← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 269

Sashe 114

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai dai ganin da ta yiwa waɗanan fasiƙan ya sa ta fara tuno da wasu abubuwa masu kamanceceniya da wanda ta ga suna aikatawa , da abunda ya shiga tsakanin ta da bature kam silum ,

ba ta tarar da su a falon ba , dan haka ta sanya ƙafafu ta bar gidan , tana tafe tana jin ƙewar bature kam silum na sake lulluɓar ta , ko yana ina yanzu ? Wataƙila ma ya manta da ita ! , ruwan hawaye ta ji suna taruwa a idanun ta ,daidai lokacin da take tura babbar ƙofar gidan su malama maryam ta shiga ,

   karaf suka ci karo da lubna wacce take ƙoƙarin fitowa daga gidan hannun ta riƙe da wata leda ,

Yauwa ƙawata Dan Allah zo ki raka ni wancan gidan ummi ta aike ni ,
   Tana mata nuni da wani babban gidan da yake chan kusa da ƙarshen layin su ,
   Ba musu ta bi bayan ta , lokacin da lubnan take jan hannun ta ,

   Saƙo lubna ta kaiwa matar gidan tana bata saƙon suka mata sallama suka yi fitowar su ,

Sun zo dai-dai tsakiyar harabar babban gidan , yakaka ta ga wani É—an dogon saurayi É—an gayu ya sha gaban lubna fuskar sa a marairaice idanun sa fes akan ta ,

   Lubna Haba dan Allah ki saurareni , yau wajen watanni bakwai kenan ina bin ki da soyayya ta amma kina min walakanci , dan Allah ki TAIMAKA MIN ki yadda da soyayya ta wallahi ina tsananin son ki ,

   Ba tare da lubna ta ɗaga ido ta dube shi ba ta kewaye shi ta wuce tana sake jan hannun yakaka ,

Charaf ! Ya riƙo hannun ta Lubna Dan Allah ki taimak....

  Wani irin ƙara lubna ta sa kamar ya jona mata wuta , ta warce hannun ta da matuƙar ƙarfi cikin abinda bai wuci daƙiƙai ba ta cire hannun ta ta wanke shi da mari , kafin cikin muryar ta da take karkarwar kuka ta tace
    Kar ka kuskura ka sake taɓa ni , ni ba ƴar iska karuwa ba ce ,

   Kukan da ya zo mata ya sa ta kasa ƙarass zancen ta da gudun gaske ta juya tana barin gidan ,
   Yakaka wacce take sakakai a tsaye ta bi shi da kallon tausayi a hankali ta furta kalmar
    Kayi hakuri
  Gƴaɗa mata kai yayi
Cikin sanyin jiki ta juya ta bar shi a wajen ta nufi gida ,

Tana shiga cikin gidan ta tarar da lubna rungume jikin mamar ta banda kuka babu abunda take , malama maryam sai tambayar ta take me ya same ta ? Me aka mata ? Ta gaza bata amsa ,

  Kallo mai bayyana haushi yakaka tayi mata lokacin da take zama a gefen malama maryam ,

Anty wai fa dan kawai wani mutum ya kama hannun ta yace ta taimaka masa yana son ta shine ta mare shi ta gudo gida tana wannan kukan ,
   Ta ƙarasa zancen muryar ta na nuna jin haushin abunda lubna tayi ,

    Waye ya kama hannun ta ? Wanne mutum ne , ke lubna ɗago ki dube ni waye ne ya riƙe miki hannu meye tsakanin ku da shi ? Ki faɗa min gaskiya ,
   cikin shisshiƙar kuka lubna tace ummi , Mukhtar ne ɗan gidan Alhaji Umar , shine tun watannin baya yake tare ni yana cewa wai yana so na , shine yau ya tare ni a gidan su har ya riƙe min hannu wai na taimake shi yana so na ,

    Nan take fushi mai tsanani ya bayyana a fuskar malama maryam , ta shiga yin faɗa meyasa tun ranar farko lubna bata sanar mata ba ? Ita kuma ta faɗawa baban su lubnar ya sami mahaifin yaron anyi musu tsakani ba ,
    Faɗa take yiwa lubna tamkar zata doke ta , a karshe ta gargaɗe kan ko kusa ta da shi bata yadda ta sake tsayawa ba kuma zata faɗawa baban su ya sanar da mahaifin yaron su ja kunnen ɗan su , ya fitar harkar ƴar su ,

  Sororo ! Yakaka tayi cikin jin mamakin malama maryam menene abun tashin hankali haka ?
  Da son kwantar mata da hankali tace ,

   Anty ai hannun ta fa kawai ya riƙe , kuma fa cewa yayi ta taimaka masa ,

wani irin kallo malama maryam tayi mata ,

   Yakaka ,

Namiji baligi ya kama hannun mace baliga haramun ne a musulunci , muddin ba muharamman juna suke ba domin tafarki ne na samar da ZINA a tsakanin mace da namiji  ,

Zina kuma haramun ce a musulunci, kuma tana daga cikin manyan laifuka wanda ake kira Kaba'ir.
Allah ya fada cikin Qur'ani
و لا تقرب الزنى
Wato kada a kusanci zina.
Hikimar fadin hakan shine ba aikata zina kadai ba, aikata abunda zai janyo zinar irinsu rungumar juna , taɓe-taɓen juna da shafe-shafen jikin juna tsakanin namiji da mace dukkansu Allah yayi hani domin hanya ce ta kusanta kai ga zina ,

cikin sanyin murya yakaka tace

Anty menene ZINA  ??

Zina ita ce Saduwa a tsakanin namiji da mace ,( ina nufin mace da namiji su kasance cikin abun rufuwa É—aya jikin su na cikin na juna , azzakarin namiji yana cikin farjin mace ) ba tare da hukuncin aure ya shiga tsakanin su ba , duk mace da namijin da suka yi tarayya irin haka ba tare da an É—aura musu aure kamar yadda addinin musulunci ya koyar ba to babu shakka sun aikata zina ,

kamar yadda na faÉ—a miki ita zina tana cikin manyan laifukan da Allah yayi hani da su sannan kuma ya tanadi hukunci ga duk waÉ—anda suka aikata ta ,

Hukuncin Zina a shari'ance ,  ita zina ba'a tabbatar wa da mutum ita dole sai da hujjoji, hujjoji guda biyu ne ko dai mutum ya yarda da kanshi ya aikata , ko kuma mutane huɗu su ganshi turmi da taɓarya a wannan hali ne ake tabbatar da zina,

Amma ko mutune uku ne suka ce sun ganshi turmi da taɓarya sai ɗaya yace shi dai ya gansu a tube suna shafe shafe to baza a karbi shaidun su ba, za'ai musu bulalar ƙazafi tamanin tamanin ,

Amma idan shaidu sun kammala ko mutum ya amsa da bakin sa yayi zina Hukuncin sa a shari'ance shine bulala É—ari ga waÉ—anda basu taba aure ba. Kamar Yadda Allah ya faÉ—a"

الزانية والزانى فاجلدا كل واحد منهما مأة جلدة، ولا تأخذكم بهما رأفة فى دين الله إن كنتم تؤمنون بالله واليوم الآخر.
Wato mazinaci da mazinaciya ayi wa kowanne su bulala É—ari, kada tausayi ya kama masu dukan idan har sun kasance masu imani da Allah da ranar lahira.

Sai wanda yayi aure akwai hadisin da yace duk mai aure ko wanda ya taɓa aure idan ya taɓa zina za'a jefe shi, amma sai idan shine da kanshi yazo yace yayi zina yana so a jefe shi, amma idan bai yadda a jefe shi ba ba za'ayi mishi dole ba za'a barshi ne.

Wani irin tsoro da tashin hankali me tsanani ne ya dirar mata , cikin wata irin muryar da ke bayyana tsantsar firgicin da ruhin ta ke ciki , tace

   Anty ko da mutum taimako yayi ,

Malama maryam cikin tsanaki tace ban fahimce ki ba yakaka wanne irin taimako ne yake zuwa ta hanyar aikata zina ??

Anty ina nufin ko shi namijin cewa yayi mace ta taimaka masa , sai ita ma ta taimaka masa , suka yi , shikenan tayi zina ??

Su dukan su sun aikata zina , saboda babu biyayya ko temakekeniya tsakanin bayin Allah wajen saɓa masa , su dukkanin su basu da hujjar kare kan su , suyi gaggawar tuba ga ubangiji domin zina babbar musiba ce ,

Sannan kuma yakaka ai duk namijin da zai cewa mace ta taimaka masa ta bashi kan ta suyi zina , ai wannan babban maƙiyi ne a gare ta , bata da maƙiyi sama da shi , mugu ne kuma macuci domin na farko zai ɓata tsakanin ta da ubangiji , yasa ta aikata abunda Allah zai yi fushi da ita , da zai hana ta samun ganin Alkhairi da dacewa cikin rayuwar ta duniya da lahira har sai idan ta tuba ,

Na biyu duk ranar da mutane suka san me suke aikatawa, mutanen kirki zasu guje ta , za'a dunga mata kallon fasiƙa, mazinaciya ƴar iska , karuwa .

Na uku idan ta hanyar zina da suka aikata ta samu ciki ta haihu , abun da ta haifa idan ya girma shi ma da kan sa zai tsane ta , ƙimar ta zata zube a idanun abunda ta haifa , saboda ta zamto sanadin da mutane zasu dunga ƙyamatar sa da ganin sa wani mutum da aka samar da shi ta haramtatciyar hanya ,

Bayan haka illolin zina suna da yawa , daga ciki akwai É—aukar munanan cututtuka da zasu iya kai me su ga mutuwa ,

A ƙarshe namijin da duk zai yi zina da mace abu ne me wuya ya aure ta , ko da ya aure ta kuma bazai taɓa ganin ƙimar ta da mutuncin ta ba , sannan ƙanƙanin kuskure zai iya haifar da zargi a tsakanin su da zai lalata musu aure ,

Kuma duk macen da tayi zina kafin tayi aure bata da wata martaba a idanun duk wani namijin da zai zo ya aure daga baya saboda ta rasa ƙima da mutuncin ta na ƴa mace tunda tayi zina .

Ki gujewa abunda duk zai kai ki ga aikata ZINA yakaka cikin ta akwai tarin masifu kin ji ko ??

Bata amsa ba illa miƙewar da tayi bata tsaya ba ta taka da gudun gaske tana barin gidan ba ta ko tsaya ta sanya takalman ta ba bare ta saurari ƙiran da malama maryam take mata ,
Chapter 114 · 0% Book details