Sashe 125
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lafiya mun same ku lafiya ? Yaya Yumna ?
Ga ta tana lafiya ,
ÆŠan shiru suka yi kafin ya katse shirun da tambayar ta
Ina kuke da noufin zouwa da hantsi hakka ??
A É—an ruÉ—e tace , zamu shiga fada gaishe da hajiya umma ,
Baza ku fita yanzou ba umma na tare da jama'a da wannan lokacin bani son idanun jama'a bisa ga kan É—iya ta , ko dai ki bar ta ki tahi ke É—ai , ko kuwa ki bari da sanyin la'asar kun tahi tare .
Ko kusa baza ta so ƴar ta ta gifta ta kurkusa da shigifar gimbiya moumuna ba bare har ta taka ƙafafun ta cikin wani al'amari da ya gifta a tsakanin su me girma , wanda ya tarwatsa takaitatcen zaman daɗin da suka fara gudanarwa a tsakanin su , daga nan aka yi walƙiya kowa ya shaida kowa , yayin da daga lokacin ta fara bin irin takun gimbiya moumuna da nazari , nan ta fahimci dayawa daga cikin boƴaƴƴun fuskokin ta masu cike da abubuwan al'ajabi tare da sarƙaƙiya da baki yayi kaɗan wajen furta su ga wani har sai idan wannnan mutumin ya ga kome a idanun sa .
Hakan ya sa ta rufe kome ta haÉ—iye a cikin ta , ta kuma killace kan ta da É—iyar ta daga gimbiya moumuna da Æ´an barandar ta doumin ita É—in ai gubba ce ga rayukan alhalin masarautar maraÉ—i !
Da sauri ta miƙa hannu tana ƙoƙarin amsar ƴar ta daga gare shi
Mun hakure zouwa yammaci kamar yadda ka faÉ—i mouna Biyamuradi .
Janye yumna yayi ya hana ta ɗaukar ta , a hankali ya kamo hannun tare da sarƙafe ƴan yatsun sa a cikin nata hannun yana jin yadda taushin hannun ke tado masa da yanayin da yake ta dannewa tsawon satika , " muryar sa tafe da amo marar ƙarfi yace
Mu tai ki ciyar da ni abounci na taho tare da yunwa me tsanani .
Ƙoƙarin zare hannun ta take tana satar kallon sashin gimbiya maimouna ,
Cikin sa'a idanun ta ya sauƙa akan gnala shugabar bayin sashin gimbiya moumuna ta na abunda yake goge gilashin falon gimbiyar ta ciki a zahiri , wanda tashin farko siyama ta fassara abunda take da ɗaukar rahoto
Toh Biyamuradi , amm...
Shitt
yace mata lokacin da yake jan hannun ta zouwa sashin sa kai tsaye da yumna saɓe kan kafaɗar sa ta dama tana ƙoƙarin ɗauke hular kan sa ,
Suka fara taku tare da masaniyar yau wajen ta ya kamata ya kwana a tsarin ƙwanakin girki .
Gimbiya moumuna wacce tun isar sa fada ta samou labarin zuwan sa , inda bata yi ƙasa a guiwa ba ta tashi shirin tarɓar sa ,
Ta tashi hankulan bayun ta da aikin gyara gida wasu kuma na haÉ—a mata ruwan wanka tare da fidda mata kayan da zata sanya a jikin ta ,
Zuwa shigowar sa gidan ta fito daga wanka ta fara shiri , yana dosar gidan saƙo ya iso mata , hakan ya sa ta miƙe daga gaban mudubi ta ƙarasa gaban babban window na ɗakin ta dake sama ta raba labulen biyu daga inda take ta hangi kome da ya wakana tsakanin sa da siyama .
Wani irin tuƙuƙi take ji yana taso mata daga cikin rai har tana jin ɗacin sa a maƙogoro .
Meyasa ne wankin hula ya kai ta É—are har tsakiyar sa ?? Lamarin da suka yi hasashen yiwuwar sa a watanni zuwa
Shekara bayan zuwan ta masarautar maraɗi , sai ga shi shekaru har sun fara ƙoƙarin haurawa kirgen yatsu biyar ?? Wacce iriyar mummunar rashin sa'a ne gare su haka ?? Wanne sirri ne da yake boye cikin duhu da ya zamto shamaƙin da ya shiga tsakanin ta da cikar burin ta ?? Menene shi da ya wuce tasirin ƙarfin su ??
Tattare labulen tayi ta cukuikuye shi a tafin hannun ta tana jin kamar tayi girgiza ta fasa bango ta dira a sashin yarima youssouf ta kaddamar da manufar ta ..
Ranki ya daÉ—e kÆ´akya.....
Bata bari gnala ta ƙarasa kalmomin ta ba wacce ta shigo ta durƙusa daga bayan ta ,
Da hannu ta dakatar da ita ,
Ayi gaugawar shiryawa Biyamuradi abincin sa a aika da shi shiyar sa .,
Ke zaki miƙa abincin da kan ki daga nan kin kawo mi ni labari na lamarin da ya auku gaba gare ki .
Allah ya huci ran gimbiya Æ´ar sarkin nahiyar mu maigirma oumarnin ki shine abun bi .!
da shigar su sashin nasa da yake me matuƙar girma , da tsari tare da wadatar tsaftar da ta haifar da kyakkyawan yanayi a wajen ,
Ya zauna bisa ɗaya daga cikin kujerun falon nasa , yana sauƙe yumna kan kafafun sa ,
siyama wacce ta saɓule mayafin ta ta ajiye a gefe ta sunkuya tare da yin gurfano a gaban sa , cikin nutsuwa ta kai hannuwan ta tana kunce masa igiyar takalmin sa tare da zare masa shi a hankali ,
Ɗan kiɗan da wayar sa ta yi dake nuna alamun shigowar saƙo ya sa shi zaro wayar daga aljihun sa ,
  Lokacin da take ƙoƙarin karɓe hular sa dake hannun yumna ta ƙi bada hular ,
  Ki bar mata hular mana , kin ka sani ko ɗiya tayi gadon baban ta ?
  Da murmushi bisa fuskar ta ta wuce sama domin ajiye masa takalman sa , ta zo ta fara yi masa shirin girki .
  Saƙon gimbiya maimouna ne mai ɗauke da tsararrun kalamai na barka da zuwa ƙarshe take sanar da shi ta bada saƙo a kawo masa ,
 Fita yayi daga wajen adana saƙon yana shirin ajiye wayar hoton da ya ɗauke su ɗazu ya bayyana a fuskar wayar,
Ƴan yatsun sa ya sa ya jawo hoton ya cika wayar ya na nutsar da idanun sa kan fuskar ta me ɗan haske kaɗan da take ɗauke da wani sirri me tasirin da ya zarce a ƙira shi kyau ,
fatar ta suɓul-suɓul babu wasu ƙurarraji bare tabbuna manyan idanun ta da yankan su yake a tsaye da ƙwayar baƙi na cikin su me girma ne sosai , suna da ɗaukar hankali ta yadda ko yaya ta juya su sai mutum ya gan su ,  har kullum yana dogon tunani akan son sanin me ya makanta su ??
 A hankali yayi ƙasa da hoton zuwa kan bakin ta da haƙoranta suke a buɗe tana dariya ,
  Tsintar kan sa yayi da murmusawa, ya kai babban ɗan yatsan sa yana shafar fuskar wayar daidai zagayen ɗan bakin nata ,
   lokacin da ya tuno da yadda take haɗe fuska ta tsuke bakin , duk idan ta ji motsin sa a waje , ta takura kan ta ta gaza walwala ,,
 Kiyi haƙuri fatima ni ma ba zaɓi na bane irin rayuwar da muke gudanarwa a tsakanin mu a matsayin ki ta iyalina ,girman laifi na ya sa na gaza yin wani yunƙuri , ni ɗin me laifi ne a gare ki da duk ranar da gaskiya ta bayyana wataƙila baza ki yafe min ba , hakan ya sa na jinkirta miki har zouwa lokacin da kome zai bayyana agare ki , da na tabbatar ranar ta na zouwa , lokacin kike da zaɓi na zama da ni ko bari na bisa ra'ayin kan ki ,
   Kiyi haƙuri Fatima zahra ina jin kunyar ki .
 Â
  Ƙwanƙwasa ƙofar da aka yi ya sa shi kai duban sa ga ƙofar tare da mayar da wayar sa cikin aljihu
  Daidai da ƙarasowar siyama wajen wacce kalaman sa na ƙarshe suka sauƙa cikin kunnuwan ta ,
  Suka yi sanadiyyar harɗewar takun kafafun ta tare da sa zuciyar ta yin tsalle .
Â
Wacece fatima ? Wanne matsayi ne gare ta da har Biyamuradi ke neman afouwar ta ? Shin laifin me ya aikata mata ?
Â
  Ruɗanin da ta afkawa ya hana ta tsinkayar kalaman da yake mata sai da ya ɗan ɗaga muryar sa da ƙarfi .
 Siyama ki buɗe kofar nan saƙon maimounatu ne ya iso ,
  Ba tare da ta amsa ba ta taka tana nufar ƙofar , cikin ran ta damuwa goma da ishirin ta san sarai saƙon ko na menene, abunda maimounatu ta saba yi mata ne a koyaushe , shine yau ma ta maimaita .
Tana buɗe ƙofar tayi arba da gnala tare da wasu bayu biyu hannuwan su riƙe da manyan farantai da aka rufe su da tumaƙasa irin na alfarma ,
  Ajiye faranta suka yi tare da yin gurfano a gaban ta ,
 Ranki ya daɗe barka da fitowa ! saƙo ne daga gimbiya tace a shigar da kaɓaki ga maigirma yarima .
  Fuskar ta a ɗaure ta ce
Ki je sashi na yanzu yanzu ki ƙira min Rakiya ku zo tare !
Da sauri Gnala ta miƙe
Ba ke ba .
 Tace da kaushin murya
 Ciki sauri ta koma ta tsugunna
Ke tashi ki je ki taho da Rakiya
  Tana nuni da ɗayar baiwar .
Cikin ƙasa da mintuna uku sai ga su tare da wata yarinyar mace da zata iya zuwa sa'a ga siyamar ,
  Ranki ya daɗe uwargijiya ta .
Rakiya ki É—auko waÉ—annan farantan ki biyo ni da su ,
  Ta furta haka tana juyawa ciki Rakiya ta bita ɗauke da faranti guda , kafin ta dawo ta ɗau sauran da ɗai ɗaya ta shiga da su ,
   Tana gama shigarwa ta fito gami da jan ƙofar , tana iya jiyo lokacin da uwargiyar ta ta murza ɗan mukulli ,
Kallon kallo suka yi tsakanin ta da gnala , kafin ta ratsa ta tsakanin su tana wucewa kan ta a ɗage bakin ta ɗauke da ɗan siririn murmushi ta fara rere waƙar da ta zo kan harshen ta a dai-dai lokacin
 Aiki yayi kyau , tunda gida ya gyaru tsaf-tsaf ?
  Allah kawo ran albashi mui fatantamawaaa .