← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 269

Sashe 132

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A fahimtar ta youssouf yana da wata mace wacce yake tsanananin so da a kowanne lokaci zata iya cuso kan ta cikin rayuwar sa ta mallake shi wanda hakan yake babbar barazana ga rayuwar auren sa da yarinya falmata miskiniya ,

   Hodijan !

Kai tsaye É—akin da falmata ta shiga nan ta tasamma ,

  A zaune ta tarar da falmatan daga ƙasa a bakin ƙofar ɗakin ta takure ,

Kallon ta tayi ta ji tausayin ta ya tsirga mata , hakkun ta fara hango ƙalubale a rayuwar auren yarinyar da ko fahimtar kalmar auren ma ba ta kai ga yi ba ,

  mutuniyar kina zaune anan ne ??

da sauri falmata ta É—ago kan ta ,
  Hajja ya tafi ??  Mama tana hannun ki ?
   Eh ya tafi ga kuma mama a baya na , taso nan muyi wata magana kin ji ƙawalliye roman jaɓa !

******
Abuja Nigeria

Yakaka ta dage da neman ilmi tun ana koya mata haruffa ,A ,B,C,D , da kuma ا ب ،ت ،ث، sannu sannu ta haddace su tare da iya rubutun su , aka fara haɗa mata jimla , tana koyan rubutun su tare da sanin ma'anar su ,

ba ƙaramin daɗin koyar da yakaka malama maryam take ji ba saboda wankakkiyar ƙwaƙwalwa me saurin ɗauke abu da yakaka take da ita ,

A hankali ta fara lura da ƙarancin wayon da yake ga yakaka tare da gidadanci , sai tayi ƙoƙari tana gyara mata duk lokacin da ta ga tayi wani abunda bai kamata ba , tare da yawaita yi mata ƴan nasihu akan duk wasu manya da ƙananun zunubai .

Gefe guda lubna na ƙara zage damtse ita a dole sai yakaka ta iya English da arabic ta iya magana da yarukan kamar yadda ta iya , dan haka sai ta tsiri yiwa yakaka magana da English ko Arabic ta daina yawan yi mata magana da hausa koyaushe ,

ga bangaren yakaka ita ma ƙwarai ƙwarai take jin daɗin haɗuwar ta da malama maryam da ƴaƴan ta , domin sun ja ta a jiki suna kuma gwada mata ƙauna hatta mahaifin su da ba sosai ma suke haɗuwa ba , amma duk lokacin da suka haɗu yana amsa gaisuwar ta faram-faram babu nuna tsangwama ,

Dan haka gidan su nan ne wajen yinin ta idan babu makaranta , ranakun makarantar ma daga ta baro makarantar gida zata tayi sallah ta ci abinci ta sauya uniform ɗin ta , ta dawo gidan ta kama musu ƴan aikace aikace kafin malama maryam tayi sallah ta ɗan huta , zaman ta da samy baby sai ya ƙaranta ,

Ranar wata litinin an tashi da hazo sosai tare da sanyi mai tsanani tun safe , zuwa yamma sai hazon ya ƙaru sararin samaniya yayi jawur iska me ƙura tare da tsananin sanyi yana kaɗa jikin al'umma , kusan kowa sauri-sauri yake ya gama abunda yake a titi ya koma gida

Bayan tashin su yakaka a makaranta tare suka dawo da malama maryam ita ta wuce gida da zummar yin sallar la'asar ta ci abinci ta sauya kaya ta koma gidan malama maryam wacce ta sake jaddada mata kan lalle fa ta zo su yi darasi kar ganin yanayin garin ya sa ta ƙi zuwa , cikin ladabi ta amsa da
   To zan zo Anty !

Da sallama ta tura ƙofar falon samy baby tare da danna kan ta kai tsaye , abunda ta gani ya sa jakar hannun ta saɓulewa zuwa ƙasa ,
   Ɗaya daga cikin ƙawayen samy baby ne tare da saurayin ta suke yin masha'ar su nan kan kujerar falon babu kunyar ubangiji ko shakkar za'a iya shigowa agan su haka ,

Da sauri yakaka ta kawar da ganin ta daga kan su , tare da sunkuyawa ta É—au jakar ta da sauri ta wuce É—aki ba tare da ta sake kallon su ba tana jin yadda jikin ta baki É—aya ya É—au rawa da tasowar sabon yanayin da take ji cikin illahirin wata jijiyar jikin ta ,"

A kasalance ta gama kome hatta cin abincin ta da samy baby take ajiye mata shi a É—akin ta,

ta shiryo ta fito falon da fatan son sake ganin su , saboda ganin su na ɗazu da ya tayar mata da wani yanayi cikin jikin ta tare da bijiro mata da guguwar begen yarima da ta ɗan kwanta sakamakon mayar da hankalin ta da tayi kan karatu ,

sai dai ganin da ta yiwa waɗanan fasiƙan ya sa ta fara tuno da wasu abubuwa masu kamanceceniya da wanda ta ga suna aikatawa , da abunda ya shiga tsakanin ta da bature kam silum ,

ba ta tarar da su a falon ba , dan haka ta sanya ƙafafu ta bar gidan , tana tafe tana jin ƙewar bature kam silum na sake lulluɓar ta , ko yana ina yanzu ? Wataƙila ma ya manta da ita ! , ruwan hawaye ta ji suna taruwa a idanun ta ,daidai lokacin da take tura babbar ƙofar gidan su malama maryam ta shiga ,

   karaf suka ci karo da lubna wacce take ƙoƙarin fitowa daga gidan hannun ta riƙe da wata leda ,

Yauwa ƙawata Dan Allah zo ki raka ni wancan gidan ummi ta aike ni ,
   Tana mata nuni da wani babban gidan da yake chan kusa da ƙarshen layin su ,
   Ba musu ta bi bayan ta , lokacin da lubnan take jan hannun ta ,

   Saƙo lubna ta kaiwa matar gidan tana bata saƙon suka mata sallama suka yi fitowar su ,

Sun zo dai-dai tsakiyar harabar babban gidan , yakaka ta ga wani É—an dogon saurayi É—an gayu ya sha gaban lubna fuskar sa a marairaice idanun sa fes akan ta ,

   Lubna Haba dan Allah ki saurareni , yau wajen watanni bakwai kenan ina bin ki da soyayya ta amma kina min walakanci , dan Allah ki TAIMAKA MIN ki yadda da soyayya ta wallahi ina tsananin son ki ,

   Ba tare da lubna ta ɗaga ido ta dube shi ba ta kewaye shi ta wuce tana sake jan hannun yakaka ,

Charaf ! Ya riƙo hannun ta Lubna Dan Allah ki taimak....

  Wani irin ƙara lubna ta sa kamar ya jona mata wuta , ta warce hannun ta da matuƙar ƙarfi cikin abinda bai wuci daƙiƙai ba ta cire hannun ta ta wanke shi da mari , kafin cikin muryar ta da take karkarwar kuka ta tace
    Kar ka kuskura ka sake taɓa ni , ni ba ƴar iska karuwa ba ce ,

   Kukan da ya zo mata ya sa ta kasa ƙarass zancen ta da gudun gaske ta juya tana barin gidan ,
   Yakaka wacce take sakakai a tsaye ta bi shi da kallon tausayi a hankali ta furta kalmar
    Kayi hakuri
  Gƴaɗa mata kai yayi
Cikin sanyin jiki ta juya ta bar shi a wajen ta nufi gida ,

Tana shiga cikin gidan ta tarar da lubna rungume jikin mamar ta banda kuka babu abunda take , malama maryam sai tambayar ta take me ya same ta ? Me aka mata ? Ta gaza bata amsa ,

  Kallo mai bayyana haushi yakaka tayi mata lokacin da take zama a gefen malama maryam ,

Anty wai fa dan kawai wani mutum ya kama hannun ta yace ta taimaka masa yana son ta shine ta mare shi ta gudo gida tana wannan kukan ,
   Ta ƙarasa zancen muryar ta na nuna jin haushin abunda lubna tayi ,

    Waye ya kama hannun ta ? Wanne mutum ne , ke lubna ɗago ki dube ni waye ne ya riƙe miki hannu meye tsakanin ku da shi ? Ki faɗa min gaskiya ,
   cikin shisshiƙar kuka lubna tace ummi , Mukhtar ne ɗan gidan Alhaji Umar , shine tun watannin baya yake tare ni yana cewa wai yana so na , shine yau ya tare ni a gidan su har ya riƙe min hannu wai na taimake shi yana so na ,

    Nan take fushi mai tsanani ya bayyana a fuskar malama maryam , ta shiga yin faɗa meyasa tun ranar farko lubna bata sanar mata ba ? Ita kuma ta faɗawa baban su lubnar ya sami mahaifin yaron anyi musu tsakani ba ,
    Faɗa take yiwa lubna tamkar zata doke ta , a karshe ta gargaɗe kan ko kusa ta da shi bata yadda ta sake tsayawa ba kuma zata faɗawa baban su ya sanar da mahaifin yaron su ja kunnen ɗan su , ya fitar harkar ƴar su ,

  Sororo ! Yakaka tayi cikin jin mamakin malama maryam menene abun tashin hankali haka ?
  Da son kwantar mata da hankali tace ,

   Anty ai hannun ta fa kawai ya riƙe , kuma fa cewa yayi ta taimaka masa ,

wani irin kallo malama maryam tayi mata ,

   Yakaka ,

Namiji baligi ya kama hannun mace baliga haramun ne a musulunci , muddin ba muharamman juna suke ba domin tafarki ne na samar da ZINA a tsakanin mace da namiji  ,

Zina kuma haramun ce a musulunci, kuma tana daga cikin manyan laifuka wanda ake kira Kaba'ir.
Allah ya fada cikin Qur'ani
و لا تقرب الزنى
Wato kada a kusanci zina.
Hikimar fadin hakan shine ba aikata zina kadai ba, aikata abunda zai janyo zinar irinsu rungumar juna , taɓe-taɓen juna da shafe-shafen jikin juna tsakanin namiji da mace dukkansu Allah yayi hani domin hanya ce ta kusanta kai ga zina ,

cikin sanyin murya yakaka tace

Anty menene ZINA  ??

Zina ita ce Saduwa a tsakanin namiji da mace ,( ina nufin mace da namiji su kasance cikin abun rufuwa É—aya jikin su na cikin na juna , azzakarin namiji yana cikin farjin mace ) ba tare da hukuncin aure ya shiga tsakanin su ba , duk mace da namijin da suka yi tarayya irin haka ba tare da an É—aura musu aure kamar yadda addinin musulunci ya koyar ba to babu shakka sun aikata zina ,
Chapter 132 · 0% Book details