Sashe 143
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
har ta zo ta san me ake nufi da aure ta hanyar malamar da take koyar da ita wacce a farkon fara ɗaukar darasi a wajen ta take yawan yi mata bayani akan auratayya a addinance da yadda mace zata kula da kan ta da mijin ta ta fuskar auratayya ba tare da kunyar kome ba cikin rashin sanin ta hajja ce ta yiwa malamar bayanin ƙarancin ilmi da wayon falmata ta kuma roƙi da ta dunga mata darasi na musamman akan auratayya ,
A hankali yau da gobe ta fahimci manene aure , matsayin miji a gun matar sa da matsayin mata a wajen mijin ta ,
Ta shiga ruÉ—ani na sosai da har kawo yau bata fita daga cikin sa ba , " yaushe yakaka da Baban mama suka yi aure ?? Ita ba ta san lokacin ba kawai jin yakaka tayi da cikin mama .
Akwai tsoro me tafe da son bada kariya tare da kyautata zato ga ƴar uwar ta yakaka , haɗi da son tsaftace mama shi yasa a duk lokacin da tunanin hanyar da aka bi aka samar da mama ya taso mata , take yaƙar tunanin da ƙarfi da yaji , bata son wani abu da zai aibata yakaka ya raɓi tunanin ta ,
Kewa tare da ƙaunar ƴar uwar ta bai ragu ba ko kaɗan a cikin ran ta sai ma zurfafa da yake sake yi yayi mata ƙaton miƙi a cikin rai .
Rashin son suyi zaman auratayya irin na sauran ma'aurata da Biyamuradi ya nuna tsawon shekarun bai taɓa damun ta ba ,
Hasalima ta fi son hakan .
Zaman mama take , tana rayuwa ne a ƙarƙashin sa kaɗai domin mama , za kuma ta cigaba da tsayawa ɗauke da auren sa a kan ta har abada muddin tana tare da mama .
****
Daga niamey kai tsaye maraɗi ya wuce , bayan isar shi faɗa ya kai gaisuwa , kai tsaye ɓangaren sa ya nufa ba tare da ya shiga cikin gidan su wajen hajiya umma ba , yasan yanzu tana tare da jama'a masu neman taimako da ƴan barandar ta , sai zuwa yammaci zai shiga wajen ta zuwa lokacin ƙafa ta ragu a sashin nata ..
Tattaki yayi zuwa sashin sa da yake bigire guda na gidan , bayun da suke kai kawo a fada su na ta kai gaisuwa bayan waɗanda ke take masa baya tun daga ƙofar fada .
A bakin sashin sa suka jaa tunga saboda a tsarin sa bayi maza basa shiga ɓangaren gidan sa da matan sa ke ciki .
Yana sanya ƙafar sa a cikin gidan ya ji wani yanayi marar daɗi na lullubar sa , hakan kuwa yana da nasaba da rashin daɗin zama a gidan da yake ji har kullum ya kuma rasa dalili .
Taku ya fara yi da nufin isa sashin gimbiyar ta shi maimouna .
Sai dai ƴan hannuwan da ya ji sun riƙe masa ƙafafun sa su suka sanya shi ya maida ganin sa ƙasa ,!
Yumna
Ya furta yana ƴar dariya tare da kai hannu ya ɗauki ƴar yarinyar da take ta yi masa dariya , ya ɗaga ta sama ya cilla ta tana ɓangala masa dariya .
Rungume ta yayi a jikin sa lokacin da yake maida duban sa kan mamar ta wacce take ƙarasowa wajen fuskar ta ɗauke da murmushi , a shirye take tsaf , ba wata shahararriyar kwalliyar fuska tayi ba illa jikin ta da yake kiruf a rufe da babban mayafi tun daga wuyan ta da ya sha ado da tufafi irin na alfarma ,wanda ya amshi zubi da tsarin jikin ta na samɓaleliyar mace me zubin matan fulanin usul .
Janye idanun ta tayi daga cikin nasa kamar koyaushe da bata iya jurar ganin cikin idanun sa duk kuwa da tsawon shekarun da suka shafe a matsayin ma'aurata ,
Barka da zouwa Baban Yumna , da fatan ka isso lafiya ?
Lafiya mun same ku lafiya ? Yaya Yumna ?
Ga ta tana lafiya ,
ÆŠan shiru suka yi kafin ya katse shirun da tambayar ta
Ina kuke da noufin zouwa da hantsi hakka ??
A É—an ruÉ—e tace , zamu shiga fada gaishe da hajiya umma ,
Baza ku fita yanzou ba umma na tare da jama'a da wannan lokacin bani son idanun jama'a bisa ga kan É—iya ta , ko dai ki bar ta ki tahi ke É—ai , ko kuwa ki bari da sanyin la'asar kun tahi tare .
Ko kusa baza ta so ƴar ta ta gifta ta kurkusa da shigifar gimbiya moumuna ba bare har ta taka ƙafafun ta cikin wani al'amari da ya gifta a tsakanin su me girma , wanda ya tarwatsa takaitatcen zaman daɗin da suka fara gudanarwa a tsakanin su , daga nan aka yi walƙiya kowa ya shaida kowa , yayin da daga lokacin ta fara bin irin takun gimbiya moumuna da nazari , nan ta fahimci dayawa daga cikin boƴaƴƴun fuskokin ta masu cike da abubuwan al'ajabi tare da sarƙaƙiya da baki yayi kaɗan wajen furta su ga wani har sai idan wannnan mutumin ya ga kome a idanun sa .
Hakan ya sa ta rufe kome ta haÉ—iye a cikin ta , ta kuma killace kan ta da É—iyar ta daga gimbiya moumuna da Æ´an barandar ta doumin ita É—in ai gubba ce ga rayukan alhalin masarautar maraÉ—i !
Da sauri ta miƙa hannu tana ƙoƙarin amsar ƴar ta daga gare shi
Mun hakure zouwa yammaci kamar yadda ka faÉ—i mouna Biyamuradi .
Janye yumna yayi ya hana ta ɗaukar ta , a hankali ya kamo hannun tare da sarƙafe ƴan yatsun sa a cikin nata hannun yana jin yadda taushin hannun ke tado masa da yanayin da yake ta dannewa tsawon satika , " muryar sa tafe da amo marar ƙarfi yace
Mu tai ki ciyar da ni abounci na taho tare da yunwa me tsanani .
Ƙoƙarin zare hannun ta take tana satar kallon sashin gimbiya maimouna ,
Cikin sa'a idanun ta ya sauƙa akan gnala shugabar bayin sashin gimbiya moumuna ta na abunda yake goge gilashin falon gimbiyar ta ciki a zahiri , wanda tashin farko siyama ta fassara abunda take da ɗaukar rahoto
Toh Biyamuradi , amm...
Shitt
yace mata lokacin da yake jan hannun ta zouwa sashin sa kai tsaye da yumna saɓe kan kafaɗar sa ta dama tana ƙoƙarin ɗauke hular kan sa ,
Suka fara taku tare da masaniyar yau wajen ta ya kamata ya kwana a tsarin ƙwanakin girki .
Gimbiya moumuna wacce tun isar sa fada ta samou labarin zuwan sa , inda bata yi ƙasa a guiwa ba ta tashi shirin tarɓar sa ,
Ta tashi hankulan bayun ta da aikin gyara gida wasu kuma na haÉ—a mata ruwan wanka tare da fidda mata kayan da zata sanya a jikin ta ,
Zuwa shigowar sa gidan ta fito daga wanka ta fara shiri , yana dosar gidan saƙo ya iso mata , hakan ya sa ta miƙe daga gaban mudubi ta ƙarasa gaban babban window na ɗakin ta dake sama ta raba labulen biyu daga inda take ta hangi kome da ya wakana tsakanin sa da siyama .
Wani irin tuƙuƙi take ji yana taso mata daga cikin rai har tana jin ɗacin sa a maƙogoro .
Meyasa ne wankin hula ya kai ta É—are har tsakiyar sa ?? Lamarin da suka yi hasashen yiwuwar sa a watanni zuwa
Shekara bayan zuwan ta masarautar maraɗi , sai ga shi shekaru har sun fara ƙoƙarin haurawa kirgen yatsu biyar ?? Wacce iriyar mummunar rashin sa'a ne gare su haka ?? Wanne sirri ne da yake boye cikin duhu da ya zamto shamaƙin da ya shiga tsakanin ta da cikar burin ta ?? Menene shi da ya wuce tasirin ƙarfin su ??
Tattare labulen tayi ta cukuikuye shi a tafin hannun ta tana jin kamar tayi girgiza ta fasa bango ta dira a sashin yarima youssouf ta kaddamar da manufar ta ..
Ranki ya daÉ—e kÆ´akya.....
Bata bari gnala ta ƙarasa kalmomin ta ba wacce ta shigo ta durƙusa daga bayan ta ,
Da hannu ta dakatar da ita ,
Ayi gaugawar shiryawa Biyamuradi abincin sa a aika da shi shiyar sa .,
Ke zaki miƙa abincin da kan ki daga nan kin kawo mi ni labari na lamarin da ya auku gaba gare ki .
Allah ya huci ran gimbiya Æ´ar sarkin nahiyar mu maigirma oumarnin ki shine abun bi .!
da shigar su sashin nasa da yake me matuƙar girma , da tsari tare da wadatar tsaftar da ta haifar da kyakkyawan yanayi a wajen ,
Ya zauna bisa ɗaya daga cikin kujerun falon nasa , yana sauƙe yumna kan kafafun sa ,
siyama wacce ta saɓule mayafin ta ta ajiye a gefe ta sunkuya tare da yin gurfano a gaban sa , cikin nutsuwa ta kai hannuwan ta tana kunce masa igiyar takalmin sa tare da zare masa shi a hankali ,
Ɗan kiɗan da wayar sa ta yi dake nuna alamun shigowar saƙo ya sa shi zaro wayar daga aljihun sa ,
  Lokacin da take ƙoƙarin karɓe hular sa dake hannun yumna ta ƙi bada hular ,
  Ki bar mata hular mana , kin ka sani ko ɗiya tayi gadon baban ta ?
  Da murmushi bisa fuskar ta ta wuce sama domin ajiye masa takalman sa , ta zo ta fara yi masa shirin girki .
  Saƙon gimbiya maimouna ne mai ɗauke da tsararrun kalamai na barka da zuwa ƙarshe take sanar da shi ta bada saƙo a kawo masa ,
 Fita yayi daga wajen adana saƙon yana shirin ajiye wayar hoton da ya ɗauke su ɗazu ya bayyana a fuskar wayar,
Ƴan yatsun sa ya sa ya jawo hoton ya cika wayar ya na nutsar da idanun sa kan fuskar ta me ɗan haske kaɗan da take ɗauke da wani sirri me tasirin da ya zarce a ƙira shi kyau ,