← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 269

Sashe 10

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin satin mai martaba sarkin Maraɗi Abdoul-azizou Baskore ya tura da takardar neman aure ga sarki Usoumanu Ibrahim tounouss na birnin Agades , koh da sakon ya isa ga Mai martaba sarkin Agades shima ya bayyana farin cikin sa bayan da yaji ta bakin ɗiyan sa , in da ta tabbatar masa da amincewar ta tare da sake jaddada yawan ƙaunar ta ga biyamaradi youssofa, anan take mai martaba sarkin Agades ya bada tukuici mai yawa tare da takaddar jaddada amincewar sa ,"

Bayan dawowar ƴan aike daga birnin Agades a daren mai martaba sarkin Maraɗi ya gana da hajiya umma inda yake sanar da ita tayi magana ga ɗiyar ta siyama cewa a tare za'a haɗa bikin ta da na youssof dan haka ta tsaida guda cikin masoyan ta ," Anan hajiya umma bata yi ƙouron baki ba ta sanar da mai martaba haƙiƙanin shirin zuciyar ta tun daga farko ',

Ɗan jim mai martaba yayi bayan kammala jin dukkanin kalaman uwargidan sa ," sosai yaji daɗin kyakkyawar niyyar ta sai dai yadda ta ture Al'amarin bayan bayyanuwar maimouna ya sanya shi jin wani iri tamkar dai akwai sautin son kai cikin lamarin nata ," sai dai yayi saurin kauda zargin daga ransa akan sanin da yayi a duniya idan ana kirga masoyan siyama hajiya umma tana daga sahun farko ƙwarai yana alfahari da ita akan irin kyakyawan riƙon da tayi wa ƴar kanwar sa , " dan haka yace idan har ita siyama ta amince da shi youssof ɗin ya zama dole ga youssof ya auri siyama a matsayin matar sa ta biyu shekara guda bayan auren sa da maimouna idan Allah ya yadda ",

Nan take maɗaukakin farin ciki ya bayyana akan fuskar hajiya umma ,' tana mai sake jaddada masa da ƙaunar da ita siyama ta lura tana yi wa youssof ɗin tun shekarun baya ," nan dai mai martaba ya tsaida batun auren siyama da youssof sai dai ya nemi hajiya umma da ta bar batun nan a tsakanin su ,"saboda gujewa ƴan kai-kawo ', .

*Mairambiri Borno Nigeria*

Hasken ranan da ta ɗago ta fara ɗan zafi ita ta sanya ta fara motsi , kafin ta buɗe dogayen manyan idanun ta da suke farare tas tas , da sauri ta miƙe daga kwanciyar da take a cikin taɓon da ya cakuɗe da ruwan da ya kwanta a cikin ƙonanne ɗakin nasu wanda wuta ta riga ta ƙona azaran saman ɗakin ," da sauri ta fara lalube gefe-da-gefen ta , jin bata ji almun mutum a ɗakin ba ya sa ta miƙe tsaye ta fara laluben hanyar fita tare da kiran sunan ƴar uwar ta "yakaka "yakaka " santsi ne ya kwashe ta suuu ta tafi ta faɗi dabas a bakin kofar ," bayan ta ya bada ƙara ƙaƙas , " wani kuka ne ya taho mata a lokacin da wani mugun tsoro ya ɗarsu a ranta koh dai ƴan tawayen boko haram sun dawo ne jiya ? Sun tafi da yakaka ," tunanin hakan ya sa taji wani karfi ya zo mata ta yunƙura da karfin ta ," ta miƙe ta fara tafiya a cikin ruwan da ya cika tsakar gidan nasu da ƙasa bata kai ga shanye sa ba ',

Cigaba tayi da ƙwalla kiran sunan yakaka ' yakaka ' yakaka , ruwan hawaye yana me cigaba da ambaliya akan fuskar ta da karfi take jefa kafar ta ba tare da tana laluben gaban ta ba burin ta kawai ta tafi neman ƴar uwar ta ɗaya da ta rage mata," ji tayi ta kaiwa bango karo tayi taga-taga ta tafi da baya ta sake faɗuwa," da gudu take jin takun tahowar mutum kafin taji sautin muryar ta itama cikin firgici tana ƙwalla kiran sunan ta 'falmata 'falmata falmata'

Da gudu ta shigo gidan ,"wurgi tayi da ledar da take hannun ta tare da ƙarasawa gurinta zuwa lokacin ita ma kokarin tashi take tana mai sake kiran sunan "yakaka ', ɗago ta tayi tare da rumgume ta cikin jikin ta ,' itama kamkame ta tayi ," kafin su dukkanin su biyu su saki juna suna masu haɗa baki gurin tambayar junan su,'
"Falmata baki ji ciwo ba koh ?
Yakaka ina kika je babu abun da ya same ki koh ?
Banji ciwo ba yakaka ina kika tafi kika barni kin sa hankalina ya tashi kar ki sake tafiya ki barni yakaka ,"falmata ta furta hakan tana me laluben fuskar yakaka ,"

Hannun ta kai gami da share mata hawayen da suke gudu har yanzu akan ƙuncin ta ,"kafin cikin ƙarfin zuciya tace kiyi hakuri kanwata lokacin da gari ya waye naji wucewar mutane ɗai ɗaya hakan ya sa na lallaɓa na leƙa anan naga wani mutum shi ɗaya da gudu zai wuce shine na bishi nima ina tambayar sa koh ya ake ciki a gari ," shine yake gaya min shi hanya ce ta biyo da shi ta nan ƙauyen mu ,'daga ƙaramar hukumar Bama yake ," a yau suka wayi gari da afkawar ƴan tawayen boko haram a yanzu haka sun farma ƙaramar hukumar Bama suna ta kisa ,"irin dai yadda suka yi anan jiya ", mutumin ya tabbatar min da gwara na gudu domin ƴan tawayen boko haram zasu iya dawowa su mamaye dukkanin ƙauyukan da suke tsakanin Bama da Konduga tun da sun riga sun mamaye garin bama ", na tambaye shi to ina zamu ? Shine ya ce min ance wai a cikin Birnin Maiduguri gwamnati ta tanadi wurin da mutane irin mu ƴan gudun hijira zamu zauna a kula da mu kafin a yaki ƴan tawayen boko haram ,"

Tashi mu tafi falmata kar mutumin nan ya yi mana nisa kin ga mu ba mu san hanyar Maiduguri ba bamu taɓa zuwa birni ba ," zame hannun ta da yakaka ta kama tayi kafin cikin muryar kuka ta fara cewa "yakaka ni babu in da zan tafi , yakaka ba mu san inda su mama suke ba , idan muka tafi kuma su mama suka dawo neman mu fa ? Mu zauna yakaka mama zata dawo neman mu zata dawo ta tafi da mu inda ta ɓuya ,"

Share ƙwallar idon ta tayi kafin ta ce falmata su mama fa su ma sun tafi Maiduguri suna jiran mu a can ," da zasu dawo ai da tun jiya zasu dawo idan muka zauna anan koh ƴan tawayen boko haram basu kashe mu ba wuya da yunwa da kishirwa zasu kashe mu ," miƙa hannu tayi ta kamo baƙar ledar da ta shigo da ita wacce take yawo akan ruwan da yake tsakar gidan ," kin ga wannan ma tsintowa nayi a hanya wata kaza tana ta so ta fasa ledar ta kasa shine na bita na ƙwace" biredi ne a ciki ki ƙarba ki ci mu tafi falmata," ta karasa zancen da sigar rarrashi ,"

********************

Hannun su sarƙafe da na juna suke tafiya ," bayan sun fito daga gidan nasu kowaccen su tayi shiru da abun da take saƙawa a cikin ran ta .

A hankali yakaka ta waiwaya tana me kallon kofar gidan su ," sosai ta tsirawa gidan ido tamkar me son kirga adadin yawan bulon da akayi amfani da shi wurin ginin gidan ," gizo idanun ta ya fara yi inda ta hango mahaifin ta ya fito kamar yadda ya saba hannun sa riƙe da hular sa , gefe guda ita ce a tsaye hannun ta riƙe da buhun su na zuwa gona daga bakin kofar kuwa mahaifiyar su ce tana ɗaga musu hannu kamar dai yadda ta saba ," hawayen idanun ta ne suka gangaro gami da ɗiga akan kafar falmata ɗan jijjiga hannun ta da yake cikin na yakaka falmata tayi kafin ta ce mu tafi mana yakaka,"

Mu tafi falmata cewar yakaka wacce ta ke bin dukkanin ginin unguwar su da kallo hotunan al'amuran da suka gudana tun daga tasowar ta a cikin unguwar suna ta wucewa ta cikin tunanin ta ," wata irin kewar mahaifarta tana mamaÆ´ar ta tana jin tamkar ta tafi kenan ," tana jin tamkar karshen ganin ta da gidan su da garin su kenan ," gefen zuciyar ta tana jin wani sabon karfi tare da karban sabon sauyin da rayuwa ta zo mata da shi ,"yayin da take jin nawin girman da ya hau kan ta na rike kan ta da kanwar ta falmata yana kama ta,' sai dai tana jin kome runtsi da Wahala zata kula da falmata ko da ita zata rasa rayuwar ta," miskin falmata ,"

Taku Falmata ta fara yi tana me jin yadda duhu yake mamaye zuciyar ta kamar dai yadda duhun yake a zahiri a idon ta ," tana jin duk wani farin cikin da ta san ta samu daga lokacin da tayi wayo zuwa yau yana barin jikin ta ,' wani irin ƙunci yana mamaye cikin ran ta ," tana jin kuncin yana ƙaruwa da dukkanin wani takun ta guda ɗaya da take yi da niyyar barin garin su mahaifar ta , zuciyar ta tana cike da tsoron sabuwar rayuwar da zata fuskan ta alhalin tana makauniya a garin da bata da kowa bata san kowa ba sai ƴar uwar ta ," tsoro sosai ya ɗarsu a ranta " , sai dai wani sashi na ranta yana faɗa mata zata dawo watarana , wataran zata dawo garin su mahaifar ta , zata sadu da mama da sauran kannen ta ," bata san lokacin da wani matsanacin kukan da yake cike da tsoro da kuncin zuciya ya kufce mata ba ,' kuka take bilhaƙ ,"

Matsa hannun ta yakaka take yi alamun rarrashi domin a zuwa yanzu ita ma bata da karfin zuciyar rarrashin falmata domin tana da tabbacin tana buÉ—e baki kukan zuciyar da take yi zai bayyana a zahiri ," ita ma bukatar rarrashi take tana bukatar matallafin da ko da ba zai taimaka mata da kome ba ," zai furta mata kalmar ZAKI IYA YAKAKA,
Chapter 10 · 0% Book details