← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 269

Sashe 90

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana zuwa ta buɗe mata gidan baya da taimakon ta ta shiga , ta zagayo ta buɗe mazaunin direba ta shiga , tana jin yadda tata zuciyar ma take yin rauni da matsanancin tausayin rayukan da yake lulluɓe ta ,tana tuhumar kan ta Anya Anya kuwa ita SAMIRA ta kyauta ???

Da gudu ta bar hsrabar asibitin ta fito kan babban titi , ta miƙa hanya sosai ta nufi kwadaben barin gari , kasantuwar daman da shirin ta tsaf , sai kawai ta ɗaɗɗaga gilasai lokacin da ta hau kan babban titin da ya nausa ya nufi wajen gari , sashi na ran ta na ƙarfafar ta akan ƙudirin ta ,

a hankali yakaka ta sauke hijabin da ta ja ta rufe fuskar ta baki ɗaya da shi ta ɗaura jajayen idanun ta da suka rine suka kumbura hatta fuskar ta tasa ta saita ganin ta akan titi tana kallon manya bishiyoyi da ƙananun dazuzzukan da suke kusa da gari ,"

zuciyar ta na wani irin ƙuna , ƙuna mai tsanani , tana jin ta empty , tana jin ta kamar tana kan guguwa tana walagigi da ita tana jin tamkar ta rasa kome da kowa , tana jin tamkar tayi KUSKURE MAFI GIRMA A RAYUWAR TA .!

A hankali ta maida kan ta jikin tagar motar ta kwantar tare da runtse idanun ta , zuciyar ta na dawo mata da hoton Halin da ta bar FALMATA DA MAMA a ciki , kunnuwan ta na amsa kuwwar kukan JARIRIYAR TA ...

WAI
    Wai
       Wai

Assalamu Alaykum kowa da kowa , ina gaishe ku tare da fatan Alheri , nasan kun yi dogon jira na tsawon sati biyu cif yau ' da fatan zaku dunga min uzuri , domin da ace ɗaya daga cikin ku ya san tarin aiyukan dake jibge akai na wallahi da babu mai yin ƙorafin rashin ganin cigaba akai akai ,

duk da haka zan ji daɗi idan ku ka cigaba da min uziri , ɗan adam a koyaushe yana buƙatar ɗaga ƙafa tare da bada dama !!

  Nagode kwarai da yadda ku ke bibiyar rubutuna , tare da ku da taimakon ku rubutun har ya miƙa ya haka ,, ina fatan zaku cigaba da bibiya ta har mu cimma matsaya ,"

kofar shigar da ƙorafi ko gyara tare da ra'ayoyi a buɗe take a gare ku , kai tsaye zuwa gare ni , zan ji dadi kuma zan yi amfani da shawarwarin ku muddin bai saɓawa ainahin tubalin ginin labarin ba .

  Nagode !
  
      
   

   
     
[6/24, 10:59 AM] +234 701 013 7848: Mafari .....
( Hargitsin Rayuwa )

umm'muaz

27

Da sauri Doctor Hamza yake tafiya ," Amne na bin bayan sa , lokacin da suke kutsawa cikin asibitin , bayan sha da kyar da suka yi a cikin cinkoson ababen hawa da ya fara haÉ—uwa akan titi sakamakon kusantowar lokacin sallar juma'a ,"

Sai dai tun da ya dosa bakin É—akin haihuwar taron mutanen da ya gani kama daga likitocin asibitin zuwa kan nurses da securities ya sa shi rage takun sa ,"

  Maganganun da ya ji suna faɗa cikin harshen turanci tare da kama sunan AMINA DILMARI shi yasa shi zabura ya kutsa tsakanin su ,
    What's happening/ Me yake faruwa ?
yace da su cikin wata irin muryar ,

  Calm down sir , Babban likitan da asibitin yake mallakin sa yace yana kamo kafaɗun doctor Hamza ,
Muje office muyi magana ,"  zame kafaɗun sa doctor Hamza yayi lokacin da yake fuskantar likitan ,
   Ina patient ɗina ? Yace da buɗaɗɗiyar murya , "
   Shiru likitan yayi ,"
  Wani irin bugu zuciyar Hamza take kamar zata fito waje ," kasancewar sa cikakken likita yasan yanayin da suke yi a duk lokacin da suke son sanar da mutanen marar lafiya wani mummunan labari game da marar lafiyan su,!

   Ta mutu ?

Ya tambaya yana jin yadda zuciyar sa ke matsewa da tasowar É—acin kalmar har akan harshen sa ,"

Da sauri likitan yace
   Bata mutu ba amma zai fi kyau idan muka je nayi maka bayani a nutse.

  A sanyaye Doctor Hamza ya bi bayan likitan bayan ya nunawa Amne wurin zama a gefen Falmata wacce tayi zugui idanun ta sun yi jaa sakamakon hawayen da take ta gogewa kan rashin sani halin da ƴar uwar ta ke ciki har kawo wannan lokacin ,

Mun rasa gane yadda akayi ko dalilin da yasa matar ka tare da Æ´ar uwar ta suka bar asibiti kuma suka bar Æ´ar jaririyar ta ba tare da mun sallame ta ba , sannan Alamu suna nuna kai ma baka san sun tafi ba ,"
 
   Ɗan tsayirtawa likitan yayi yana nazarin fuskar doctor hamza wanda yayi saƙare yana kallon sa , kamar dai bai kai ga fahimtar bayanin da yake masa ba ," ɗan ƙwanƙwasa bakin biron hannun sa yayi akan ƴar takaddar gaban sa,"
     Idan har an tabbatar tana gidan zamu iya sallamar ku tare da jaririyar domin ayi gaggawar sadata da mahaifiyar ta domin ta shayar da ita nonon farko ,"

   Cikin jirkitattacen kallo Doctor hamza yace wacece ta gudu tare da ƴar uwar ta suka bar jaririyar ?

    Tamkar dai sam bai ma fahimci bayanin da duk likitan nan ya masa ba ,"
    Ba kai ne mijin AMINA HAMZA DILMARI BA ?
   Maimakon ya amsa sai ya miƙe tsaye ,
   Kana nufin ita ce suka gudu tare da ƴar uwar ta ?
   A taƙaice likitan yace
Haka muke zato domin an duba duk inda yakamata cikin asibitin nan ba'a gan su ba , sannan masu tsaro/securities sun tabbatar mana da sun ga fitar mata biyu farare sanye da hijabai sun hau.....
   Ankarar da yayi doctor hamza ya juya daga ofishin ya sanya shi miƙewa ya biyo shi ,
    Wurin da ya bar Amne da Falmata nan ya dawo ,"
  Fatimah , kun haɗu ke da yayar ki ?
Da sauri ta É—ago kan ta !
Bamu haÉ—u ba Yaya dakta har yanzu ba'a kai ni inda suke ba ita da baby , ko basu da Lafiya ne ? Dan Allah ka kai ni wajen su ,'!
   Wani gumi yaji yana tsatsafo masa daga illahirin ƙofofin gashin jikin sa ,"
  Amne ta taso ta matso kusa da shi ,"
Ina mai jegon ne ?
  wai ba'a gan ta ba yace da wata irin murya chan ƙasa , Amne dake kusa da shi kaɗai ta iya jin mai yace
  Wanne irin ba'a gan ta ba inji amne ,'
  Lokacin da likitan ke sake ƙarasowa tare da wasu nurses da wasu securites ,
      Kuyi haƙuri sir , a fara duba gida ko suna chan , domin tare da ƴar uwar ta suka fita ,"
   Wata kakkarfar tsawa doctor hamza ya yiwa likitan ,
   Ka daina cewa tare da ƴar uwar ta suka fita , "
   Ga ƴar uwar ta nan , ya juya yana nuno musu Falmata wacce ita ma ta miƙe tsaye tana rarraba ƙwayar idanun ta da son sanin meke faruwa?
  Ita kaɗai ce ƴar uwar ta , ya zama dole ku nemo ta  , ba gudu tayi ba sace ta aka yi , Yakaka baza ta gudu ta bar Fatimah ƙanwar ta ba baza ta gudu ta bar baby mama ba , noorie baza ta min haka ba , ya ƙarashe da rawar murya yana jin yadda zuciyar sa ke cika da tsoron tabbatuwar hasashen mutanen asibitin ,"

   Sir kayi haƙuri amma matar ka ba sace ta aka yi ba ita da ƙafafun ta suka fita tare da wacce tace sister nata ce , bayan tafiyar ka matar ta zo , tanan muka wuce da ita , wannan yarinyar da kace ita ce ƴar uwar ta tana zaune a wajen bata nuna ta san yarinyar ba basu mata magana ba su duka biyun , sai da muka je ɗakin , suka yi magana , kuma lokacin da nake fitowa da baby domin kai ta wurin mamar ta naga bayan wasu mata biyu suna fita , ina hasashen su ne , domin su ne kaɗai matan da aka ce an gani sun fita da hijabi tsukin awannin nan ," ka zo ma na nuna maka shaidar flask ɗin ruwan zafin da matar ta kawo , har yanzu yana ɗakin !,
   Cewar wannan nurse ɗin da ta kai yakaka ɗakin hutuwa ,"

Bai ce ƙala ba ya bita a baya zuwa ɗakin , anan ya tadda flask ɗin da ta ambata tare da wata ɓakar leda da sauri ya ɗauki ledar ya buɗe ,
   Babu kome a ciki sai hijabin yakakar wanda ta zo da shi asibitin ," hajabin da yayi wa farin sani domin shi da kan sa ya saya mata su guda biyar mabanbantan launika .

    Shiru ne ya ratsa ɗakin ,"

   Doctor hamza yayi shiru kan sa a sunkuye da alama ya zurfafa cikin tunanin me yake shirin faruwa ne ? Da gaske ta gudun ne ? To meyasa zata yi haka ?Anya tana cikin Hankalin ta ? Ko dai gida suka koma tare da RAHIMA ? Idan ba haka ba yaran wa suka sani ? Ina za ta ? Basu da kowa ƴan gudun hijira ne .

   Ina baby ??

  Da sauri babban likitan yace a je a zo da baby , yana fatan Allah ya sa wutar masifar da take son kunnuwa masa a asibiti kar ta kai ga ruruwa har ta ɓata masa sunan asibiti .
Chapter 90 · 0% Book details