki a wahala tare da ƙuncin rayuwa , kin dai ga kaɗan ɗin sa yadda ta faru da ku a wajen madam saly , to wannan kaɗan ne akan irin wahalar da zaki iya faɗawa muddin kika cigaba da barin cikin nan a jikin ki , ranar babbar nadamar ki da shiga tashin hankalin ki kuwa shine ranar da abun da yake cikin nan naki zai fito duniya ,toh kiyi yaya da shi ? Ki kai shi ina ? Ki raine shi da me ? Ki kula da rayuwar sa da me ? Idan ya girma ya tambayi ina uban sa ki ce da shi me ?  Amsar ita ce babu !

ke da kan ki yaks kina buƙatar matallafi wanda zai ɗago ki ki tsaya da kafafun ki kema ki taimaki ƴar uwar ki miskiniya , ki tuna baku da kowa baku da kome baku da wurin zuwa baku san kowa ba , kowan ku sun ƙare ,"
  mts ta jaa tsaki ni bata lokaci na Ma nake a wofi , ke da na zauna ina faɗawa waɗannan kalaman kin fini masaniya akan su saboda kai tsaye ke suka shafa ,'
    Abu na karshe da ni zan faɗa miki shine idan har kika amince muka je aka raba ki da cikin nan ni kuma na miki alƙawarin zan tsaya miki ki shiga harkar bariki da karfin ki , ki ɗaukaka ki tumbatsa ,ki kai gaci , domin garin abuja zamu wuce kina gama warwarewa ,

idan kuwa har kika nuna ƙin amincewa kamar yadda na hango alamun hakan akan fuskar ki , to ni na janye hannu na akan lamarin ki , ki nemi wurin da zaki baiwa kan ki tare da cikin jikin ki zuwa kan ƙanwar ki mafaka , ni da kike gani ma bazan wuce sati mai zuwa ba zan sake barin gari , ban kuma san ranar dawowa ta ba ," dan haka zaɓi ya rage gare ki yaks ,! Kiyi tunani daga yanzu zuwa gobe

    Daga haka ta ɓalle jakar ta ta fidda naira dubu biyu ta miƙawa yakaka ,'

   ni zan fita ga wannan ku ci abincin rana da dare ke da ƙanwar ki , ni sai gobe zan dawo , ku kula min da ɗaki na akwai muhimman kaya na a ciki ,!

Daga haka ta kaɗa kan ta tana mai barin ɗakin , sautin ƙarar cumgum ɗin bakin ta tare da sauran kalaman da ta furta suna amsa kuwwa cikin kunnuwan yakaka ,"  

To ita yanzu INA MAFITA ???

Tayi zurfi cikin tunani har bata san lokacin da falmata ta dawo ba , sai ji tayi tana ambaton sunan ta ,"

A sanyaye ta miƙa hannu ta riƙo hannun falmata ," tana buƙatar mashawarci tana buƙatar a bata ƙwarin guiwa akan abun da ta ƙudurta cikin zuciyar ta , toh sai dai bata da abokin shawara bata da kowa a tare da ita sai falmata ƙanwar ta , dan haka a karo na farko tayi niyyar ta buɗe zuciyar ta ga falmata duk kuwa da ƙarancin shekarun ta amma bata da haufi akan kaifin hankali tare da tsinkaye irin na falmatan wanda halitta ce ko kuwa baiwa daga Allah .

falmata samy baby tace gobe zamu je a fidda min abun da yake ciki na ,! ta ɗora da warware mata duk yadda suka yi da samy baby da irin togaciyar da tayi mata na barin su da kan su idan har taƙi amincewa a fitar da cikin .

Shiru kowaccen su tayi ,"

   Yakaka ki bari mu haihu mu zama mu uku muma ,!

    Ta tsinkayo kalaman falmata da suka sanya ta ɗan murmusawa ,"kalmar mu haihu ta bayyana ƙauna ta gaskiya da take tsakanin su abun da ke cikin ta ba nata bane ita ɗaya nasu ne su biyu da ƴar uwar ta,"

    falmata idan mun haihu aina zamu zauna da yaro jinjiri ? kuma da me zamu yi rainon yaron ?
   
   Zamu ajiye shi cikin jikin mu ruwa da rana da sanyi da iska baza mu bari su cutar da shi ba , zan yi bara na samo kuɗi muyi rainon sa ,

Lokacin da falta tayi irin cikin ki naji mamar su bakura tana cewa Allah ya sa kar ta zubar da cikin ta kashe yaron babu kyau babban zunubi ne ,"

Idan muka bar cikin nan kowa zai cigaba da tsanar mu , duk inda muka je za'a kore mu ,

   muna da junan mu yakaka, kina da ni ina da ke , duk inda muke zamu kasance tare kafin abin da yake cikin ki ya fito mu zam mu uku , zamu haɗu mu zama rumfa agare shi har ya girma ,!

Idan muka tafi wani garin da tace zata kai mu mun sake yin nisa da maman mu , watakila shikenan mun tafi baza mu dawo ba toh aina zamu ga maman mu ? Yakaka ban san ko kema kina jin irin abun da nake ji ba a kullum ji nake watarana zamu haÉ—u da maman mu tana nan bata mutu ba ,!
  kar mu bar garin nan yakaka !

Amma ya zama dole mu bar gidan nan falmata !

   Mu tafi ina ?

Koma ina ne zamu tafi falmata .

Toh yakaka shikenan ,!

Shiru ya ratsa tsakani a hankali yakaka ta zame gami da kwanciya rigingine tana mai sake zufafa cikin tunani ,
    Tun ranar da ta fahimci cewa tabbas fa tana ɗauke da ciki a jikin ta , taji wani  ƙaƙƙarfar so da ƙaunar aɓun da yake cikim nata yana huda zuciyar ta yana ƙaruwa a duk wayewar garin duniya ," ƙaunar sa tana sake ninkuwa idan ta tuno fa bature kam silum shine baban abun da yake cikin ta , wani farin ciki take ji a duk lokacin da ta tuno zata haifi ɗa mai irin kamannin sa ,watakila ma ya gado mahaifin sa wurin gayu da ƙwalisa , a jikin ta take ji watarana zai dawo gare ta , zata nuna masa ɗan sa ko ƴar sa , ko ya ƙarba abun da ta haifa ko kar ya ƙarba ,wannan ba damuwar ta bace ba , kamar yadda falmata tace , zasu yi rainon abun da ta haifa da dukkanin ƙarfin su , zata haɗa shi da falmata ta zamto garkuwa a gare su , zata zamto musu inuwar da zasu tsaya a ƙarƙashin ta su fake zafin rana da dukan ruwan sama , zata kasance bangon da zasu jingina su huta a jikin sa , zata yi kome domin ganin rayuwar su ta inganta ,

Tamkar abun da yake cikin ta yaji irin tunanim da take , sai ya harba a karo na farko ya fara motsawa a cikin mahaifar ta alamun da yake nuna a yau an busa masa numfashi !

  a ɗan firgice ta kai hannun ta saitin inda taji motsin sa tayi kasaƙe tana son sake ji , ai kuwa sai ta ji zil-zil ya sake motsawa da ɗan karfi ,"

Da sauri ta kamo hannun falmata wacce take taÉ—in zuci ," ta É—aga rigar ta tare da É—aura hannun saitin cikin ,"
  Falmata kin ji abun da yake ciki na ya fara motsi ,"
   da sauri falmata ta sake manna hannun ta lokaci guda tana washe gajejjerun haƙoran ta , ta ina ne inda na ji ???? Suka dafe cikin tare
       Sake yin ɗan ƙaramin motsi yayi , ai kuwa a tare suka saki ƴar sakakkiyar dariyar su ,tamkar masu gasa !
        yaron mu INA SON KA , falmata ta furta hakan da sanyin murya

da tattausan murmushi yakaka take kallon ta ,"
        NI KUMA INA SON KI FALMATA NA .

5:20am

Falmata falmata ,
   yakaka ke tashin ta , jin an shiga sallar asubah ,'
    tashi mu tafi lokacin tafiyar mu yayi !
   toh yakaka ,
   jakar baccon su ɗaya ta ɗaurawa falmatan a kai ita ma ta ɗau ɗayan bayan ta kullewa samy baby ɗakin ta ,tare da ajiye mukullin a ƙarƙashin shimfiɗar goge ƙafa da yake shimfiɗe bakin kofar ɗakin .

Da bin bango suka fita a gidan suka miƙa bakin hanya hannayen su sarƙe da na juna ,

a tsorace suke sosai akan hanyar babu kowa sai jifa jifa suke cin karo da mutane zasu masallaci , zuciyar yakaka sai bugu take da fargabar gamuwar ta da karnuka .

Da ikon Allah suka ƙaraso bakin babban titi , lokacin gari ya fara yin ɗan haske shaa ,' Alfijir ya keto ,' cikin nutsuwa suka tsallaka titin , yakaka tana mai waiwayawa kallon kwarin unguwar a ran ta tana jin har abada baza ta sake tako kafafun ta cikin unguwar ba !
.
A cikin rumfar bakin wani shagon da yake jikin kasuwa suka yada zango , yakaka wacce ta gaji tilis da ƴar tafiyar da suka yi sakamakon rashin ƙarfin jiki , ta kwanta a dandaryar sumintin gaban shagon gami da yin matashi da baccon ta , falmata kuma ta zame ta zauna daga jikin bango ,"

Falmata ke zan ajiye ki wurin barar ki na da idan an fito kasuwa ni kuma zan É—an kewaya na nemi wani É—an aiki , ko dako ne ma nima nayi na É—an samo mana wani abu kafin mu ga yadda Allah zai yi da mu koh ?

hakane yakaka , amma ke ki zauna kawai kin san fa baki da isasshiyar lafiya kar ki je kiyi aiki kuma ki cutar da kan ki da yaron mu ,!

bazan yi aikin wahala ba daidai karfi na zan yi falmata .

  Toh shikenan yakaka .
Chapter 63 · 0% Book details