Sashe 253
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wata irin tsawa Doctor Hamza yayi da ba ita Sofi kaɗai ba ,hatta Sam sai da yayi zillo yana ɗan kuka ya koma bayan kujera ya laɓe.
"Kar ki ce min kome Sofi , bana buƙatar jin ƙaryar ki ta banza abunda nake so kawai shine ...
Ɗan jim yayi yana kallon ta yadda ta wani irin saƙare cikin rashin madafa matsanancin tashin hankali gami da wani nisassashen yanayi shimfiɗe akan fuskar ta inda take bata motsa ba , ba domin tazarar dake tsakanin su na da ɗan yawa ba da babu abunda zai hana ya iya jin sautin bugun zuciyar ta..
"Ki tafi gida Sofi .
Ya ce da wata irin kakkaurar murya yana É—auke ganin sa daga kan ta ya zagayo da Yakaka daga bayan sa yana sake bin jikin ta da kallo kamar dai yana yiwa Sofi nuni da mummunan laifin da ta aikat ,yana kallon fuskar Yakaka tamkar ita yake yiwa maganar ya É—ora da cewa.
"Ki je gida akwai buƙatar ki sake samun ƙarin tarbiyya irin ta masu hankali da cikakkiyar koyarwar Islama ko ɗaya ba zan iya sake jimirin ɗaukar salon haukar da kike yi ba .
"Ki tafi gidan ku Sofi.
Ya furta hakan da buɗaɗɗiyar muryar da yasa kuka tahowa Yakaka da sauri ta shige cikin jikin sa tana zagaye shi da hannunwan ta , matsanancin tsoro na ɗarsuwa a ran ta ganin ɓacin ran sa Mai tsanani irin wanda ta daɗe bata gani ba.
"Ga Sofi kenan matar son sa da ita ce ta kora ta layin.
ina ga ita kuma ? Da ta yaga kayan ta da kan ta ? Watakila idan ya gama da Sofi ya dawo kan ta "shikenan Hajja ta jawo mata .
Hannun sa da ya sauke a bayan ta yana É—an buubbuga ta alamun rarrashi yasa ta ji nutsuwa ta fara dawo.mata da sauri ta É—ago kan ta tana kallon fuskar sa da shi ma ita yake kallo.
Zata yi magana ya hana ta ta hanyar jaan hannun ta zuwa hanyar ɗakin sa ba tare da yace ƙala ba
A ɗan tsorace ta dubi sashin Sofi har lokacin tana nan a tsaye inda take tamkar an dasa ta kallo ɗaya ta yiwa fuskar ta tayi saurin janye idanun ta tana jin yadda zuciyar ta ta doka da ƙarfi babu shakka ta hango wani lamari mai kaifi daga cikin idanun Sofi da suka tara ruwan hawayen da basu kai ga zuba ba '
"Ki tafi tare da dabban da kika kawo min gida bana so na fito na ga É—ayan ku .
Doctor Hamza ya furta hakan kafin su kai ga shiga É—aki.
Wani irin tsuma jikin Sofi yake so take Allah ya kawo wani ya wanka mata marin da zai farkar da ita daga mummunan mafarkin da take yi "Doctor Hamza ne da kan sa yau yace ta fita ta bar gidan sa ? Razanar da ta tsinka mata gudun jikin jikin bai wuce dalilin korar ta ta ba " akan wannan kuchakar 'yar gudun hijirar 'Yar talakawa 'yar ƙauyen ne Hamzan ta ya kore ta?
Kai ina ƙarya ne lokaci yayi da zata farka daga gyangyaɗin da take yi da har yasa tayi saken da wankin hula ke shirin kai ta tsakar dare akan Yakaka.
Ihu take son kurmawa amma tana ganin a halin da take ciki babu lokacin ihu , da gudu ta taka ta hau sama É—akin ta mukullin motar ta kawai ta É—auka sai fa wani siririn mayafi da ta rufa akai ta fita daga gidan .
Wani irin gudu take yi a kan titi da ya zarce ka'ida tana yi tana dukan kan ta da hannun ta É—aya .
Lokacin da ta shiga gidan su kai tsaye falon Momy kori ta zarce wacce bata san da shigowar ta ba sai da ta ji ana mata rotse a falo ta yunƙura daga kwanciyar hutun da take yi akan gado ta fito tana cewa "meye haka ? Meke...'
Sauran kalmomin sun maƙale ganin 'yar ta Sofiya ce take mata wannan aika aikar duk ta farfasa mata show-glass
Da gudu ta ƙarasa tana riƙo ta Amma sofi sai sake fisgewa take da alamun fitar hayyaci a tare da ita .
Hankali tashe take kiran sunan ta
"Sofi , Safiya ke Safiya meye hakan ? Kin yi hauka ne dan ubanki.? Nace hauka kike ?
Ganin taƙi saurararta yasa Momy Kori ta cire hannu ta wanke ta da marin da yasa Sofi wani irin juyowa a fusace ta tunkuɗa Momy kori tayi zaman dirshan a kujerar gefen ta .
"Momy ki rabu da ni wallahi sai na tarwatsa rayuwar Yarinyar nan yadda nake tarwatsa wannan show-glass din naki.
"Wallahi sai na kashe ta , kafin ta kashe min aure ta raba ni da Hamza a ƙarshe tasa baƙin-ciki ya kashe ni .
Wani irin kallo Momy kori take bin ta da shi da yake nuni da zunzurutun takaicin da take ciki da kyar ta buÉ—i baki ta ce .
"Yanzun nan ke dan Ubanki akan kishiya kike wannan haukar ? Akan kishiya kika min wannan ɗanyen aiki ? Kika min wannan ɓarnar Sofi ? To billahil azim sai kin biya kuɗin abubuwan duk da kika rotsa dan buhun ubanki.
Miƙewa tayi tana jin gara ta bar gurin kafin zuciya ta ciwo ta ta jawo ta ta fara kirɓa .
Tana barin wajen Sofi da take tsaye ta silale jaɓar ta zauna a ƙasa kafin ta saki wani irin ihun da farkon sa kururuwa kafin ya miƙa da wani irin Kukan da yake siƙewa ta maƙollotan ta .
...[4/15, 8:07 PM] +234 706 503 6187: MAFARI
.......HARGITSIN RAYUWA
Umm'muaz
54b
Ta É—au tsawon lokaci a haka kafin ta ji hannun ya dafa ta da sauri ta É—ago kai cike da zumuÉ—in son ganin Doctor Hamza ne ya zo rarrashin ta .
wacce ta gani yasa ta saurin kawar da kan ta tana turo baki gaba .
Momy kori ta ƙarasa zama akan kujerar dake daf da ita tana jin tausayin 'yar ta na daɗa mamaye ta shi so jarabbata ne sannan muddin idan Sofi ta gado ta wajen matsanancin kishi to fa tana iya hasashen irin ciwon da take ji a rai wanda ita ma da a ba ita aka yiwa kishiyar ba amma tunda aka yiwa Sofi take cikin jin takaici a duk lokacin da ta tuno .
"Sofi kukan nan ya isa haka ki nutsu ki faɗa min me ya faru ? Ki min bayani dan na cire ki daga wannan halin sanin kan ki ne ba zan juri ganin ki haka ba .
Ganin Momy kori ta ɗan sauko yasa Sofi gyara zama ta shiga rattaba labaran da suke cike da ƙarairayi kan irin tozarcin da Yakaka take sa wa Doctor Hamza na yi ma ta tana yi tana sharar ƙwalla a ƙarshe kuma ta juya baya ta kwaye rigar ta ta nunawa Momy kori inda kwalba ta yanke ta tana cigaba da cewa .
"Wallahi Momy kin ga inda ta sa wuƙa ta soki bayana kawai dan ta ga yana ɗaukar hankalin Doctor , da kokuwa fa ta kama ni tuƙuru Momy ....
"Dan Ubanki ni rufe min baki ke kina me har wannan afiruwar yarinyar me kama da kazar mayu zata kama ki da kokuwa bakya shaƙe shegiya ki mata ƙamshin mutuwa ?
"Amma kuwa albasa bata yi halin ruwa ba cewa nake da wayon ki sarai a gidannan kin san dai kishiyoyi uku na kora idan aka haɗa da wanɗan da zamanin ku na ƙanana kuwa su rai takwas ne ras ai ni bana barin kishiya ta rufa kwana arba'in nake saita mata hanya ko tafi kuturwa naci kuwa.
"Amma shine ke dan sakarci za ki sakarwa kishiya baki har ta raina ki tana rarumar ki da kokawa kamar wata sa'ar ta ? Gaba-gaba kuma ai sai dai ta zane ki da bulala, dan ubanta da za ta ce ba za kiyi kiwon kare ba gidan na uban ta ne ko na uwar ta ?
"Shi kuma Hamzan da yake ya zama shanyayye sallamamme shine har zai koro min ke yace ki fita ki bar masa gidan ? To bai isa ba , Ai auren ku ke da shi mutu ka raba tunda ya zama sanadin da kika je kika huh-hura jikin ki haka kika yiwa kan ki illa ai kuwa bai isa sakin ki ba muddin ina raye ubansa ma na raye .
Langaɓe kai Sofi tayi tana kif-kifta ido irin ta wanda gaskiya ta yiwa yawa yake kuma buƙatar a bi masa kadu .
Kwafa momy kori tayi kafin ta buÉ—e murya tana kwala kiran mai aikin ta
"Lami ke Lami wai bakya ji ne ? miƙo min wayata ki kuma zo ki tattara gurin nan ki gyara mayyar TV ke da bakya gajiya da kallo sai ki tashi daga gaban Tv haka ya isa .
Da gudu wacce aka ƙira da Iyami ta miƙo wayar ta kuma dauƙo tsintsiya ta fara aikin gyaran gurin .
Layin Doctor Hamza Momy Kori ta shiga nema amma har ta tsinke bai ɗaga ba , a ƙufule ta sake ƙira wannan karan ma sai da ta kusa tsinkewa Yakaka wacce take gyaran ɗakin inda su ka sha kokuwa ita da Sofi ta ɗaga wayar ganin mai ƙiran "Momy ne kawai a rubuce dan haka tayi zaton Amnee ce .
"Hello tace da 'yar muryar ta mai sanyi .
"Tsam Momy Kori tayi tana sake samun tabbaci kan duk abinda Sofi ta faɗa mata jin Yakaka ce ma ta ɗau wayar Hamzan lalle Yakaka ta riƙa .
"Dan Ubanki ina mai wayar yake ? Ko nima iskanci za ki min ? To bari ki ji ko karuwar uwarki Mayya bata Isa bare ke Dallah ni ba shi wayar nace .
Ta ƙarasa tana sakarwa Yakaka wata tsawar da ta razana ta ba shiri ta sauƙe wayar ta ajiye dai-dai da shigowar Doctor Hamza wanda ya sha artabu da Sam kafin ya fitar da shi daga gidan .
Yana shigowa wayar ta sake ɗaukar kiɗa ya ƙarasa ya ɗauka ganin mai ƙiran na sa ya sa shi yin tsaki a sarari , har wayar ta tsinke bai ɗaga ba .
Nan take wata ta kuma shigowa.