Sashe 51
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gudun da yake ba na hankali bane , bai ko tsoron dare da yadda garin yake haɗe da hadari sai walƙiya ake yi, bai tsagaita ba sai da ya shigo da'irar birnin maiduguri lokacin sha ɗaya da rabi na ɗare har ta gota, cikin garin babu kowa kan titi sai sojoji ƴan uwan sa da suna hango motar ta sa mai ɗauke da fentin launin kakin soja suke buɗe hanyoyin da suka bi suka tottoshe saboda tsaro, shawagi ya fara yi da motar marar sa na cigaba da karta masa har yana ganin duhu-duhu , ya haɗa zufa sai tsuma yake yi, ina zashi ? Shi ba wani sanin kan garin yayi ba guri ɗaya zuwa biyu ya sani , daga barikin garin wurin abokin sa , sai kuma wurin sayar da burkutu ,
karya kan motar yayi ya lokacin da ya ji kamar an umarce shi da ya tafi zuwa wurin sayar da burkutun , a chan zai samu wacce zata iya kula da shi ,
Yana yin fakin ɗin motar ya fito ba tare da ya damu ya rufe murfin ba ya fara taku yana bin hanyar da zai sada shi da cikin gidan hannun sa ɗaya ya riƙe marar sa , da layii ya ƙaraso cikin rumfar , sai dai bakikkirin ya tadda wurin , babu kowa an watse kujerun gurin kansu a tattare suke, wani irin jiri ya ji yana kwasar sa , ya tabbata yau mutuwa zai yi ,
Tun shigowar sa yakaka wacce bata daÉ—e da kwanciya ba, bayan ta tattara cikin shagon ta kintsa kome, sai dai ta gagara bacci saboda tsinkewar da zuciyar ta ke yi wanda ta danganta hakan da tsoron tsawa da walkiyar da ake yi ,
Taji shigowar sa a tun takun sa na farko a cikin shagon , tsumu tayi cikin zanin rufuwar ta , tana sake jin bugun zuciyar ta na ƙaruwa da duk wani motsi da yake ,wanene cikin daren nan ? Koh wani ne yayi mantuwa ? kaƙƙarfan kamshin turaren sa shi ya ziyarci hancin ta , kamshin da ya ɗauki tsawon kwanaki a hancin ta kafin ta daina jin sa a wancen haɗuwar ta su ,'
Kamshin na musamman ne dan haka sai ta zame abun rufuwar daga kan ta dan ta samu damar shaƙar ƙamshin da kyau cikin ran ta kuma tana ƙwaɗayin ganin fuskar sa ,
Da É—an tazara a tsakanin su domin shi yana tsaye daga bakin kofar ta ciki yana fuskantar inda yakaka ke kwance sai dai bai kai ga fahimtar mutum ba ce saboda babu wadatar haske kuma baki É—aya bai cikin hayyacin sa ,
Sosai ta buɗe fuskar ta tana ƙare masa kallo ta cikin ɗan hasken da yake shigowa ɗakin da taimakon hasken hadarin da ya gangamo cikin duhun daren , bata gani ainahin kamannin fuskar sa sai dai siffar jikin sa da take gani , gani tayi ya sunkuya yana riƙe da cikin sa
Tsawa aka yi tare da walƙiya da ya haddasa yakaka tsorata har ta miƙe zaune , motsin ta ya sanya shi ɗago kan sa ,walƙiyar da aka sake yi ta hasko masa farar fuskar ta ta zuba masa ido tana kallon sa daga inda take zaune ,'
Wani tsallen farin ciki zuciyar sa tayi, da sassarfa ya fara takawa yana nufar ta tamkar mayunwacin zakin da ya kwan uku ba abinci ,
Baya ta fara yi akan bencin tana matsawa , cikin in'ina tace ,'
Babu ruwa ya ƙare ,mun ruga mun tashi an gama aiki sai gobe da rana ,'
Kalaman ta sun zo dai-dai da ƙarasowar sa gaban ta , baiyi wata wata ba ya miƙa hannu ya ɗago ta daga kan bencin ta hanyar ɗago kafaɗun ta ya tsaida ta akan kafafun ta , ba kuma tare da ya ce da ita ƙala ba ya juya tare da jaan hannun ta da ya riƙe nufin sa ta biyo shi ,'
Waiwayowa yayi jin ta turje tana ƙokarin zame hannun ta da ya riƙe tamau ,
Cikin wata irin dusasshiyar murya da take fitowa daga ƙarƙashin maƙoshin sa yace ,"
Ki taimaka min kar na mutu ko nawa ne zan biya ki ki taimake ni ,"
Daga haka ya juya yana jaan hannun ta , bata yi turjiya ba ta fara bin sa kafafun ta ko takalma babu ," kalmar taimako da ya ambata tare da wani abu da take ji yana fisgar ta a game da shi ya sa ta bi shi ,'
Sun zo tsakiyar filin gidan aka fara yayyafi ,' yakaka ta sake tsayawa saboda gargaɗin da zuciyar ta ke yi mata akan yunƙurin bin mutumin da bata sani ba cikin dare zuwa wurin da bata kai ga sani ba wai shin ina hankalin ta yake ne ??
Juyowa yayi aka saki tsawa da walkiya tare da ƙaruwar ƙarfin ruwan sama , haɗa ido suka yi ta hasken walkiyar suka kalli juna na wasu dakikai ba tare da kowannen su ya samu damar magana ba ,"
Cikin idanun sa ta hango ruɗanin da yake ciki , tare da wani abu da ya taɓa zuciyar ta da bata kai ga fahimtar yanayin sa ba , sai dai koma menene yayi tasiri matuƙa wurin raunana mata zuciya ta yadda ta ji kowanne irin taimako ne zata iya yi masa , zata mishi kome yake so , tana nufin kome ,
A bangaren biyamuradi youssouf kuwa shi ma kallon cikin idanun ta ya taɓa shi , ya hango rauni tare da zallar ƙuruciyar da ke tattare da ita ,sai dai sun gaza tasiri agare shi domin daga lokacin da ya riƙo hannun ta ya fara jin wani irin nutsuwa tare da ɗaukewar ciwon da yake ji ,har da wani danshi danshi yake ji a ƙasan ran sa wanda ya tabbatar masa ita zata iya fidda shi halin da ya ɗauki tsawo awanni ashirin da huɗu cikin sa , yana jin zai iya biyan ta ko nawa ne domin ta yadda da shi ,
Ganin bata ce kome ba ya sa shi ya cigaba da tafiya riƙe da hannun ta sai dai wannan karon tare suke jefa kafafun su a jere tamkar sabbin masoya cikin samun amincewar yakaka da ta hakiƙance zata taimaka masa , "
Bai saki hannun ta ba sai da ya dangana ta da cikin motar sa ba tare da fargaban kome ba yakaka ta shiga ta zauna tana shaƙar ƙamshin turaren sa da ke da matuƙar tasiri agare ta ,"
Da ƙarfi ya fisga motar wanda yayi dai-dai da fara saukar ruwan sama da matuƙar ƙarfi ,
wani ƙaramin Guest house ya nufa wanda yake ganin sa akan hanyar shigowa gari , cikin su babu wanda yake ce da ɗan uwan sa ƙala ba har suka isa , bai wani sha wahala ba wurinnsamar musu da ɗaki zamantowar sa jami'in tsaro ,
Riƙe da hannun yakaka wacce ta zamto tamkar rakumi da akala ya danna kai cikin ɗakin ,'
Daga lokacin da suka sanya ƙafa cikin ɗakin kome ya fara kasancewa nan ne mafarin hargitsin rayuwar su , sun gudanar da kome cikin amincewa tare da tallafin junan su , yakaka bata hana biyamuradi kan ta ba wanda ita da kan ta baza ta iya faɗin dalilin ta na sadauƙar masa da mutuncin ta ba ita dai ta san koma wanene wannan mutumin da ya kasance mutum na farko da ya fara kasancewa da ita a wani bigire kuma cikin wani yanayi irin wannan ,akwai wani al'amari mai girma a tare da shi .'
A bangaren biyamuradi kuwa tsintar kan sa yayi a wata duniya mai nisa wacce take tare da wani irin daɗi da sanya nishaɗi da bai taɓa jin makamancin sa ba , ji yayi ko da dakika guda baya fatan wani abu ya gifta da zai katse masa jin daɗin sa ,
Yana jin zai iya mallakawa yarinyar nan kome ta buƙata , idan ya ce kome yana nufin kome ."
Ta hasken ranar da ya hasko ɗakin ta tsakanin ɗan yalolon labuƙen ɗakin yakaka take ƙarewa fuskar biyamuradi kallo , komen sa mai kyau ne babu abun da ya fi ɗaukar hankalin yakaka irin jajayen laɓɓan sa ," tambayar kan ta take daman maza ma na shafa jambaki ? hannu take niyyar kaiwa fuskar sa ta ga ya buɗe idanun sa a firgice kamar ba wanda ke bacci ba ,"
Da sauri ta jaa baƴa tare da maƙurewa a jikin gadon ,"
Zama yayi yana me ƙarewa ɗakin kallo kafin ya waiwayo kan yakaka tare da wani irin kallo da ta kasa tantance ma'anar sa ya watso mata tambayar da ta shayar da ita mamaki ,"
Wacece ke ??????
Assalamu alaikum masoya, ku min afuwa da jinkirin da aka samu kafin zuwan wannan shafin , da kuma rashin baku amsoshi n sharhn ku a shafin baya duk hakan ya faru ne sakamakon aiyuka da suka sha kaina , ina fatan na wanke kaina da wannan mafi tsawon shafi da na rubuto muku ?? Idan haka ne nima kar ku min rowar sharhin ku ,' ku faɗi ra'ayoyin ku,akan wannan tafiya tamu, a wannan karon zan bada lokaci mu tattuna tare domin ƙarin armashi , na gaishe ku kyauta !!!
[6/24, 10:59 AM] +234 701 013 7848: MAFARI
Hargitsin Rayuwa
Umm"muaz
19
Wacece ke ??
Ni ni nice yakaka ,"
Ya ka ka ? Ya maimata sunan kamar me koyon magana ,'
Ina ne nan ? Waye ya kawo ni nan ? Me muke yi anan ??
Wannan karon a tsorace yakaka take kallon sa ,"kar dai mahaukaci na biyo ni yakaka na shiga uku ," ?
Tsawar shi ita ta katse mata tunani cikin hargagin su irin na soji yake sake maimaita mata tambayoyin ,"
Fashewa tayi da kuka cikin rikici ta fara cewa ," ni ka mayar da ni gida nima ban san ina ka kawo ni ba ,!
Tare da tarin wani al'amari da ya shallake tunanin sa ,' ya maimata tambayar ,'
  Na kawo ki ?
Eh ba kai bane jiya ka É—auko ni cikin dare ka ce zan taimaka maka shine ka kawo ni nan ,"