← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 269

Sashe 135

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata ji ko É—ar ba akan sanin da tayi auren su auren haÉ—in iyaye ne , tare da sanin da take da shi akan irin tsanar da shi yake gwada mata , ta ji ta gani ta amince ta kuma shirya yin zaman aure da shi da gasken gaske , cikin kowanne irin hali , tana jin son da ita take masa zai ishe su rayuwa ita da shi ,
   Soyayyar sa ga gimbiya maimouna bata razana ta , illa kishi da ke nuƙurƙusa ran ta , dan haka ta sha alwashin ko da ƙaƙa , sai sun raba soyayyar youssouf biyu ita da maimouna kamar yadda zasu mallake shi a matsayin miji su biyu a lokaci guda , idan ya so ita na ta kason soyayyar idan ya so ya zubda a rariya , bata da damuwa son da take yi masa ya ishe su , .

Shiri take ka'in da na'in ubbo tana taya ta haiƙan , gefe guda hajiya umma na bada ta ta gudummawar a matsayin siyama na ɗiya a gare ta , ɗiyar da ta goya tayi rainon ta tun tana tsumman goyo ,

Lokacin da gnala take sanar da gimbiya maimuna dangantakar dake tsakanin youssouf da siyama har ma da zantukan da ta ji siyama na tattaunawa da  ubbo , bata wani ɗau batun da muhimmanci ba , saboda wasu dalilai nata da take ganin ko da ace zai aure su su biyun ita bata jin hakan zai dame ta , burin ta ɗaya tal , shine ta samu nasarar aiwatar da ƙudurin da zai sa ta aure shi .

Dan haka ko da yake kame-kamen sanar da ita batun auren sa da siyamar yana bin ta da kalaman rarrashi , kwantar da murya tayi ta dunga zuba masa sassanyan rikicin da ya sake ɗaga darajar ta a idanun sa tare da sake dilmiyar da shi cikin ƙaunar ta ,
     Ya dunga jin yayi sa'ar samun nutsattsiyar mace kuma me haƙuri, wacce mace ce a zamanin yanzu da za'a yiwa kishiya gab da lokacin auren ta , a kuma haɗa su aure rana guda , ba'a yi danbarwa da ita ba ? Ƙwarai ƙwarai maimouna ta ƙara ƙima a idanun sa ,

Samun haɗin kan ta farad ɗaya ya lafa guguwar ƙin auren a cikin ran sa , sai ya samu nutsuwar fuskantar shirye-shiryen auren tare da cigaba da zarya wajen sabon gurin aikin sa da aka tura shi Dosso , inda zai zama shugaban soji na baki ɗayan yankin na jahar Dosso ,

Tafkeken gida aka mallaka masa tare da motocin hawa biyu , ƙari da tarin hadimai sojoji tun daga kan masu gadi , direba , har zuwa kan me girki .

Tsakanin jahar Maraɗi da jahar Dosso babu tazara me yawa , dan haka lokacin da yake da samun tabbacin wajen zama a dosso , sai yayi niyyar bayan bikin su , zai dawo da gimbiya maimouna nan gidan sa na dosso , kusa da shi , ita kuwa siyama ta cigaba da zama can a maraɗi , tunda ita ta zaɓi auren cikin gida sai ta samu matabbata a cikin gidan , !

Sai dai yana sanar da hajiya umma niyyar sa , a take ya ga sauyin fuskar ta ,
     Abu guda ta ce da shi .

Kome tsanani kayi ƙoƙarin kwatanta adalci tsakankanin matayen da Allah ya baka amanar riƙon amren su , kar ka kuskura ka karkata ga ɗaya daga cikin su , saboda gujewa fushin Allah da azabar sa ka kiyaye , siyama da maimouna duk su biyun matan amren ka ne .

*****

Tun farkon satin aka fara gudanar da shagulgula da wasannin daga bangaren masarautar maraÉ—i har da ta Agades wanda suke da tarin wasannani da al'adun gargajiya fiye da na maraÉ—i , haÉ—i da shiri sosai da suka yi na bikin kasantuwar kowa ya san gimbiya maimouna É—iyar gata ce ta sosai ,

Har zuwa yau da take ranar sakun lalle ga amare , gobe juma'a za'a É—aura auren

Kamar yadda al'adar masarautar maraÉ—i take , duk lokacin da za'a yi sakun lalle ba'a yi a cikin masarauta ,

can tsibirin maraɗi ake tafiya da amayar ,"wani ƙaramin gari ne da yake ƙarƙashin jahar maraɗi da ake ƙiran sa tsibiri bashi da nisa sosai da ainahin cikin garin maraɗi ,

Gidan sarkin tsibirin nan ake sakun lallen a cikin gidan akwai wata mace da ake ƙira ,inna , wacce sunan sarautar ta ce ,inna ɗin ," ita take sakun lalle ga amaren da duk za'a shigar ko za'a fitar daga masarautar maraɗi,

Karfe ɗaya na rana gimbiya maimouna tare da ƙanwar mahaifiyar ta da ƙanwar mahaifin ta da matar maimartaba sarkin agades ta biyu tare da wasu daga cikin matan ƴan uwa na ƙurƙusa tare da rakiyar amintattun hadiman ta mata biyu da bayu maza uku  sai kuma ƙaramar jakaɗiyar agades,  jirgin su ya iso tashar jirgin sama na maraɗi daga agades ,inda nan take motocin da suke jiran su domin kai su tsibiri suka ɗauke su kai tsaye zuwa tsibirin maradi ,

Tarɓa me cike da girmamawa aka yi musu , inda suka tarar da gidan cike da manyan mata masu sarauta na kurkusa da fada cikin su har da manyan yayun biyamuradi ,"Ammi da Dada da Asma'u da ake ƙira ma'u ƴar wajen hajiya mama ta farko . ," da kuma ƙaramar jakadiya .

Tsakanin su bai cika awanni biyu ba siyama ta iso ƙarƙashin rakiyar ƙannen maimartaba sarkin maraɗi su biyu tare da hajiya mama da ubbo sai kuma ƙannen baban ta su biyu ,

Ta ko'ina buɗa da ƙirari ne yake tashi saboda makaɗa da maroƙa da suka cika faɗar sarkin tsibiri duk da cewa an dakatar da su daga shiga cikin gidan inda aka fara shirin sakun lallen amaren
   
  Shimfiɗa ce aka yi da manyan jajayen dardumai , a tsakiyar babban ɗakin , inda aka ajiye babban tum-tum na zama a tsakiyar shimfiɗar ,

Inna tayi umarni da a shigo da siyama za'a sanya ta a lalle ,

Ko kafin bangaren gimbiya maimouna su ce kome , hajiya mama ta yunƙuro ,

  Wacce siyama kouwa ? Ai ita maimouna ita ce matar farko dan haka ita za'a fara sanyawa ga lalle ko kouwa ?

  Hakka zance yake ranki ya dade uwagijiya ta ,

  cewar ƙaramar jakadiyar Maraɗi

Aiyuriyuriyyyy ayuririyyyyyy ayyuririyyyy !!

Wata zazzaƙar guɗa ta fito daga hancin jakaɗiyar agades , saboda jin babban matsayin da uwargiyar su ta samu ,

  Taka a sannou-sannou ƴar sarki jikar sarki , matar yarima ɗan sarki surikar sarki , gaban ki salama bayan ki lafiya  farar macce fitila gida , tauraruowar ki me ƙarfi ce wacce hasken ta ya tarwatsa ya zagaya nahiya tun dagga birnin agades har yankin maraɗi , wouce gabba kin yiwa sauran mata zarra , kin yi gado ba haye kika yi ba mahaifiyar ki ai ita shugaba ta matayen agades ,
 
  A hankali ta sanya kan ta cikin ɗakin tana jin yadda ginshiri irin na sarauta yake sanya ta ƙasaita da jin faɗi.

Bayan shigar ta guda daga bangaren mahaifin ta tare da guda daga bangaren mahaifiyar ta suka rufa mata baya , ubbo ta yunƙura zata shiga hajiya mama ta dakatar da ita tare da yiwa ma'u umarni da ta bisu kamar yadda al'adar take mutum ɗaya daga bangaren dangin miji ke shiga ɗakin sakun lallen .

Bayan zaman gimbiya maimouna inna ta janye hular alkƴabbar dake bisa kan ta , baƙin gashin ta da ya sha gyara ya bayyana , inna ta sanya wata ƴar kyakkyawar kibiyar kitso ta raba gashin biyu hagu da dama ,

Matar da take waziriyar inna ta miƙo mata wani ƙoƙo cike fal da madara sanuwa/nono , ta karkata ƙoƙon a sannu sannu ta fara zuba madarar a daidai tsakiyar tsagun ,

A hankali kakkauran nonon ya fara kwaranya , bisa tsagun kafin ya saki layi ya tarwatse a gaba ɗayan cikin gashin maimakon ya bi kan hanyar da aka masa ƙaɗai ,

Nan take inna da waziriyar ta suka haɗa ido suna masu gƴaɗa kai a hankali , yayin da fuskar ma'u ta sauya tana bayyana ɓacin rai a sarari , har aka gama zuba nono nan haka yayi faca-faca akan fuska da jikin kayan gimbiya maimouna ,

A fusace ma'u ta juya ta fita daga É—akin gefen mahaifiyar ta ta je ta tsugunna ta mata raÉ—a , nan take fuskar hajiya mama ya bayyana wani sirrantatcen murmushi , kafin tayi gyran murya tayi wa jakadiya alama da ido ,

Nan take jeka ta karkace kai ta rangaɗa ƙaƙƙarfar guɗa da ta sanya , mutanen agades samun kwanciyar hankali musamman innonin gimbiya maimouna da duk suka sha jinin jikin su , kan shirun da suka ji daga ɗakin ko dai ƴar ta su tayi kuskure ne cikin rayuwar ta ?

Amma jin buɗa daga bakin jekadiyar maraɗi ya sa hankalun su ya kwanta yayin da tasu jakadiyar ma ta karkace kai ta dunga sakin zaƙaƙan buɗoɗi ,

  Bayu mata biyu suka jawo wata ɗirkekiyar tunkiya fara sol suka ɗanka ta ga hannun matar sarkin agades ,
   Tunkiyar gimbiya maimouna ce ta sakun lalle , nan take bayun agades suka kama igiyar tunkiyar suka riƙe gam .

Ma'u ta koma ɗakin ƙarƙashin umarnin hajiya mama ta sanya farin kyalen ta share fuskar gimbiya maimouna gami da jan hular alkyabbar ta ta rufa mata akan ta ,

Suka fito daga É—akin ,

Bayan an sauya shinfiÉ—a da wajen zama aka yi umarni a shiga da siyama ,

Ƙanwar mahaifin ta ɗaya tare da hajiya mama sai kuma ubbo su ne suka shiga da ita ta zauna akan tum-tum

Inna ta tsaga gashin ta , ta karbi ƙoƙon madarar ta shiga tsiyayo mata shi daga tsakiyar kan ta sannu sannu ya shiga bin layin yana gangarawa har zuwa kan siririn karan hancin ta yana ɗiga a gaban rigar ta , har nono ya ƙare bai karkace hanya ba ,

Wata ƙarƙarfa guɗa ce ta taso daga hancin inna da tayi amsa kuwwa har fada da nan take makaɗa suka ƙara ƙarfin kiɗan su da ƙirari ,
Chapter 135 · 0% Book details