← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 269

Sashe 136

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga waje ma bayun masarautar maraɗi suka dunga sakin buɗa ba ƙaƙƙautawa ,

Zuciyar hajiya mama tayi bakikkirin lokacin da ubbo ta sunkuya ta ɗau farin kƴallen tana gogewa siyamar madarar fuskar ta idanun su suka gauraye cikin na juna sassanyar ƙaunar da take tsakanin su tayi tasiri idanun siyama suka ciko da ƙwallar murnar ganin wannan ranar me cike da ɗinbin tarihi a wajen ta , a hankali ubbo ta kai hannun ta duk biyu ta rungumo siyamar zuwa jikin ta , a hankali ta raɗa mata a kunne

   Madallah da ke ƙauna ta ɗiyar kirki , me daraja ,Madallah da ke mace tagari abar alfaharin iyayen ta da mijin auren ta !

Ko kusa ran hajiya mama bai yi daɗi ba da cikar budurci da alamu suka bayyana ga siyamar kamar yadda al'adar daman take nuni ne da macen da take cikakkiyar budurwa ita ce wacce nonon ke bin dai-dai tsagun layin ba tare da ya karkace ba , ta so ƙwarai ace an samu matsala irin wacce aka samu ga gimbiya maimouna ,

domin tayi amfani da damar wajen hana yiwuwar auren siyama da youssouf wanda ta ji zancen sama ta ka babu zaton ta babu tsammani , kuma a zahiri bata ƙaunar duk wani abu na alkhairi ya raɓi youssouf ,

Sannan irin tashin hankalin da mommoudu ya shiga da jin zancen haɗin amre tsakanin youssouf da siyama , alhalin shi zuciyar sa ta rayu tsawon lokaci ɗauke da dakon soyayyar siyamar , meyasa kome na cigaba da samun nasarar rayuwa yana ga youssouf ba shi ba ? Meyasa maimartaba ya tattara duk wasu gata da kulawa ya bada ga youssouf alhalin ga shi , shine kuma ƙarami ?

*******

Biki aka yi na bajinta da gata , irin wanda ba'a taɓa yin makamamcin sa ba a tsakanin jahohin biyu , aka yi biki aka gama lafiya lau amare sun ka tare a gidajen su da suke cikin da'ira guda sai dai kowaccen su tana sashin ta yayin da sashin biyamuradi yake tsakiyar nasu , gini ne guda uku a tsaye ,

Daren ranar lahaɗi da aka yi wuni aka watse shine daren da farkon sa yake zaƙi ga youssouf kafin zuwan tsakiyar sa da kome ya rikiɗe ya kuma sauya ya birkice ya hautsine masa , ya sanya shi shiga ruɗani , nadama bakin ciki tare da tarin tsoro ,

Maimouna ita ce macen da ya ɗau aniyar kwada mata ƙauna da soyayya irin wacce yake da burin nunawa ga matar auren sa , hakan kuma ya fara gwada mata a tun farkon daren da yake jin tamkar ya haɗiye ta dan so ko kuwa ya buɗe cikin ƙirjin sa ya cusa ta , sai juyi da ita yake yi yana lallaɓa ta daki-daki tamkar ƙwai , kafin kome ya kankama , zuwa lokacin da zai fahimci bara gurbin ƙwan da ya ɗaukowa kan sa ya kuma ta'alaka soyayyar sa akan ta , har ma ya sallama mata duk wani so gami da yadda da ya mallaka ,

Ashe yayi kuskure ne , shin ashe ta riga ta so wanin sa kafin shi ? Har ma ta mallaka masa abu mafi daraja agare ta wato gangar jikin ta ? Ashe ita ɗin ta ha'ince shi ne ? Shin ko dai shine ya ha'inci kan sa ? Shin ko dai ayar Ubangiji ce ke tabbata akan sa ? Idan kayi zina da matar wani ? Idan kayi zina da ƴar wani ?  Idan kayi zina da ƙanwar wani ?? Uwar wani ??

Tunanin hakan ya tsorata shi tsoro me tsanani , da ya hana tasirin fushin sa bayyana har ya nuna shi ga gimbiya maimouna da ta cigaba da yi masa lamɓo da nuna masa salo salo na gogaggun mata har da ƴan ƙananun koke koken ta , ita ciwo take ji ,

Sai yayi wani zugum kamar soko ya sanya mata ido , ah to shi zata yi wa bariki ?? Ai ya san me ake nufi da budurci , " amma tunaninikan da suke bijiro masa da shuÉ—aÉ—É—en laifin sa suke barazana ga nutsuwar sa saboda zuwan dodo-dodo da suke masa suna sake maimaita kan su tare da bada fassara akan halin da ya riski matar sa a ciki ,

Hannun sa ya kai da ƙarfi ya jawo ta ya jefa kan ta kan ƙirjin sa yana jin yadda iskancin kukan da take yana sake dagula masa lissafi ,

ÆŠan Allah ki min shiru
  Yace da ita , a tsawace

Da yake daman kukan gulma ne sai tayi luf kafin gajiyar biki tare da gajiyar farkon daren su danne ta bacci me matuƙar ƙarfi da daɗi ya silalo ya chafke ta ,

A hankali ya zame ta daga jikin sa ya miƙe daga kan gadon , rigar baccin sa ya ɗauka ya saka , ya fara taku yana barin ɗakin ,

Yayi zurfi a cikin tunanin abun da ka iya je ya dawo cikin rayuwar sa , mama ita take ta kai kawo cikin ran sa , rayuwar É—iyar sa yake hangowa , yana jin wani irin al'amari me girma wanda yake tafe da tsoro akan ta , yana son tsare ta , so yake ya boye ta kar laifin da ya aikata ya shafe ta , tsoro yake kar tarihi ya maimaita kan sa ,

Bakin cikin da yake shaƙa kaɗai a wannan daren yayi masa yawa ma , me yafi ka san cewa matar ka tayi tarayya da wani ta hanyar zina sanya bakin ciki da ruɗani a cikin rai ??

Wani irin kishi me tsanani yake ji , wani irin yanayi yake ji akan ta , ji yake ƙimar ta na zubewa tana zagwanyewa daga ran sa tamkar narkakkiyar roba a cikin wuta , ji yake tamkar yana ƙyamar ta ,

," yaya maimounatu zata min haka,"??
    Yake tambayar kan sa , yana sake maimaitawa ,

  Meyasa ? Meyasa ? Wai meyasa ?

Bai san cewa ya fito har harabar gidan ba sai da ya ji ƙaƙƙarfar iskar dake wajen tana ɗaga rigar sa da bai ɗaure maɗaurin ba , a hankali ya kai hannu ya ja igiyar yana ɗaurewa ,

Tun da ya fito idanun ta suka sauƙa a kan sa saboda daman ta gagara bacci ban da juyi babu abunda take , ita mace ce me zafin kishin abunda take so , dan haka sanin cewa da tayi yau ɗin biyamurdi zai kasance da gimbiya maimouna ya ta'azzara soyuwar ran ta , ya sa bacci gagara ɗaukar ta duk kuwa da iya satar sa ,

   Dan haka ta fito ta barandar ɗakin ta dake sama tana iya hango gaba ɗayan harabar gidan ta kurkusa daga inda take , duk kuwa da sanin da tayi dare ya raba ƙarfe 1:30am , to amma zafin kishi haɗi da bagen so ai rufe idanun me su suke yi .

  Me ya fito da shi a wannan daren ??
   Ta tambayi kan ta

Ta san shi farin sani kamar yadda duk wani motsi nasa yake kusa da zuciyar ta , take kuma iya fassara kowanne motsi nasa

Kada dai inda ya saba fita ya tafi a dai-dai wannan lokacin ya nufa ?? Wani irin tashin hankali ta ji ya taso mata ,
   Zato take ya daina ? Tunda tun bayan dawowar sa daga nigeria bata ji alamun fitar sa ba , bata kuma gan shi ya fita ba ,

Tunanin ta ya katse lokacin da ta ga ya É—aga kan sa sama tare da waiwayowa sashin da take ,

   Da sauri ta tsugunna tana ɓuya a bayan ginin gaban barandar ,

Cigaba yayi da kallon sashin nata lokacin da zuciyar sa ke kitsa masa wataƙila ita ma wannan ɗin da aka liƙa masa , ta riga ta gama sayar da nata mutuncin a waje ,

ya dangana kome da ya faru a matsayin hakkin baiwar Allah yakaka da ya É—auka , ya jagorance ta suka aikata mummunan laifi , shi daman Alhaki ai kuikuyo ne .!

*****

Asubar fari ya hau shiri , garin baki É—aya yayi masa wari , so yake ya tafi , yana son zuwa ya ga mama yasan ganin fuskar ta ne kaÉ—ai zai iya sassauta masa zafin da ran sa ke yi ,

Daga sashin sa kai tsaye cikin gida ya tasamma sashin hajiya umma ba tare da ya dubi sashin kowaccen su ba tsakanin sashin gimbiya maimouna da tun barin sa da yayi cikin dare da sashin siyama wacce bai ko kai da sanin launin kayan da suke cibge a ciki ba ,

Yana ratsa sararik gidan yana amsa gaisuwar bayu da hadiman da suke kai kawo suna gyaran gidan da sanyin safiyar .

A falo na ciki ya tadda hajiya umma tana Azkar , gefen ta ɗan ƙaramin tire ne da aka jera gorar ruwa da ƴan kofunan gilashi ,

Tana ganin sa farin ciki ya bayyana kan sa bisa fuskar ta , cikar haiba da mutuntukar da ta hango tare da shi ya sa ya yi mata ƙwarjini a yau , tabbas aure cikamakin addini ne , cikin sa akwai martaba tare da girma me yawa ,

Gaishe ta yayi sai dai saɓanin da da yake shigewa kusa da jikin ta , yau ɗin tanƙwashe kafafun sa yayi a gaba kaɗan da ita ya sunkuyar da kan sa ,

Kallon tsanaki tayi masa ba sai ya faɗa mata ba ta san yana tare da damuwa me girma wanda a jiya kafin rabuwar su da yamma babu wannan damuwar a tare da shi , dan haka take hasashen ko menene damuwar sa tana da alaƙa da iyalan sa , ita kuma bata da burin zama ɗaya daga cikin iyayen da suke bincikar rayuwar gidan auren ƴaƴan su dan haka sai ta yi kamar bata ga damuwar ta sa ba , ta matsa zuciyar ta da ke son sanin meye ya same shi ?

Yaya kwanan ɗiya na su dukkanin su da fatan kun tashi lafiya ? Basu da buƙatar wani abu ?

Duk kowa lafiya umma na basu buƙatar kome ,
Chapter 136 · 0% Book details