Sashe 199
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a tsawace ta katse ta ,
  " ki tashi ki tai ga shiyar matar can ki ce ina biɗar ganawa da Major Youssouf Abdoul-azuzou Youssouf Baskore .
 A ɗan firgice Gnala ta ɗago kan ta tana duban uwargijiyar ta , jin yadda yau ta ƙira sunan Yarima garan-gatsau babu wani sakayawa bare girmamawa , sai dai yadda ta ga fuskarta ta tsorata ainun , dan haka ta miƙe jiki na rawa ,ta fice tana cewa ,
 " Allah shi huci ranki Gimbiya ɗiyar Sarki .
sanin da tayi bata da ikon shiga sashin Siyama kai tsaye , sai da kamun ƙafar Rakiya shugabar hadiman sashin da ita ce zata yi mata jagora , yasa ta ratsa dogayen bishiyoyi da shuke-shuken farfajiyar gidan ta cimma Rakiya a shiyar ƴan aiki ,
 Da kallon banza suke bin junan su , tamkar kishiyoyin da suke zama bala'i, kamar Mai ciwon haƙori Gnala ta buɗe baki da kyar tace ,
  " saƙo dagga Gimbiya tace a shaidawa Matar Yarima , gimbiya na biɗar kaɗaicewa da shi .
 Rakiya wacce take cin gyaɗa ƴar marau-marau , ta karkaɗa ƙafa bayan ta afa gƴaɗar ta a baki , ba tare da ta dube ta ba tace ,
  " kin ga Gnala ki ɗaga sauti kiyi magana yadda zan iya ji amma kin zo kin tsaya akaina kina wani mui-mui da baki ,yo ce miki aka yi aka yi kunnen nawa zuƙo sauti yake ? Aikin banza .
 Gnala ta ƙuta , cike da takaicin rashin mutuncin Rakiya.
da ƙaƙƙarfan sauti ta ɗaga murya cikin faɗa-faɗa tana maimaitawa mata saƙon Uwargiyar ta ,
  " ah ke saurara haka kar ki fasan dodon kunne ki fallasheni , kin zo kina min hargagi akai ya ruɓaɓɓan radi'o ,
  " Naji , sai ki wuce mu tafi , tace tana miƙewa ta zira takalman ta ,
 Da wani mummunan kallo Gnala ta bita kafin ta dafa mata baya , suna tafe Rakiya na rera waƙar Barmani mai coge "cikin waƙar ɗuwawai ," inda take cewa ,
   A hayayye ɗuwaiwai dole a zauna da ku , to ko ana so , to ko ba' a ƙauna ,ko da sun tsiyaye , wayyo ladi ko a tsidau , kai koma cikin kwata ne .
Daga bakin ƙofa ta nemi iznin shiga wajen Uwargijiyar ta ta hanya matsa mata ƙararrawar dake shaida isowar ta ,
Siyama wacce ta zuba abinci da zummar fara ciyar da Youssouf sai ta miƙe bayan ta ɗau izni daga wajen sa , fahimta da tayi wani saƙo muhimmi Rakiya take tafe da shi a dai-dai wannan lokacin .
Da buɗe ƙofar ta ci karo da Gnala wacce take tsugunne a gaban ta , ba ɓata lokaci ta isar da saƙon Uwargiyar ta .
 Murmushi Siyama tayi cikin ran ta tana aiyana " ai shi daman wanzami bai son jarfa ,
 Da baya ta dawo tana sanar da Youssouf saƙon Uwargidan sa , jim yayi ," shi ba da gangan yaƙi zuwa wajen nata ba , rigimar ta yake gudu , baya son ta ƙara masa damuwa akan wacce yake ciki ,
 Miƙewa yayi tare da yin baya da kujerar dake gaban teburin , tunda har ta sauƙe girman kan ta na ɗiya mace ta ƙira shi , duk kuwa da laifin sa , shi ya zama dole ya tafi gareta ,yayi aikin rarrashi da neman Afuwar ta tunda zuwa yanzu ai yana da ɗan ƙarfin jikin ɗaukar duk wani bore da zata iya yi masa ,
 Sai da ya kai tsakiyar falon ya waigo ga Siyama wacce take tsaye jikinta a sanyaye tana bin sa da kallo , dawowa baya yayi , a hankali ya rungume ta , tsawon wasu daƙiƙai , ya sake ta tare da sumbatar leɓɓan ta a tsanake ,
  Daf da fuskar ta , ya kawo tashi fuskar cikin muryar da take tsakanin maƙoshin sa yace ,
  " Nagode da kome Ƙamnata , je t'aime pour ça, tu es spécial pour moi seulement ,
 Ya saketa a hankali ya juya yana barin falon ,
  Tsaye tayi a gurin tana shaƙar ƙamshin sa da yayi saura a gurin , ta lumshe ido tana murmushi kaɗan cikin ran ta farin-ciki ne fal ,
   " Da gaske yake da yace yana son ta ? Ita ɗin kuma ta musamman ce a wajen sa ? Ko dai duk farin-cikin kusantar dawowar masoyiyar sa ne ?
****
Bayan shigar sa falon Gimbiya Maimounatu wanda yake da rangwamen haske sakamakon ƙasa da aka yi da hasken fitulun falon sosai a tsaye ya hango ta ta juyawa ƙofar baya ,
A hankali ya taka ya isa inda take tsaye , hannunsa ya sanya ya kewaye cikin ta tare da haɗa bayanta da ƙirjin sa sosai ,
Da sigar rarrashi yace ,
   " Bana cikin Farin-ciki da ganin ɓacin ran ki princesse, ina bakin-cik...
Da wani sauti daban da wanda ta saba yi masa magana da shi ta katse shi ,
    " ya ya kake son samun farin-ciki lokacin da ka kwashi tsawon wasu shekaru kana assasa baƙin-ciki a zuciyar wasu mutanen ?
"Â ka baranta da farin-ciki ba zaka yi farin-ciki ba har abada kai ma .
  Da ƙarfi ya juyo da ita yana laluben ganin fuskar ta , sai dai hasken wajen ya masa ƙaranci .
   " kiyi haƙuri Maimounatu ni ɗin mai laifi ne a wajen ki na sani ,
Wani ɗan ƙaramin murmushi mai sauti tayi ,
  " haƙuri , laifi ?
  Ta ce da sigar tambaya ,
Dariya tayi mai sauti , dai-dai da shigowar ƙira a wayar sa ta cigaba da cewa ,
  " Ai ni baka min laifin kome ba kan abunda ka aikata ma rayuwar ka ? To ma menene dan ka rage dare da yaya ka kuma zo ka amri ƙamna ? Ai babu wani laifi ga hakan ni dai ta ɓangarena , dan haka kada ka bani haƙuri bisa wannan ba damuwa ta ce ba .
 Jiki a sanyaye Youssouf yake bin ta da kallo , sai yake ganin baki ɗaya ta sauya masa ,
   Hasken wayarsa ya kunna tare da cewa ,
  " Maimounatu meye ya samu fitilun sashin nan ne ? Hala sun mutu ? Bari za'a sauya wasu ,
  " fitilin sashin nan na taya Uwargijiyar su baƙin-ciki ne kamar yadda zuciyata tun-tuni ta kasance a cikin duhun da yake matsananci fiye da wannan , tun a wata ɓakar-rana cikin ranaku da ka sanya bakin bindigar ka ka tarwatsa min fitilar zuciya ta ,
  Wayar sa ya mayar aljihu bayan ya ssnyata a silent , da alama sai yayi da gaske da alama ran Gimbiyar ta shi ya kai ƙololuwa a wajen ɓaci , jin yadda take amfani da wasu kalmomin da ya gaza fahimtar su ,
Jawo ta yayi ya zauna tare da ita tana bisa cinyar sa ,
   " Duk ki bar waɗannan kalaman Maimounatu , Fatima-zahra ƙaramar yarinya ce , ba zata ƙi ku zauna lafiya ba sann....
  katse shi tayi ta hanyar ɗora yatsanta manuni akan laɓɓan sa ,
   "shitt , Yarima Youssouf nace kada ka damu ,
  Miƙa hannu tayi ta ɗauko tatatcen ruwan 'ya'yan itatuwa da ta sarrafa da hannun ta , ta nufi bakin sa da kofin ,
  Jimm yayi yana kallon sheƙin idanunta ta ɗan hasken wajen , dariya tayi yana iya ganin hasken haƙoranta kafin tace da shi
  " Sha mana Yarima , abun shan ka ne mafi soyuwa , ni da hannuna nayi sa musamman domin kai .
  Ƴar ajiyar zuciya yayi jin alamun ta fara sauƙowa , hannun sa ya ɗora akan nata ya kai kofin zuwa bakin sa , yayi Bismillah ya kafa kai ,
  Ya sha sosai saboda ƙishirwar tare da yunwar da ya yini yana ji , ya kuma gagara cin kome sai fa yanzu da ya fara samun nutsuwar zuciya ,
  Wata irin damƙa da cikin sa yayi masa kamar kiftawa ido bayan gama sha , shiyasa ya zame Gimbiya maimounatu daga jikinsa ,
 Da sauri ya fidda wayar sa daga Aljihu da har lokacin ƙiran Tafeeda bai bar shigowa ba , da hasken shigowar ƙiran ya kai hannu ya ɗau kofin yana haska ciki .
Da wata irin muryar yace ,
  "Maimounatou menene cikin wannan juives din ? Meye a ciki ? Meye.. Kasa ƙarasa magana yayi
  Gumi ya shiga karyo masa saboda wani irin ciwo mai tsanani da ya ji ya turnuƙe shi tamkar ana filla-filla da kayan cikin sa , zamewa yayi daga kan kujerar bayan ya saki kofin hannunsa zuwa ƙasa ,
 Cikin azaba ya ke duban Fuskar ta , yana iya hango wani É—an guntun murmushin cikar buri da take yi , bata yi motsi ko kaÉ—an ba wajen ba shi wani taimakoÂ
  Wani irin gurnanin nishi ya fara yi , ya miƙe a ƙasa yana murƙususu ,ciwon da yake ji bai taɓa jin makamancin sa ba , wani irin duhu mai tsanani yake ji yana sabko masa daga can wani waje mai nisa a kwakwalwarsa Alhalin kunnuwan sa sun samu ƙarin ƙarfin ji ,
  Domin yana iya jiyo sautin murmushin laɓɓan Maimounatou , so yake ya buɗe baki yayi ko da addu'a ne amma ya gaza ,
Wani ciwo mai kaifi da ya yanki uwar hanjin sa shi yasa shi burtso da Amai ta hanci da bakin sa , da yasa duhun da yake sabko masa hanzarin ƙarasa saukowa ya rufe masa ido ya daina ganin kome alhalin idanun sa na buɗe da hakan ya yi dai-dai da tsayuwar jijiyoyin jikinsa , kome kuma ya tsaya masa chak .