Sashe 2
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tayi kuka har hawayen ta ya ƙafe har tunanin ta ya tsaya , ta gigice iyakar ɗimaucewa ,ta rasa hankalin ta a tsakiyar gonar rungume da gawar mahaifin ta wanda jinin sa ya bata mata jiki face face ,har wani wuri ya fara bushewa a hankali ta ɗaga kanta ta dubi yadda dare ya fara alamun shigowa rana ta tafi zata faɗi ga kuma hadarin da yake haɗowa, cikin shishiƙar kuka ,jiri da tsananin galabaita ta ɗaga kan mahaifin nata da tun kafin rai ya kammala fita daga jikin sa ta ɗora kan sa a kan cinyoyin ta a gaban idanun ta ya rasu ,ita ta ke bashi kalmar shahada duk da karancin shekarun ta , cikin wani irin kuka ta sake mayar da kan nashi ta ajiye bisa cinyoyin nata tare da sake rungume gawar shi ( da ta Riga ta fara ƙandarewa ) tana wani irin shishikar kuka , ta ɗau tsawon lokaci a haka sannan ta sake ɗagowa tare da zare hijabin kan ta ,ta shimfiɗa cikin karfin zuciya ta sauke kansa a hankali daga jikin ta ta ɗora akan hijabin nata, kuma ta ɗauki lokaci tana yi masa addu'a.
Sannan ta mike a zabure ta juya cikin hanzari ta nufi hanyar gidan su domin ta sanar tana tafe tana waiwayen duhun ciyawar da ta riga ta kare gawar mahaifin nata , har dai ta zura da gudu tana kuka tana sharar hawayen ta.
Birki ta jaa tare da rage takun tafiyar ta lokacin da ta bullo bakin hanya , hakan yana da nasaba da guje guje gami da iface-iface da ƙarar harbe-harben da take ji yana tashi daga ainahin cikin ƙauyen nasu , kowa ta nufa da gudu domin ta tsaida shi tayi tambayar me ke faruwa sai taga an bangaje ta an wuce da gudu wasu na kuka wasu na salati da addu'o'i wasu kuwa kana ganin su ma kasan gudun ceton rayukan su suke domin dai duk sun kukkuje sun ji munanan raunika ,amma ahaka suke gudu suna barin ainahin cikin ƙauyen nasu zuwa cikin gonaki da daji.
A hankali ta ɗaga kanta sama tana iya hango yadda sararin samaniyar ƙauyen nasu ya tuniƙe da hayaki har ma tana iya hango harshen wuta da yayi tsiri yake toroƙo a wasu sashi na cikin garin, nan take wani irin tsoro da tashin hankali ya mamaye zuciyar ta tunowa da mahaifiyar da kannen ta da tayi suna cikin ƙauyen nasu ,da yanzu take hango tarwatsewar sa da mummunan bala'in da ya fada musu .
Cikin karfin zuciya ta yunƙura da gudu ta nufi hanyar gidan su , tana ta cin gware da karo da mutanen da suke gudu daga cikin garin( amma ko kula bata yi ba) zuwa lokacin da ta ji carafa an kama hannun ta da karfi an fusgo ta, da sauri ta waiwaya tana fatan ko ɗaya daga cikin ƴan gidan su ne "mamar su ko ƙannen ta.
Amma sai taga modu ne saurayin da unguwar su ɗaya ɗan maƙotan su ne , cikin sauri ta dawo da baya tare da rike hannayen sa biyu tana haki ,fuskar ta ɗauke da matsanancin tashin hankali take tambayar sa ina mamar ta ina kannen ta ? Amma maimakon ya bata amsa sai taga yana jaan ta da gudu su koma hanyar da ta bullo , da karfi ta fisge hannun ta tare da yi ma sa tsawa tana sake maimaita tambayar ta "Modu nda mamanyi nda kiramiyanyi " ?
Yakaka yanzu ba lokacin tambaya bane domin rayukan mu suna cikin haɗari , ban san inda suke ba , ki zo mu gudu yagana, kashe mutane ƴan tawayen *BOKO HARAM* suke sun yanka babanmu ,da yaa bakura sun tafi da Fannah da yaakori "(kannen sa) " maman mu ban san inda take ba ita da sauran kannen mu ,sun ƙona gidan mu da gidan ku da ....
Tunda ya fara nisa cikin bayanin sa ta daina fahimtar me yake cewa , zuciyar ta ta tafi ga tunanin me yake faruwa da su ne ?, ta yaya zata rasa kowa da kome nata a yini ɗaya ? Baban ta ya mutu , bata san inda mahaifiyar ta da kannen ta suke ba a mace suke ko a raye ? Ina zata je ? Bata da kowa bata san kowa ba bata taba zuwa ko'ina ba babu inda ta sani bayan ƙauyen su , a hankali ta juya tana nufar cikin garin su hanyar unguwar su cikin ran ta tana aiyanawa gwara ita ma a kashe ta gwara ta mutu .
Bata da karfin jiki da na zuciyar tunkarar wannan sabuwar rayuwar da take tunkaro ta wacce bata hango kome a cikin ta ba sai tarin tashin hankali wuya da wahala ,maraici da rashin madafa .
Da karfi modu yake kwala mata kira yana so ta dawo su tafi domin shi yaga irin bala'in da bata gani ba da yake cikin garin wanda mutuwa ce murarar ta , mutuwar ma ta walakanci wanda aka harbe da bindiga ya mutu shi ya ji daÉ—i akan waÉ—an da aka kwantar aka yi wa yankan rago da waÉ—an da aka sanya wa wuta suka kone kurmus ,da waÉ—an da aka jefawa bom yayi kaca-kaca da su .
Dan haka ya kasa bin ta ya taro ta "duk da cewa akwai boyayyar soyayyar Yakaka cikin ransa wanda bai kai ga bayyana ta ba" amma baya jin matakin son da yake yi mata ya kai wanda yake yiwa ransa da rayuwar sa baya jin zai iya salwantar da ran sa domin taya ta neman iyayen ta, dan haka ya sake juyawa da gudun gaske yayi gaba ba tare da ya sake waiwayar ta ba ,
Cikin rashin sanin inda take sanya kafafun take tafiya kunnuwan ta sun toshe daga jin hayaniyar da ta cika duniya, tunanin ta ya bar gangar jikin ta ta yadda har bata jin turewa da bangajewar da mutane suke mata , wanda yawancin su daga unguwannin da suke ƙasa da tasu unguwar suke fitowa wanda a halin yanzu ƴan tawayen suke far musu ,.baza ta ce ta yaya aka yi ba kawai taga kanta ne a gaban rugujajjen ƙonannen gidan nasu da har yanzu ta wasu wuraren wutar bata gama mutuwa ba domin tana iya hango hayakin da ya ke turnuke da gidan .
Da gudu ta taka ta shiga gidan tana kwalla kiran "mama "yaana "falmata " shiru taji babu motsin kowa , cikin tashin hankali take kallon tsakar gidan nasu da yake a hargitse kamar sansanin yaƙi , kome baya muhallin sa duk da daman su basu da kome a cikin gidan nasu sai tsumokarai da ƴan tsofaffin kayan aikin su na gida wanda su ma a halin yanzu duk a ƙone suke idan ka dauke randar su da take binne cikin ƙasa da gudu ta nufi ɗakin su duk da hayakin da take hangowa cikin ɗakin ta saman sa wanda rufin zanar ya riga ya cinye ,ya zama saman a buɗe yake wayam, hakan bai hana ta cusa kanta cikin ɗakin ba babu kome cikin ɗaƙin sai burbuɗin tokar wutar da ta gama cinyewa , bakikkirin hayaƙin ma daga kan guntun kayan su ne da ya gama ƙonewa ba jimawa yake tashi .
Durƙushewa tayi ta saki wani irin kuka da yake fita daga karƙashin zuciyar ta ,kukan maraicin da ya same ta a rana daya , kukan rasa komen ta da tayi , kukan sabuwar Rayuwar da take fuskanta .
Ta ɗauki tsawon lokaci tana kukan nan har zuwa lokacin da ta fahimci hayaniyar da ta cika garin nasu ta fara raguwa sai tsilla tsilla take jiyo ihu da wucewar mutane a guje , har zuwa lokacin da ta tabbatar dare yayi , ganin duhun da ya mamaye sararin samaniya , da sauri ta miƙe tunowa da tayi bata yi sallar azahar, la'asar, da magarib ba ta kuma tabbatar lokacin isha'i ya yi tana son yin addu'a ta sani bata da kowa bata da kome a yanzu sai Allah dan haka gun shi zata kai kukan ta .
Tana fitowa tsakar gidan ta rasa abun da zata yi alwala da shi ,( sakamakon duhun da ya mamaye tsakar gidan, ) da taimakon hasken walƙiyar da take ta haske sararin samaniya, ta hango wani bakin kwanon da duk wuta ta kone sa wanda ada shine kwanon da suke ji da shi duk gidan kuma shine kwanon cin abincin baban su .
Da gudu ta karasa ta É—auki kwanon ta rungume tare da fashewa da kukan tuno mahaifin ta da gawar sa take can a cikin gona bai samu ko darajar suturtawa a kai sa makwancin sa ba .
Bayan ta share hawayen ta takarasa tare da buɗe randar su wacce ita ƙadai ce ba'a tarwatsa ba a gidan su ,"dalilin tana binne ne cikin ƙasa" ta sunkuya tare da buɗe randar , hawayen idanun ta da suka ƙi tsayawa suna ɗiga cikin randar , ta yi goho tare da sa kwanon cikin randar da nufin ɗibo ruwan ciki amma sai taji hannun ta ya tokare bai karasa ƙasan ba sannan kwanon ya bigi wani abu a cikin randa a firgice ! Ta mike jikin ta yana rawa tafara jaa da baya ,tana tunanin menene a cikin randar ?
Ji da tayi kamar wata karamar dushashiyar murya tayi magana Daga cikin randar da ya sanya ta sake shiga cikin fargaba !, kuma kamar wacce aka zabura ! Sai ta nufi randa da gudu gami da durƙusawa ta leƙa cikin randar zuciyar ta cike da zumuɗin Allah ya sa tunanin ta ya zama gaskiya .
Ai kuwa da sauri ta sa hannu gami da taya ƴar uwar ta ta fitowa daga cikin randar da tayi maboya a ciki wacce bakin ta ya riga ya guntule ya farfashe daga sama , tana gama taya ta fitowa ta rungume ta cikin kuka yakaka take tambayar Falmata ina mamar su ? ina sauran ƙannen su ?