← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 269

Sashe 94

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Unguwar "Gwarimpsamy baby tayiwa tsinke , tana shiga unguwar bata yi nisa ba tayi parking a bakin wani ɗan madai-daicin gida mai ɗauke da ƙaramar ƙofa da ɗan madaidaiciyar ƙofar shigar da mota da mota ɗaya zata iya shigewa ," fita tayi ta sanya ɗan mukulli ta buɗe ƴar ƙaramar ƙofar ta shiga ta ciki ta buɗo ƴar babbar ta dawo ta tada motar tare da sanya shigar da motar cikin gidan , bayan ta kashe motar ta zagayo gami da bude ƙofar bangaren da yakaka take ta taimaka mata ta fito , "

Da kyar ta iya sanyo ƙafafun ta waje sakamakon yadda marar ta take karta mata , tana fitowa taji jiri na kwasar ta taku ɗaya ta iya yi jinin ya fara bin ƙafafun ta da gudu ,"
   Wayyo Allah ciki na
  Ta furta lokacin da tayi baya luu ta faɗi , da sauri samy baby ta taro ta tana ,"
   Na shiga uku ke yaks meye haka ? Ni samira kar ƴar mutane ta mutu a hannuna daga zuwa ," abun arziki bai karɓi kare ba ,"
  Kama ta ta sake yi ta mayar ta motar da sauri ta sake buɗe gidan ta fitar da motar ta kulle gidan gami da cilla motar a titi zuwa asibiti mafi kusa da ta sani tana tuƙi tana waiwaiyen yakaka wacce ta fara fita hayyacin ta ,"

Wani asibiti mai zaman kan sa ta kai ta inda tana zuwa aka karɓi yakaka ana tambayar samy baby meya same ta , nan ta shaida musu haihuwa tayi ɗazu da safe ɗan ya koma ,"

Nan dai suka shiga bata taimakon gaggawa bayan sun tsayar da gudun zubar jinin suka mata Allurai tare da ɗaura mata ƙarin ruwa , ba'a ɗauki lokaci ba ciwon ya lafa ta samu bacci ,,"

Agogon hannun ta Samy baby ta duba kafin ta jaa tsaki , har ƙarfe 7:40pm , wayar ta ta zaro daga cikin ƴar jakat hannun ta nan ta tadda miss calls ɗin samarin ta daban-daban , number da tayi wa suna da "Dude" ta bi bayan ƙiran ,"
  Hello boo ya kake ?
Daga chan ya amsa mata , yana tambayar ta inda ta bar wayar nan ta sanar da shi ta zo da ƙanwar ta wacce ta gaya masa ɗin , amma bata ji daɗi ba ne ,"
   Kuna wanne asibiti ya tambaye ta
  Nan ta sanar da shi asibitin da suke ,"

Ba'a ɗauki lokaci ba ya iso asibitin ,  mutum ne magidanci da ya tasamma shekaru arba'in da biyar ,

Babu kunya samy baby ta mannu da jikin sa tana masa ƙwarƙwasa lokacin da suka haɗu , kafin ya nemi da ta haɗa shi da Casher na asibitin , nan tayi masa jagora ,"
   ba ɓata lokaci ya dire naira dubu ɗari , aka rubuta takaddar shaidar biyan kuɗin aka ba samy tare da sharaɗin idan chanjin su ya rage zuwa lokacin sallamar marar lafiyar za'a mayar musu da ƙuɗin su , idan kuma su zasu yi ciko ma sai su ƙaro , "

   Basu tsaya sauraran sauran bayanan nasa ba suka yi wucewar su samy baby tana manne da jikin sa ,"

ÆŠakin da aka kwantar da yakaka suka je ,
  Har yanzu Alluran da aka mata wanda akwai na bacci a ciki basu sake ta ba , dan haka suka tadda ta tana ta baccin ta ,"
   
   Wani kallon ƙasan ido yayi mata ,"
   Yane baby na kin san fa nayi shirin daren yau tare da ke , sai kuma ga marar lafiya mun samu ,"
     Karkaɗa masa ido tayi ta wani rausaya ,
    Boo yadda kake so haka za'a yi , zamu iya tafiya mu bar ta ai ƙarƙashin kulawar ma'aikatan asibitin , ni da kaina nayi tanadin daren yau domin ka , ta ƙarasa zancen tana kashe masa ido ,"
   Wata shashar dariya ya sake kafin ya juya yana cewa
   Baby na kenan shi yasa nake daɗa jin ki a cikin jini da tsoƙa ta , bari naje mu gama da ma'aikatan asibitin game da waɗanda zasu kula da ita , sai na dawo mu wuce ,"
   
      Samy baby tare da farkan ta , basu yi tunanin a irin halin da ƴar mutane zata iya farkawa cikin dare ba , suka yi tafiyar su sheƙe ayar su suka bar ta ƙarƙashin kulawar biyu daga cikin nurses ɗin asibitin waɗanda Alhaji Gali ya danƙa musu hatimin nasara a hannun .   

   Yakaka ba ita ta farka ba sai wajen ƙarfe uku na sulusin dare , ta tashi bata jin ciwon kome illah rashin ƙarfin jiki da kuma ƙirjin ta da take ji yayi nawi a sakamakon ruwan nono da ya zo ,"

    Yawo tayi da idanun ta , ta tabbatar babu kowa a ɗakin sai ita kaɗai , miƙewa tayi ta zauna tare da zuro ƙafafun ta ƙasa tana bin ɗakin da take da kallo wanda yake wadace da hasken lantarki ,

    Hotunan abubuwan da suka wakana tun daga safiyar jiya su suka yi ta dawo mata ɗaya bayan ɗaya , kamar a lokacin suke faruwa ,"

   Wani irin kuka ta fashe da shi lokacin da tunanin ta ya kawo ta dai-dai wurin da take sanya ƙafafu tana wucewa ta gaban falmata ba tare da ta tsaya ta mata magana ba barw tayi mata sallama,damuwar da ta hango a idanun falmata a lokacin da ta waiwaye ta da kallon ƙarshe a jiya , ta tabbatar damuwar da take kwance idanun falmatan ya assasa ne ta dalilin rashin sanin halin da take ciki , ji tayi zuciyar ta ta kumburo da ta lalubi son sanin halin da falmatan take ciki har ta kwatanta a yanzu ,

   Wayyo Falmata na ta furta a sarari tana dafe ƙirjin ta , yunƙurawa tayi ta tashi da sauri ta nufi ƙofar ɗakin , kamar wacce aka dakatar kuma sai ta tsaya , tsayuwar ta baya rasa nasaba da tunowa da tayi a bigiren da take a yanzu wanda yake da tazara mai tarin yawa tsakanin ta da inda ta baro Falmata ,"

   Ruwa mau ɗumi ta ji yana kwarara ta cikin rigar ta da ya sata saurin janye rigar ta ga menene ??
    Ruwan nono ne yake zuba ," tuno da ɗiyar ta da ta bari ba tare da ta kai ga ko ganin fuskar ta ba tayi , kukan da ta baro ta tana yi wanda ta tabbatar na yunwa ne sautin sa take iya jiyowa tamkar a yanzu take ji , wani irin tausayi ne tare da wani iri lamari mai girma da ya zarce nadama taji yana bin jijiyoyin jikin ta da gudu kafin ya zo ya watsu cikin zuciyar ta , "
    Zubewa tayi akan guiwowin ta ta baje a ƙasa tana sake sakin wani ƙaƙƙarfan kukan da yake ɓullowa tun daga ƙarƙashin ran ta ,"

Ƙarfe shida na safe nurses ɗin da aka bawa ajiyar yakaka suka shigo ɗakin da take su biyu , ɗayar riƙe da magunguna tare da allurai .,"

  Turus suka yi lokacin da suka ga gadon da take babu kowa , a tsorace suka ƙarasa shigowa ɗakin ,"   i
Ina take suka haÉ—a baki wajen tambayar junan su ??
   Kamar ance su waiga suka hango ta zaune a ƙasa daga jikin bango ta takure ƙafafun ta ɗora hannayen ta bisa guiwowin ta gami da kwantar da kan ta akan hannuwan ,"

  Kin tashi ne ?  A ah ya kika zauna anan ?
   Ɗayar nurse ɗin ta tambayi Yakaka suna matsowa kusa da ita ,
   Ko gizau bata yi ba Duk da cewa idanun ta a buɗe suke ta kafe su a jikin bango ,"

   Kallon juna nurses ɗin suka yi ,"
Patient da ke muke fa , ko bakya jin hausa ne ?
     Motsa bakin ta tayi ƙasa ƙasa tace
Ina anty samy ? 
   baki da lafiya ne ? Kizo ki hau gado mu auna ki kisha maganin ki na miki allura kafin doctor naki yazo , yayar ki bata kwana a nan ba sun fita da mijin ta sun ce zasu dawo da safe ,"

   Wasa gaske , ƙememe Yakaka taƙi miƙewa daga gurin da take takure a zaune , a ƙarshe dole suka haƙura suka bar ta a wajen suka yi tafiyar su shirye shiryen tafiya gida saboda masu aikin safe zasu karɓe su , suka rubuta a cikin folder nata taƙi yadda ta sha magani kuma taƙi yadda ayi mata allura ,"

  Tara na safe ta gota aka turo ƙofar ɗakin aka shigo , samy baby ce ta shirye tsaf cikin wani ɗanɗasheshen yadi , hannun ta riƙe da ɗan kwando wanda ta zubowa yakaka abun ƙarin kumollo ,
Chapter 94 · 0% Book details