← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 179 OF 269

Sashe 179

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shima zagayawa yayi ya zauna daga É—aya sashin kusa da ita ,

Bayan direban ya gama shigo da kayan Youssouf ya yi masa iznin tafiya ,

Ƙarasa haɗe sararin tsakanin su yayi , tare da riƙo hannun ta da duk ya saki ,

"Fatima me zaki ci ? Hajja zata dafa miki , ina ga ma bata san mun dawo ba ,

"Mama ki je É—akin Hajja kice mun dawo ,

Duk da cewa ba ƙarfin jiki ta cika ba sai ta miƙe ,

"to Papa ,

"Baban Mama bari na ƙira ta da kai na,

Riƙo ta yayi ya ɗorata baki ɗaya akan jikinsa , yana jin yadda jikin nata ya ɗau ɗumi ,

"ki bari Mama ta ƙira ta zata iya , kar ki wahalshe min da kan ki , shafa saman idanun ta yayi da suka ɗan shiga ciki , kin zauna da yunwa Fatima meyasa ,

Ƙarasa narkewa tayi a jikin sa tana jin daɗin irin riƙon da ya yi mata ,

"Nagaji da irin abincin su ne ,

" To me zaki ci Hajja ta dafa miki yanzu  ?

  " Ƙuli-ƙuli mai sugar raina yake so ,

Ɗan zare ido yayi sai kuma ya saki sassauƙar dariyar da har ta isa ga kunnuwan Mama wacce take ta faman tura ƙofar ɗakin Hajja ta gagara buɗewa ,

Ita ma dariya ta sanya jin sautin dariyar Babanta , tana sake tura ƙofar ta ga an buɗo , a hankali ta ɗaga kai tana kallon farar matar da take tsaye a gaban ta da bata kai ga taɓa ganin fuskar ta ba ,

Yakaka wacce fitowar ta kenan daga wanka ta ji ana taɓa ƙofar ta zo da saurin ta ta buɗe ga zaton ta Hajja ce wacce ta tafi kasuwa sayo kayan miya tun da ta idar da Salla ,

Fuskar da ta ci karo da ita a zahiri ta sa zuciyar ta sauya bugu , tamkar a mafarki ta gan ta a gaban ta duk kuwa da cewa tana da masaniyar dawowar su a tsakanin yau zuwa gobe a cewar Hajja ,.

Bata san lokacin da tayi durƙuso ba a gaban ta , ta miƙa hannuwanta biyu ta tallafe kumatun ta bayan ta dai-daita tsawon su ,

"Mama ,

Ta ƙira sunan ta da wani irin sauti ciki-ciki ,

rungumeta take nufin yi sai taji yarinyar ta janye jikinta a hankali ta yi baya-baya ,

Kafin ta juya da ɗan gudun ta tana ƙiran

"Papa , Mama , watta ce cikin É—akin Hajja ,

Da sauri ta yunƙura ta bi bayanta saboda ji da tayi gaba ɗaya zuciyar ta ta afu ga 'yar ta , wani irin shauƙin so da ƙaunar 'yar ta ke kwaranyowa a zuciyar ta ,

Da taka kafafunta a falon Falmata ta ɗago kan ta , daga ƙirjin Youssouf , tare da chanjin bugun zuciyar ta , a take ta bijiro mata a cikin rai Yakaka, ta ambata a zuci ,

Tare suka ƙaraso da Mama da ta tafi da gudu ta hau kan jikin Babanta da Falmata ta ɗaga ,

Turus tayi , idanunta ya sauƙa akan su  , da wani irin yanayi ta dubi ƙwarar idanun Youssouf da suke cikin nata da yanayin firgici ɓaro-ɓaro a cikin su ,

Cikin daƙiƙa kaɗan ta janye idanunta daga kansa ta mayar su ga Falmata , wacce take ware idanun ta da suke hango mata dusu-dusun farar mace sol a tsaye , wacece wannan ? Hajja kenan ?

Girman da Falmata ta yi tare da gogewar da tayi basu jirkita mata kamannin 'yar ƙanwar ta ba , so take ta taka taje ta rungumeta , sai dai wanda ta hango ta jingine da jikin sa ya mata tarnaƙi .

Bata motsa ba daga inda ta ci birki , illa Muryar ta da ya ratso shirun da wajen ya ɗauka ta ƙira sunan ta

"Falmata na ,

Muryar ta ta sauƙa da ƙaƙƙarfan sautin da ya wuce yadda ita ta yi maganar a kunnuwan Falmata ,

Waigawa tayi sashin da Youssouf yake a daskare , muryarta na rawa tace

' Baban Mama muryar Yayata nake ji ta ƙirani , Muryar Maman Mama , Muryar Yakaka na , yan yién .

Yakaka wacce Hawaye ya fara sauƙa daga gurbin idanun ta tace ,

"Falmata umaa yammana3 , umaa bangie3 , are3 nayie3 Falmata , Falmata are3 nayie3 , are3 Falmata kiramie nyie .

Sai ta miƙe a hankali daga gefen sa tana jin wani ƙaƙƙarfan yanayi na kusancin su na ingizata yana cire mata duk wani tsoro da shakku daga ran ta , Yakaka ai wata sashi ce na daga tsokar jikinta

babu shakka wannan Yakaka ce tsaye a gabanta , wannan farar inuwar da take gani ba kowa bace illa Yakakar ta  , 'Yar uwar ta , Ashe Yakakar ta na raye , ashe bata mutu ba ? ???

Yakaka bata jira ta ƙaraso inda take ba ta tafi ta rungumeta , zuwa lokacin su dukkanin su biyu kuka suke da sauti ,

Kukan da kowaccen su ta jima tana neman 'yar uwa da zata taya ta yin sa , kukan kewar junan su , kukan tausayi da ƙaunar junan su , kukan tunowa da farkon fari , mafarin faruwar walagigin su ,

Mama wacce tayi lamo a jikin Baban ta É—ago kan ta tana kallon fuskar sa ,

"Papa qui est cette femme étreignant ma mère? qu'est-ce qui les fait pleurer? ( Papa wacece wannan matar da ta rungume Mamana?  Meyasa suke kuka ? )

Tamkar wanda ya farka daga bacci haka ya firgita da tambayoyin Mama , kallon ta yayi kafin ya mayar da ganin sa kan su da suka ƙarasa zama a ƙasa har yanzu suna kuma rungume da junan su tamkar idan ɗaya ta bar ɗaya ɗayar zata gudu ko ta ɓace .

Motsa laɓɓan sa yayi da nufin yin magana sai dai ko kalma guda ta gaza fiddo da kan ta , wani irin zullumi mai tafe da tsananin firgici ke samun matsugunni a ƙarƙashin ran sa ,

"Yakaka bata mutu ba ta dawo ??

Wani  irin sarawa kansa ya yi lokaci guda , take gumi ya shiga tsattsafo masa tunanin makomar auren sa da Falmata yana kassara masa duk wani guntun ƙarfin sa .

Assalam Alaikum masu karatu ,

Da fatan duk kuna lafiya ?

Ina miƙa sakon gaisuwata a gareku da fatan alheri a duk inda kuka yi bigire .

za ku ce ya ta rage hannu ?? 😜😂 

Ban san ko kun fahimci MHR ya fara naɗe kayan sa ba ?  Me zai hana kafin lokaci ya gwada mana ƙarshen MHR dukkanin masoyan MHR na fili da na ɓoye su yunƙuro , kuyi ɗango ku gwada min ƙaunar ku ga MHR ta hanyar bayyana ra'ayoyin ku tare da danna ɗan tauraron nan , da ni kuma na gwada muku irin tawa bajintar ta hanyar ƙure muku ......................ɗan..ɗan...ɗanliti😂🏇 ƙur-ƙet , ah to meye ? Ya wuce na dunga yin update kullum har a gama ?? Ƙurunƙus 🙅🤓

Nagode.
[11/23, 7:08 PM] +234 706 503 6187: MAFARI

( Hargitsin Rayuwa )

Umm'muaz

41

Shigowar Hajja ita ta tsagaita kukan Yakaka da Falmata,

Da girmama juna suka gaisa ita da Biyamuradi Youssouf wanda ya samu da kyar ya iya harhaɗa kalmomin amsa gaisuwar Hajja , saboda jin sa da yake gaba ɗaya a birkice a gigice, tamkar babban mai laifin da yake jiran hukunci daga Alƙali , da yana da dama da tuntuni ya ɓace ɓat .

Hajja ta mayar da ganin ta gare su sai tayi saƙare tana bin su da kallon Al'ajabin yadda suka ƙaƙwume juna suna shiƙar kuka ,

" ku kuma yaran nan lafiya kuke kuwa ?  Uwarɗakina Falmata ya daga zuwa sai kuka ? Ai ke yanzu kukan ki ya ƙare , farin-ciki ya kamata ki ta tayi  'yar nan , bari kuka Falmata .

Falmata ta É—ago kan ta daga jikin Yakaka idanun ta da hawaye amma tana É—an murmushi tace ,

" Hajja ke ce wannan ?

Bata jira ta amsa mata ba ta É—ora da cigabada cewa ,

"Dole nayi kuka Hajja , wannan da take gabana yanzu ita ce Yayata da nake baki labarin ta Yakaka Mamar Mama , ta dawo ashe bata mutu ba , kukan murna nake Hajja , duk duniya a yanzu bani da wanda ya wuce ta .

Hajja ta ɗan taɓe baki , tana satar kallon Youssouf da yake wuƙi-wuƙi da ido yana shafa kan Mama da take jikin sa tana bin Yakaka da kallo ,

" aifa na ganta , labari kuma ya iske mini tun muna can , ai tare muka zo , ina gida lokacin da ta dawo daga inda tayi mafakarta tsawon shekaru ,

" Uwarɗakina lafiya ta samu ko ? , wallahi nayi murna , nayi murna Allah dai ya sakawa Babban soja da dubun Alheri , samun mijin da ya wuce shi a wannan zamanin akwai wuya , ki kama mijin ki ki riƙe ƙam-ƙam , Allah ya barku tare ya baku zuri'a masu yawa da Albarka ,

Shiru falon ya ɗauka aka rasa mai ƙarfin guiwar Amsawa ,

Ga Yakaka mummunar addu'a ta danganta addu'ar Hajja da ita dan haka tace " ba amin ba, cikin ranta tabbas ta san da Hajja take wannan kankanbar bata san wanene Youssouf bane , 

A sanyaye Youssouf ya miƙe riƙe da hannun Mama da taƙi barin jikin sa , so yake ya kaucewa sake haɗa ido da Yakaka , yana buƙatar wani ɗan saƙo da zai shiga ya rakaɓe ya haɗa kai da bango ya yi kuka ko zai ji sauƙin tashin hankalin da yake ciki , fili da baɗini bai ji daɗin dawowarta ba , bai ji daɗin bayynuwar ta ba , ya so da ta cigaba da zama a matatciyar ta tulin addu'o'in sa na riskar ta ,

Taku ɗaya yayi yana ajiye na biyu , yaji sun ƙira sunan sa a kusan tare ,

"Baban Mama ,
"Yusuf ,

Hatta hantar cikin sa sai da ta kaɗa , da jin tashin muryar ta da kaushi a ƙiran sunan sa ,
Chapter 179 · 0% Book details