Sashe 205
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bai bata takamai-mai É—in amsa ba a madadin haka wata sabuwar sallama ya shiga yi mata cikin sanar da ita sabuwar tafiyar da yake da nufin yi a yau zuwa France , da yace yana iya kaiwa watanni biyu zuwa uku ,
Da wani irin yanayi na tsoro take kallon sa , yaya zai tarki yin tafiya haka mai nisa bayan yasan suna mataki na ƙarshe ne na gaf da cikar burin su me hakan ke nufi ?
Duk yadda ta so ta masa rigima yaƙi bata dama , dole ta yadda suka yi sallama ,cikin kwantatciyar muryar sa ya cigaba da rarrashin ta kafin wayar sa take danƙe a hannun sa tayi ƙarar alamun shigowar saƙo , yana karanta saƙon ya miƙe a ɗimauce yana raba ganin sa a da'irar wajen hankalin sa baki ɗaya ba'a kwance yake ba ,
da ido ta bi shi ƙwalla na taruwa mata , yadda ya juya bai ko saurare ta ba , ya taɓa mata rai babu shakka akwai abunda yake faruwa da shi da bata kai ga sani ba , taku biyu yayi ta ƙira sunan sa , a hankali ya juyo yana ɗora ganin sa akan ta tsayayyun idanun sa na bayyana wani irin yanayi na tsoro .
" Ghaddafi , kada ka manta da ni zan jira ka koume tsawon lokaci , ta furta hakan tare silalowar hawaye daga kwarmin idanun ta ,
Daga inda take ta hango yadda laɓɓan sa suka motsa ko da kunnuwan ta basu iya jiyo mata amon sautin kalmomin sa ba ta fahimci cewa cewa yayi ,
  " Maimounatou ina son ki .
Ƙarar harbin bindiga da ya gifta ta kunnen ta shi yasa ta kusa hantsilawa daga kan kujerar da take zaune , kafin ta farga harbe-harbe sun yawaita a sararin wajen da nan take mutane suka kaure da guje-guje , akan idanun ta Ghaddafi ya ɗaga kafafunsa ya taka da gudun gaske yana barin wajen kamar fitar kibiya .
Ta miƙe tsaye amma ruɗani ya sa ta koma da ƙarfi ta sake zama tana toshe kunnuwan ta biyu , ta gaban idanun ta takun ƙafafun sa da suke sanye da manyan takalman sa na soji ya wuce da gudun gaske ya dafa baya akan hanyar da Ghaddafi ya bi .
Ba zata iya sanin iyakar adadin mintocin da tayi durƙushe a gurin ba, zuwa lokacin da harbin bindugogin ya tsagaita , lokacin ta samu damar miƙewa daga durƙuson da tayi a ƙasan teburin gaban kujerun wajen .
Ba tare da ta tantance yanayin da take ciki ba ta fara taku da sauri da niyyar ficewa a wajen , can gefen zuciyar ta na son sanin halin da Ghaddafi ke ciki , sai dai bata saurara ba domin tana buƙatar nutsuwa mai tarin yawa a dai-dai lokacin .
Kamar ance ta ɗago kan ta lokacin da ta ɗaga ƙafa tana barin wajen , idanun ta suka sauƙa kan dogon sojan da yake sanye da kakin sa da jini ya ɓata gaban rigar , har yana ɗiga ta wajen hannun sa , yana tafe da takun sa na jarumta a hankali ta sauƙe ganin ta ƙasa inda ya riƙo ƙafar mutumin da ya harbe yana jaan sa tamkar kayan wanki , idanun ta suka sauƙa kan fuskar Ghaddafi da jinin da ya ɓata fuskar sa zuwa ƙirjin sa bai hana ta gane shi ba ,
Duk wasu jijiyoyin jikin ta ne suka tsayawa yin aiki , jinin ta ya daskare , kamar yadda kunnuwanta suka toshe , numfashi kuma ya fara kokawar kufce mata , ƙafafun ta taji suna mata girgiɗi.
  " Ya kashe min Ghaddafi , Ya kashe min Ghaddafi .
Sune kalmomin da suka ƙwanƙwashi ran ta suka farkar da ita daga suman zaune da tayi , wani irin ihu ta sa mai sauti da ya jawo hankulan tsirarun mutanen da suka rage a wajen da zuwa lokacin daman ma'aikatan wajen ma korar jama'a suke .
Babu wanda ya saurari kukan da take yi da ake zaton na firgici ne aka tisa ƙeyar ta zuwa wajen park ɗin .
Mutuwar Ghaddafi bata zowa Maimounatou da sauƙi ba domin tamkar hauka tayi , surutai kawai take yi tana sambatun da ba'a wani fahimtar me take cewa , bata rubuta jarabawar ta ta ƙarshe ba hukumar makarantar ta turawa da Maimartaba mummunan saƙon rashin lafiyar ƴar sa ,
Nan take aka tado da mutane ciki har da manyan yayun ta suka zo Niamey suka ɗauke ta zuwa gida Agades .
Kowa ya ga yadda take yi a lokacin cewa ake gamo tayi , aljannu ne suka taɓa ta, dan haka aka shiga magungunan iska ba ji ba gani ,
Ganin ana ta banka mata hayaƙi babu gaira ba dalili , ya sa ta rusuna ta bar surutai da ƙiran sunan Ghaddafi , sai ta koma ba un ba un'un , bata iya ci bata iya shan ruwan kirki wanka ma bata yi ,
Ba'a tsahirta da magunguna ba , aka cigaba da kawo magani iri-iri , na wanka da na sha da na turare , kai har da na shafawa da shaƙawa ,
Mafi yawa zubda su take yi , ta kuma kasa sanar da kowa dalilin tashin hankalin ta , to cikin iyayen ta biyu wanene ya san Ghaddafi ?? Ya san Alaƙar su ? Babu .
Tsawon wata guda ta fara dangana sai kuma rashin lafiya Mai tsanani ya taso ta a gaba , ciwon ciki mai tsanani duk ɗan abunda ta samu ta ci sai tayi aman sa , ga zazzaɓi mai zafi tare da ciwon kai ,
Kasancewar ta wayayyiyar ƴar jami'a ita da kan ta ta fara bincikar kanta game da sauyin yanayin da take ji a jikinta , a sirance ta aiki Gnala ta sayo mata abun awun tabbatar da samuwar ciki .
Da zaton motsuwar kwakwalwar ta Gnala ta karɓi kuɗin ta sayo mata ,
Kamar yadda tayi zato gwajin farko ya nuna mata samuwar ciki a jikin ta ,
Ranar damuwa ta dawo mata sabuwa dal , tayi kuka irin wanda tun mutuwar Ghaddafi bata samu damar yin irin sa ba sai ranar ,
" ina zata da cikin jikinta tana É—iyar Martaba É—iyar Asali É—iyar sarki ?? Ya zama dole ta rabu da cikin , ina ma da ace aure suka yi ita da Ghaddafi ta samu cikin nan ? Da zata fi kowa murna da samuwar sa ,
Ita da kanta ta saci hanya ta fita , wani babban ɗakin sayar da magani ta je , bayan ta wadata mai sayar da maganin da maƙudan kuɗaɗe ya ɗau maganin zubar da ciki mai ƙarfi ya bata ,
Tun da ta saya maganin sau uku tana yunƙurin shan maganin tana kasawa , cikin satin gaba ɗaya ta sake lalacewa ta rame tamkar wacce take tsananin ciwo ,
A karo na huÉ—u ta runtse ido ta haÉ—iye maganin , ta yi kamar yadda pharmacist din ya faÉ—a mata ,
Cikin ƙasa da mintoci arba'in kachal jini ya fara sauƙa mata kafin ciwon ciki mai tsanani ya biyo baya , jini kuma ya ɓalle mata ,
Kasancewar ta kulle ƙofar falon ta bayan ta kori bayun da suke kula da ita sai Gnala kaɗai ya sa babu wanda ya san irin wahalar da ta sha da irin zubar jinin da tayi daga ita sai Gnala ,
Da kyar jinin ya dai-daita ciwon cikin kuma ya lafa ta samu bacci ,
Sai zuwa la'asar ta farka ta ji ƙarfin jikinta duk wasu kasala da rashin ƙarfi irin na masu ƙaramin ciki ta rabu da jin su , dan haka tayi wanka ta shirya tana jin raguwar damuwar da take ciki da kaso goma cikin ɗari ,
Kai tsaye sashin Mahaifiyar ta ta yiwa tsinke , inda ta tarar da ita a babban falon ta tana kishingiɗe bayu na mata hidima , ganin ta ya sa ta miƙe zaune cike da jin daɗi ta rungume ta tana murnar ganin alamun samun lafiyar ta ,
Duk da cewa ta hango wasu yanayi da bata gane da su ba a tare da ita amma ta danganta kome da larura irin ta jinnu da babu abunda basa sawa .
Suna zaune aka hasko fuskar Colonel Youssouf Abdoul-azizou baskore a babban tv da yake kafe a gaban su , ana bayani akan ƙarin girman da ya samu sakamakon samun nasarar kawo ƙarshen gungun 'yan fashi da makamin nan da ake yiwa take da escouade de lions , inda bayan rundunar su ta tarwatsu su daga terene , ya samu nasarar kashe manyan huɗu daga cikin su , ciki har da shugaban su Ghaddafi Yacouba Dango .
 Raba hoton aka yi biyu , gefe hoton gawar Ghaddafi ne , gefe kuma hoton Youssoufa ne yana dariya lokacin da ake masa ƙarin girma .
****
  Gimbiya Maimounatou ta sanya hannuwanta biyu ta share hawayen ta , kafin tayi ƴar dariya da take nuni da tasowar miƙin ƙasan ranta ta cigaba da cewa
" Tun daga wannan ranar na kuɗurci aniyar ɗaukar fansa akan sojan da ya kashe Ghaddafi da hannun sa , nima so nake na kashe shi, so nake na ɗanɗana masa baƙin-ciki irin wanda ya samar a gareni .
   " Ban damu da laifin da ake tuhumar Ghaddafi da shi da yasa aka kashe shi ba , a ganina Ghaddafi bai cancanci mutuwa a yanzu ba kome kuwa girman laifin sa , akwai sasauci hukuncin kisa yayi tsanani ga Ghaddafi , mafi girman sashi na raina ma ban yadda da laifin da aka danganta Ghaddafi da yi ba , saboda ni ban taɓa ganin sa yayi kisa a gabana ko satar kayan wani ba .
 " daga lokacin na shiga bin hanyoyin da duk nasan zasu taimaka min wajen cimma nasara kan ƙudiri na , a ƙarshe kuma nayi nasarar sanyawa Youssouf so na da har ta kai ga ya amre ni sanin da nayi wannan ce hanya mafi sauƙi da zata kaini ga kashe shi ,