← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 266 OF 269

Sashe 266

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Addu'o'i ya shiga yiwa 'yar sa tsawon mintoci fiye da talatin dan tun Falmata tana kallon su har ta É—an fara gyangyaÉ—i .

Hannun sa da ya shafa mata kumatu shi yasa ta buɗe ido da kyakkyawar fuskar sa tayi arba yana mata murmushi kafin sautin  sa ya sauƙa a kunnen ta "Mon Bébé kina ji na ?

A hankali ta gyaÉ—a masa kai idanun ta cike da baccin gajiya suke lumshewa sai dai kalmar da ya faÉ—a ya sa ta wara idanun ta da sauri ta dube shi tana son sake jin me ya ce ?

"Wanne Suna kin ka zaɓarwa ɗiyar mu na bar miki zaɓi dan saboda kawai na gwada miki kaɗan dagga farin-cikin da nake ciki.

"Da gaske kake ?
Ta tambaye shi tana narkar da idanun ta cikin nasa .

"Da gaskiya Fatima na bar miki zaɓin sunan ɗiyar mu mai darajja '

" a sa mata Yakaka .

Sautin da ya taso daga ƙasan ran ta ya subto akan laɓɓan ta .

Shiru yayi yana kallon ta kafin yayi magana ta katse shi ta hanyar cigaba da cewa "indai dai har ka bani zaɓi to a sa mata sunan Yakaka Yayata .

"Babu shakka ta cancanta domin kuwa ita ce Mafarin silar haɗuwar sa da Fatima-zahra ba domin ita ba da bai samu Fatima ba bare har ta haifa masa 'yar da yake riƙe da ita yanzu a hannun sa a ƙarshe kuma ita ɗin uwa ce ga 'ya mafi soyuwa a gare shi da har abada baya zaton za'a samu mafiyin ta wajen matsayi a cikin 'ya'ya .....

Tunanin sa bai yanke ba ya juyo yana fuskantar Falmata riƙe da Babyn a hannu yace "Meye Sunan ta na ainashi..?

Cike da zumuÉ—i Falmata tace "sunan ta Amina.

Bai ce ƙala ba sai ya sake mayar da kai ga yiwa 'yar sa addu'a kafin bayan ɗan gajeren lokaci ya ɗago kan sa yana mai ɗora mata 'yar a jikin ta yace

" Sunan 'yar mu Amina riƙe ta da kyau 'ya ce a gurin ki sannan kuma 'yar uwa.

Da hannuwanta biyu ta rungume ta tana jin yanayin da yafi na ɗazu yana danne ta ta kasa tsayar da hawayen farin-cikin da yake sauƙa fuskar ta kamar yadda ta kasa ɗauke ido daga fuskar Amina .

Haka ma Biyamuradi Youssouf da yake tsaye akan ƙafafun sa hannuwansa duk biyu a zube cikin aljihun sa yana murmushin da yake bayyana haƙoran sa ya kasa janye ganin sa daga kan su kamar yadda yake jin ƙaunar su biyun tana fisgar sa tamkar wanda guguwa ta riska a tsakiyar rairayin hamada .

***

Daga nan É—akin da Falmata zata cigaba da zama kafin a sallame ta aka kai ta bayan nan Hajiya Umma da har yanzu bata tafi gida ba ta shiga inda suke ta mata sannu sannan ta sake mata addu'a ita da Amina kafin ta bar asibitin .

Sai kuma ta fara amsar waya daga Iyaye da dangin ta na Nigeria har dai zuwa lokacin da likitoci suka buƙaci da a bar ta ta samu hutu mai yawa kar a takura ta.

***

Daga lokacin da Doctor Hamza ya ga har dare yayi bai ji wani labari ba daga iyayen sa sai ya fahimci Sofi ta rufe zancen duk abunda ya faru bata faÉ—a ba .

Dan haka shi sai ya yanke shawarar sanar da iyayen su da kansa dan haka a daren ranar bayan sallar isha'i ya hada conference call da Baba Prof da Amne da Khaalty Rahima da Momy Kori da shi kan sa Baban Sofi.

Bayan duk ya gaishe su sai ya nemi da su bashi dama zai musu bayani.

Nan ya shiga basu labarin duk yadda kome ya wakana a tsakanin sa da Sofi tun daga farko har ƙarshe .

Kafin ya gama Sallallami da kukan Momy kori tare da Amne ya cika wayar .

Sai da kyar Baba Prof ya sa suka yi shiru domin shi da kansa Baban Sofi ya gaza cewa kome kawai kamar ruwa ya cinye shi saboda tsabar shiga razana da muzanta shi da Sofi tayi.

Ɗan taƙaitatcen Bayani Baa yayi akan lamarin da ɗari-cikin-ɗari ya goyi bayan hukuncin da Hamza ya ɗauka ya ɗora da cewa "tunda har dai abu ya zama da neman aikata kisan kai to babu shakka ba amfanin zaman rabuwar ita tafi dacewa.

Matsanancin kuka Momy Kori ta sa cikin rishin kuka take sanar da su cewa ita har kawo yanzu ma da ake wannan maganar bata ga Sofi da idanun ta ba Sofiya bata zo gida ba to ina ta tafi ?

"Ta tafi ko'ina ma Kori , ina mai tabbatar miki da cewa Safiya ba za ta zo ta zauna min a gida ba domin nima ba zan zauna da mashayiya kuma makashiya ba tunda irin rayuwar da ta zaɓarwa kan ta kenan to tafi duk inda za ta tafi tayi rayuwar ta amma ni dai ban amince ta zo gidana Alhaji ka shaida ni na cire Safiya daga cikin 'ya'yana' ku kuma ina mai baku haƙuri kan abunda ya faru ita yarinyar ma dan Allah a bata haƙuri ita da iyayen ta .

Daga haka Baban Sofi ya yanke ƙiran daga ɓangaren sa .

Duk son kai irin na Momy Kori yau sai ta gaza kare 'yar ta haka tana ji tana gani saki Uku ya tabbata tsakanin Sofi da Hamza sannan kuma dole ta bada haƙuri ga su Amnee da shi kansa Doctor Hamzan da ya rasa gudan jinin sa sannan ta ajiye wayar .

Daga nan suka cigaba da jimantawa tsakanin sa da iyayen sa inda Amnee ta nuna son Yakaka ta zo gida a kula da ita amma tun ma kafin ta gama magana Baba Prof ya nuna rashin amincewar sa hujja da cewa ai shi Hamzan likita ne dan haka zai fi kowa lura da ita dole Amnee ta haƙura ita kuwa Khaalty Rahima daman bata cewa kome sai addu'a kawai tayi ta danne duk wata damuwar ta saboda kara .

Daga nan aka yanke shawarar cewa jibi Amnee da Zainab za su tafi Abujan daga nan su haÉ—u da hafsa idan sun duba Yakaka da jiki daga nan sai su dawo Kano su wuce Niger gurin Falmata .

Su Hafsa zasu dawo bayan suna Amnee kuma za ta É—an yi ko da sati biyu ne tana kula da Falmatan .

Kafin kwanaki biyu zance ya gama baza dangi kan abunda Sofi ta aikata na yunƙurin kashe kishiyar ta kuma ta gudu ba'a san inda take ba.

Amnee sun je Abuja tare da direban su a babbar motar da Amnee ta cika kusan rabin ta da kaya .

Sun kwana a gidan Doctor Hamza ta sake rarrashin takwarar ta Yakaka sannan ta bata kayan gyara da tarin wasu turarurruka sannan ta sanar da ita sakon Prof da yace cikin satin nan za'a zo a shirya mata kayan ta a gidan .

daga nan kuma sai suka wuce Maradin Niger da tarin kayan ƙamshi da gyaran jiki tare da kayan jarirai masu kyau da tsada  da Amnee tayi tanadin su musamman domin Falmata da zata haihu kayan gyaran tafiyayyu ne daga Chad .

Can a Maradi suka ga tarba irin ta saraki sai nan-nan ake da su ana sauƙe musu kabbakin arziki.

Daga Zainab har Hafsa sai da suka yi santin kyaun sashin Falmata da irin gatan da ake mata babu abunda yafi burge su irin tarin hadiman da take da su da ko yaya ta motsa sai sun mata sannu girma irin ta sarauta sai gidan sarauta .

Lokacin da Yakaka ta samu labarin cewa jaririya Sunan ta ta ci har sai da tayi kuka dan farin-ciki .

Doctor Hamza ma ya ji daɗi ya kuma musu fatan Allah ya ƙara musu zumunci a ƙarshe yayi alƙawarin daga ya ɗau hutun sa nan da wasu watanni cikin shekara mai zuwa zai kai Yakaka har Niger ta gano takwarar ta .

Ranar suna kuwa Al'umma da suka taru ba'a ce Falmata bata da dangi a Niger ba.

A gurin taron suna dangin suka dunga tsurkun tururuwar zuwa duba Hajiya Mama wacce jinya ta sarƙe ta sakamakon wasu munanan ƙuraje da suke feso mata duk a ƙafafun ta bayan hawan jini da ciwon zuciya da suka mata rubdugu bata ko iya tafiya gaba ɗaya rayuwa ta mata juyin waina a tanda .

Kowa ya fito daga sashin sai yayi gulmar sakayya ce take gani tun daga nan duniya .

Wacce irin ta Maimounatou ɗiyar sarkin Agades ma ta samu sakamakon mutuwa da Mahaifin ta yayi a tun jinyar da ya afkama sanadin mummunan abun kunyan da ta aikata kan yunƙurin kashe Mijinta a halin yanzu kuwa rayuwa ta mata atishawar tsaki batta ga tsuntsu batta ga tarko .

'Yayan Hajiya Mama kansu gaba É—aya basu da sakewa a cikin taron sunan duk kuwa da cewa sun zo sun kuma kawo kayan jaririya da na uwa irin na alfarma .

Da kaya sai da Falmata ta rasa gurin zuba su tsakanin wanda Mijin ta tayi mata da wanda iyayen sa suka mata da wanda Iyayen ta suka kawo mata da kuma na 'yan uwan sa ga kuma na dangi da abokan arziƙa .

***

Bayan suna da Zainab da Hafsa da zasu koma kayan niƙi-niƙi aka haɗa Su da shi .

Ita kuma Amnee ta zauna kula da Falmata da ta dage tana lura da ita saboda haihuwar da tayi wani ɗam rami na musamman na turara jiki ta sa aka mata a cikin uwarɗakin Falmata kamar yadda al'adar su take su basu cika shan magungunan na mata ba sai gyaran jiki tsaftar sa da ƙyalƙyale fata suka fi bawa muhimmanci .

Gefe guda kuma ita ma Hajja ta dage da nata gyaran irin na matan ƙasar Hausa da su kuma suka fi bawa shan kayan ɗa'a muhimmanci .

Kafin sati biyu Fatar Falmata ta zama kamar bayan tarwaɗa yayin da wani fitinannan ƙamshi ya zauna mata a jiki 'yar kiɓar shayarwa da tayi ta amshi jikin ta sai ta koma kamar irin hamshaƙan matan nan da suke kan ganiyar ƙuciyar su duniya kuma ta juya hasken ta akan su tana haska su .
Chapter 266 · 0% Book details