← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 269

Sashe 58

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   Cikin rashin jin daɗi falmata ta karya wuya ,
      Kai amma banji daɗi ba yakaka mutumin yana da kirki , tun da kika fara aiki a gidan su muke samun jin daɗi .,'

    Uhum ,!
     Cewar yakaka tana mai miƙewa
Bari na sauya kaya na nazo kan aiki ,!

Chan ƙasan kayan ta a kusa da kuɗaɗen niger da agogon sa da ya bata a haɗuwar su ta farko ta ajiye hoton tare da kuɗin hannun ta , a ran ta tana jin hoton sa da agogon sa zasu zame mata abun ɗebe kewar sa kafin samy baby ta dawo mata da shi kamar yadda ta alƙawarta mata !

Washagarin ranar samy baby ta samu yakaka , suka je asibiti ƙarƙashin jagorar wani nurse abokin hulɗar samy baby , tare da taimakon sa aka yiwa yakaka allurar hana ɗaukar ciki , ba tare da an tsawaita binciken ina mijin ta ba ?, tare da tunasar da ita dawowa sake yin wata allurar duk bayan watanni uku !

  Yakaka bata ji ko ɗar ba sai ma farin ciki da take ji chan ƙasan ran ta a domin kan hanyar su ta zuwa asibitin samy baby ke sanar da ita a yau ɗin nan zata garzaya barracks wurin nuhu inda zata samu cikakken bayanin inda youssof yayi bigire idan ma ta kama har inda yake sai ta kai yakaka ! har ɗakin kwanan sa ,! Ah to meye bariki ce fah !  A haka suka tsaya .

Sai dai tun dawowar su daga asibitin yakaka ta gaza tsinana wani abun kirki , saboda wani irin murÉ—awa da marar ta take ta sake , ga duhu-duhu da take gani a idanun ta ,! Gaba É—aya jin ta take marar lafiya ,' dan haka ta zari nera dubu biyu cikin kuÉ—in ta ta bawa madam saly tace bata jin daÉ—i zata je ta kwanta ,"
    Jiki na rawa madam saly ta warce dubu biyu tace ta je ta kwanta za'a yi aikin ta .!

   Kafin azahar yakaka ta jigata saboda tsabar ciwon ciki da kwankwaso ta takure a guri ɗaya sai murƙususu take  , ! Larki ce ta shigo ɗakin ta tadda ta a galabaice ," nan take tambayar ta meye yake damun ta tace ciki da baya ,'
        Cewa tayi ta bada kuɗi a anso mata magani ƙila ciwon cikin al'ada ne daman yana irin haka ,!

   Da rarrafe ta jawo jakar kayan ta ta fiddo da duk kayayyakin ta zaƙulo damin kuɗin ta , ta fidda naira dubu ɗaya ta bayar a anso mata magani ,!

Ta koma ta kwanta gami da runtse idanun ta !

   Da kan ta larki ta je ta amso mata magungunan saboda ta hango moriya , ta kuma ƙulla abunda ta ƙudurta cikin ran ta ,"

Ta tsaya a wani É—an shago ta sayo mata ruwan leda guda biyu !

Lamoo ! ta samu yakaka tana sauraran gangar jikin ta ,"
   Ta taimaka mata ta zauna tare da ɓalla mata maganin ta miƙa mata ruwan ta kora , ta koma ta kwanta cikin wani sabon yanayin rashin kuzari da take jin kan ta a ciki .

Larki ta ɗan saci kallon jakar kayan yakaka , ta gan ta a buɗe yadda ta bar ta bayan ta miƙo mata kuɗin !

Yaks bari na tattara miki kayan naki , ai ba'a bar kayan haka ba ko dan gudun masu dogayen hannu kin san É—akin namu babu tsaro ,' ,

Idon ta a rufe ta É—an gÆ´aÉ—a kan ta ,!

Da azama larki tayi wa jakar kayan rumfa ta bada baya ga yakaka wacce idanun ta ke rufe ,"
     Kayan ta fara mayarwa bayan ta wawuso kusan rabin kuɗin da yake cikin jakar ta chusa a lalitar ta ,"

  A ranta tana cewa ! To meye ? Ta san yarinyar sabuwar hannun ce dan haka tana kan ganiyar ta , dan ƴan waɗannan kudaɗen ba kome bane a wurin ta , ƙila ma bata san yawan su ba daga ta shafa ta ji sun ragu , fita zata sake yi wurin masu bata ta sake samo wasu , Dan haka gwara itama ta samu ta wawushe nata , ko ta samu ta kashe wasu matsalolin ta,  ta kuma  farfaɗo da jarin ta na goro da taba !

Da wannan zancen zucin ta kammala maida kayan tsaf ! Ta juyo da kallon ta kan yakaka domin ta sanar da ita ,"

Sai taga bacci ma take da alama ta samu lafawar ciwon !

Tura jakar tayi inda suke ajiye ta cikin ranta tana ayyana ta samu hujjar da zata kare kan ta ko da ace yaks tayi cigiyar kuÉ—in ta ," cewa zata yi bata san wanda ya É—auka ba ita dai ta gyara mata kayan ta fita ,!

Sai bayan la'asar yakaka ta farka ! Daga baccin da yake cike da mafarkin biyamuradi da soyayyar sa da ta maƙale mata a zuci !  Watsa ruwa tayi tayo alwala , ta haɗa sallolin azahar da la'asar tayi su ,

Tsumu tayi a zaune kan ɗankwalin ta da ta shimfiɗa tayi sallah bisa ,  ta rasa abun da ke mata daɗi .

Babu laifi taji sauƙin ciwon cikin sai dai sakayau take jin ta ga wani irin ƙuncin zuciya da take ji uwa uba kewa tare da ƙaunar youssouf da take tokarin ta a duk bayan daƙiƙa guda wanda ko da wannan aka bar ta kawai ya isheta cuta ! Ji take kamar ta shekara da barin ganin sa haka ta shafe tsawon daren jiya tana jin kewar sa ta gaza bacci sai juye-juye ,

Cikin sati biyu kachal da suka yi tare da juna ya mata mugun sabo da soyayyar sa mai tsayawa a zuci , duk da cewa soyayyar ba da baki yake ambato mata ba , a aikace yake idar mata , shiyasa gaba ɗaya take jin kewar sa hatta a fatar jikin ta da kowanne saƙo da lungu na jikin ta ,! Har gizo hannuwan sa ke yi mata a sassan jikin ta ,' ko yaya ta rufe idanun ta fuskar sa take gani tana mata gizo , shi ba ma'abocin murmushi agare ta bane , amma yanayin kamammiyar fuskar sa yana bala'in burge ta , babu shakka a rayuwar ta bata taɓa ganin mutum ɗan gayu mai kyau irin sa ba !

Yunwa take ji domin rabon ta da abinci tun karin safe ," sai dai kallo É—aya tayi wa robar abincin ta da take ajiye a gefe wanda take da tabbacin wake da shinkafa ne a ciki ta É—auke kai , ' abinci daddaÉ—a bakin ta yake kwaÉ—ayi !

   Jakar ta ta jawo domin ta ɗauki kuɗi taje sayan abinci wurin su kolo

Kallo ɗaya tayi wa kuɗin tasan an taɓa su , da azama ta fiddo su ta ƙirga ta ga dubu goma sha bakwai ne a maimakon dubu talatin da huɗu,!

Jujjuya kuɗin take idanun ta sun ciko da ƙwalla , tana da buri akan kuɗin , so tayi ta kai falmata babban asibitin ido a duba ta domin kwana biyu idon yana ɗan matsa mata da ƙaiƙayi kuma suna yin jaa , cikin ran ta bata fidda rai watarana falmata zata gani da idanun ta ba , ji take watarana falmata zata ga hasken da yake wadace cikin sarari duniya , watarana zata ga fuskokin jama'a , zata ga fuskar ta kamar yadda kullum ita take ganin ta !
, sannan idan kuɗin ya rage ta jaa jari ta fara soya doya da kwai da yammaci zuwa dare , kafin dawowar bature kam silum domin ta ɗanɗani daɗin kuɗi da ƴancin da suke samarwa ga mai su ! Baza ta iya sake zama irin na tsananin talauci tare da walaƙancin da ake musu sanadin babu ba !  idan ya so sa dunga raba ribar tare da madam saly , ta san baza ta ƙi ba !,

Amma shine wani azzalumin marar imani ya kwashe mata kuÉ—in ?! Tunanin larki ya faÉ—o mata arai , ko ita ce ta É—auka ? Amma larki anya zata É—auki kuÉ—in ta ?

Koma waye na bar shi da Allah ! Ban yafe ba .

   Ta furta hakan a sarari tana share guntuwar ƙwallar ta , ta zari naira dubu ɗaya , a ranta tana tunanin chanjin ta da ya rage hannun larki , bata ,  bata ba ko maganin na dubu ɗaya ɗin ne ? Ita dai baza ta tambaye ta ba idan ma ta cuce ta dan kan ta ! ¿

Kai tsaye ta wuce rumfar su kolo , ta miƙa kuɗin tace a bata tuwon shinkafa da miyar yakuwa , malmala biyu da nama guda huɗu ,

Kolo ta miƙo mata tuwon a naɗe cikin leda tare da miyar a wani ɗan kwanon roba bayan ta gargaɗe ta akan ta dawo musu da kwanon miyar  !

Kai tsaye wurin wanke wanken falmata ta wuce , ta tadda ta wanke-wanken sun taru tana ta faman wankewa ana ƙaro wasu , saboda yamma tayi lokacin ciniki ne kuma an kusa gama sayarwa ! Alamun gajiya ya bayyana a gare ta ,ga gumi da ta haɗa fiye da rabin zanen ta a jiƙe yake da ruwan wanke-wanken! Ajiye abincin hannun ta tayi a gefe !

Cikin ruwan kumfan ta sa hannu gami da zare soson daga hannun falmatan ,
      Kawo nayi sauri na gama , kin ci abinci falmata ??

Da murmushi a fuskar ta ta cire hannun ta a ruwan gami da goge hannun ta a jikin rigar ta ,'
    Ban ci ba yakaka , kin ga aikin yayi yawa wanke wanken ina yi ana ƙaro wasu ,"
    Amma yanzu zan samu nayi sallah sai na ci ,"

    Da ido kawai yakaka ta bita lokacin da ta matsa jikin fanfo ta fara alwala ,"

   Ɗan kwalin ta ta shinfiɗa tayi sallar azahar da la'asar akai , bayan ta idar , tace yakaka ta bata abincin ta ,da ta rufe shi da faranti a gefe ,"
Chapter 58 · 0% Book details