← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 269

Sashe 56

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Take falmata ta hau murna jin za'a nemo maman su ," nan dai ta hakura zata dunga zama yakaka ita zata dunga zuwa sabon aikin da ta samu !

Haka kwanaki suka jaa har yau da suke kwanaki goma sha huɗu da fara tarayyar su , zuwa yanzu yakaka tayi nisa cikin makauniyar soyayyar biyamuradi bata ji bata gani wata irin mahaukaciyar soyayyah take masa da bata ƙi ba su tabbata har abada a tare ,

Ta bangaren biyamuradi kuwa shi tun farko babu batun so atsakanin sa da yarinyar , hasalima ya ɗauke ta ne kawai a matsayin mai bashi maganin cutar da yake ganin ta kama sa a kwanakin nan na jarabar mace , wanda a yanzu kuma yake jin ya fara samun sauƙi domin a ƴan kwanakin nan yanayin da yake ji mai tsanani a duk ranar da bai kusance ta ba ya ragu , dan haka zuwa yanzu ya fara jin zai iya daina harkar gaba ɗaya tunda daman dole ce ta sanya shi farawa ,( a cewar sa )

A yau yayi niyyar sallamar yarinyar da Æ´an kuÉ—aÉ—e masu tsoka domin yau idan ya koma daji ba zai sake fitowa kwana kusa ba zai maida hankalin sa kachokam kan aiki , giyar da kan ta zai gwada barin ta na kwana biyu ,

Daga wanka ya fito jikin sa ɗaure da towel , kai tsaye ya nufi ƴar wadrobe ɗin da take ɗakin ya fiddo da mai tare da mataji ,( comb ) ya shafa mai tare da taje ƴar sumar sa da bata cika yawa ba ,  , ya jawo ƴar ƙaramar jakar matafiya da yake sako kayan sa a ciki shiga ɗaya idan zai shigo gari ya fiddo kakin sa na soji ya sanya ya fesa turare tare da ɗaura agogon sa , kayan jikin sa da ya cire wanda yake riga long-sleeved da dogon wando , ya ɗauka ya mayar cikin jakar tare da haɗo ƴan sauran tarkacen sa duk ya zuba a ciki ,

Ya samu wuri ya zauna a gefen gadon ya jawo takalman sa mahaÉ—in kayan sa yana É—aurawa a kafar sa ,

Duk abun da yake yakaka wacce take shirye tsaf a kishingiɗe a gefen gadon tana bin sa da kallon so da ƙauna haɗi da burge ta da duk wani motsi na sa yake , "

Tunani take ina ma ina ma ace wannan kyakkyawan mutumin da har yau bata kai ga sanin sunan sa ba duk kuwa da kusanci mafi girma da suka samu a tsakanin su , ina ma da zai AURE TA , ?
   Da ita kuwa ta gama jin daɗin rayuwa tare da nasarar rayuwa ,

ÆŠago kan sa yayi ya kalle ta , É—an gajeren murmushi yayi mata
    Yaya irin wannan kallo haka ƴan mata ?
Kayi kyau bature kam silum ," amma ina ta tambayar ka meyasa kai kayan ka ba irin na sauran sojoji ba , baka bani amsa ," 

A  takaice ya amsa mata saboda ni ba sojin ƙasar ku bane ,"

    To inane ƙasar ku ?

     Wani wuri ne mai nisan gaske ! ,"ya amsa mata

  Wallet ɗin sa ya ɗauka ya fiddo da dukkanin kuɗaɗen ciki , da suke sabbin ƴan dubu ɗai ɗaya , " ya tako ya zagayo ta bangaren da yakaka take ,
  Kamo hannun ta yayi tare da ɗora mata kuɗin ,"
  Ƴan mata ,( kamar yadda yake kiran ta tun haɗuwar su a zahiri ya manta sunan ta bai kuma taɓa damuwa ya sake tambayar ta sunan ta ba toh ina ruwan sa da sunan ta ? Amfanin me sunan zai masa ? )
    Ni zan tafi yau kuma bazan dawo nan kusa ba saboda yanayin aiki na , ƙila na dawo cikin sati biyu masu zuwa ƙila sai cikin wani watan watakila kuma .... Sai ya ɗan yi shiru  tare da duban fuskar ta ,"

Wacce tunda ya fara bayani idanuwan ta suka cika da ƙwalla , wani irin bugu zuciyar ta take yi ,

Zame hannun ta tayi kuɗin suka sauka akan katifar ,"  
        "ka bar kuɗin ka bature kam silum ba sai ka biya ni ba , ni dai dan Allah kar kace baza ka dawo yau ba , ka dawo dan Allah ni ko baka bani kuɗi ba zan taimaka maka kamar kullum , akwai wasu sauran kuɗin da kake bani ma ina tara su duk zan dawo maka da su ni dai dan Allah bana so na daina ganin ka , idan bana tare da kai zuciya ta bata min daɗi , na saba da kai .

tun da ta fara magana yake bin fuskar ta da kallo wacce kafin ta kammala ta jiƙe da ruwan hawaye , wani irin tausayin ta ne ya kama shi , tausayi mai tsanani , ya fahimci yarinyar ta faɗa a tarkon son sa , wanda shi kuma sam bai so hakan ba domin kuwa a zahiri bata da gurbi cikin rayuwar sa ko kaɗan , " shi kuwa ina zai kai ƴar talakawa marar galihu irin wannan yarinyar toh ya kai ta ina ? Masarautar su ? Ai auren ɗan sarki sai ƴar sarki idan kuwa ba ita ba toh sai fa ƴar manyan attajirai ," kai shi bai taɓa ɗaukar ta da wani matsayi ba ma da ya wuce macen da yake biya ta gusar masa da sha'awar sa , bata da wani banbanci da sauran karuwai !

  Duba ƴan mata ," ni akan aiki na zo ƙasar ku , batta kasancewa kullum mu zauna tare , ki ɗauki kuɗin ki riƙe a hannun ki zasu miki amfani watarana , ni akan hanya nake ," ki manta da ni kiyi rayuwar gaba har yanzu ke yarinya ce kin ji kou ? Tashi mu tai na sauke ki gida .

A motar ma share hawaye yakaka take sosai take jin ciwon barin ta da zai yi , yace wai ta manta da shi , anya ? Ita ta san baza ta iya mancewa da shi ba ," ya samu wani irin gurbi mai girma ya kafa kan sa cikin zuciyar ta ," 

kiran wayar sa shi ya katse shirun su , samun waje yayi ya tsayar da motar a gefen hanya , " nan ya amsa wayar
    Kira ne na gaggawa ake yi masa daga sansanin su na soji !

Da sauri ya buɗe murfin motar da hannu yake yiwa yakaka alama na ta sauƙa masa a mota ,"

Jikin ta a sanyaye ta sauƙa tana gama ficewa a motar ya ja murfin da ƙarfi ya harba motar bisa titi a guje .'

tsumu ta tsaya a gefen hanyar tana sake kallon kuɗin hannun ta ," kome bai mata daɗi wani irin ɗaci take ji daga ƙasan ran ta yana taso mata ,
  Matsawa tayi jikin wata mota da take tsaye a gefe ta jingina jin da tayi tsayuwa na neman gagarar ta ," kuka take son yi so take ta samu wuri tayi ta kuka ko zata ji saukin abun da take ji a ran ta , da gaske ya tafi bazai dawo ba ? ko wasa yake yi mata ?

Tun kafin ya tsallako titin daga ɗan shagon da ya tsaya ya saya kayan marmari a gefen titin ,  hasken ta ya dalle masa idanu , amma kasancewar sa mai tsananin kamun kai da nutsuwa babu ruwan sa da harkar mata (irin yadda samarin yanzu suke )  ya sa yayi saurin ɗauke kan sa ,

Har ya ƙaraso jikin motar da take jingine da take mallakin sa ce bai sake kallon inda take ba ,"

Murfin motar ya kama zai buÉ—e sannan ya juyo ya dube ta ,"
    Baiwar Allah zan ɗauke motar daga wurin ,!
    Ko gizau bata motsa ba
  Ɗan tsaki ya ja marar sauti , wasu matan dai basu da kamun kai dubi wannan yadda ta zo ta dogare a bakin titi duk masu wucewa idon su akan ta .
Ya sake maimaitawa da É—an karfi ,
   Zan ɗauki motar nace baiwar Allah

a hankali ta juyo da fuskar ta inda take jin tashin muryar sa , kamar ta san muryar ,!
   Kallon juna suka yi ido cikin ido ,
Tsai yayi yana kallon ƙwarar idon ta , shin ita ce ne ko ba ita bace ? Ƙwarar idanun ta suna tabbatar masa ita ce wacce ya shafe fiye da watanni biyu yana neman ta tsakanin sansanin su da zagayen kasuwa ,wacce a karshe ƙawar ta tace sun gudu sun bar garin ," sai dai kuma yanayin shigar ta da gogewar da ya hango tare da wannan suna ƙarya ta masa ita ce , wacce ya sani ai ƴar ƙauye ce ƙazama , wannan kuwa ƴar birni ce wayayyiya kuma ƴar gayu ," kai sai dai kamanni ,

," da sauri ya saita kan sa daga ruÉ—anin da ganin kamar wacce yake bulayin nema ce ya sanya shi ,"

  Ya ɗaure fuska gami da maimaita maganar sa ta farko cikin ƙosawa ,"

A hankali ta janye jikin ta daga motar , "
    Ta gane shi sarai shine likitan da ya sha taimakon ta tun farkon zuwan ta garin ,"! Sai dai halin da zuciyar ta ke ciki a yanzu babu damar da zata tsaya yin magana da kowa ko da kuwa kalmar gaisuwa ce , domin tana buɗe baki kukan da take yi a zuci ne zai fito fili , dan haka ta ɗauke kan ta ,' ta matsa bakin titin sosai domin tarar adaidaita ya kai ta gida tayi jinyar gangar jiki da ruhin ta da tun yanzu suka fara kewar bature kam silum ,"
Chapter 56 · 0% Book details