Sashe 227
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fuskar sa ɗauke da faffaɗan murmushi ya miƙawa Malam Idris ( Mijin Malama Maryam ) Hannu suka yi musabaha , lokacin da yake miƙewa da shirin tafiya , bakin sa ɗauke da duk wasu kalmomin da ake iya amfani da su wajen godiya ga mutumin da ya kai maƙura wajen yi maka Alkhairi .
Da farin-ciki su ma suke amsa masa suna masa rakiya , fitowar su tsakar gida ya zira hannuwansa duk biyu a Aljihu , kuɗaɗen ciki da bai ƙirga su ba su ya tattaro baki ɗaya ya danƙawa Sadiq da yake tsaye a gefe cike da ladabi ya sanya hannu biyu ya amsa yana godiya .
Sun rabu cikin mutunta juna ya jaa motar sa yana barin unguwar , daga cikin zuciyar sa yake jin ɗaguwar wani abu mai kama da nannauyan dutse da ya danne masa zuciya ya taƙaita masa walwalar sa shekara da shekaru ,
ji yake kamar an tsamo sa daga cikin wani zuzzurfan ramin da ya faɗa a ciki , yanayin da yake ji bai taɓa tsintar kansa a ciki ba soyayya mahaɗi ce ta rayuwar kowanne ɗan Adam wanda da zarar an samu tangarɗa ta bangaren ta sai rayuwa ta zama kamar lami babu armashi a cikin ta .
Tuƙin da yake yi yaji yana neman gagarar sa zuciyar sa na neman abokin taya ta murnar da 'yancin da ta samu , dan haka ya gangara gefen titi ya tsaya , jingina kansa yayi da jikin kujerar motar bai ankara ba ya tsinci kansa da yin murmushi lokacin da ya ji wani ruwa-ruwa na taruwa a gurbin idanun sa ( ƙwallar farin-ciki ) shi kaɗai kawai yake ta murmusawa wanda bai san shi ba wanan lokacin zai zaci mutsa-mutsai ne suka hau kan sa .
" Alhamdulillah ,yace yana kai hannu kan wayar da take ajiye a gefen sa ya ɗauka laluben wanda zai ƙira a dai-dai lokacin yake yi ,
Doctor Suleiman shine wanda ya fara faɗo masa arai domin ya raba farin-cikin sa da shi, saboda sanadin sa ya samu kubta daga ramin da zargi ya haƙa masa a zuci ya faɗa .
sai dai tunowa da ya yi da alaƙar da ta taɓa giftawa a tsakanin sa da Yakaka ya sa shi fasa ƙiran sa , daga ƙasan ran sa yake jin tasowar kishin son da Suleiman ya taɓa yiwa Yakaka .
Ajiyar zuciya yayi yana jin yadda zuciyar sa ke bijiro masa da wacce tafi dacewa da ya ƙira a lokacin .
Tunowa yayi da ba shi da number ta , ba ma shi da tabbacin ko tana da waya,ko babu , shiru yayi jim ! Yana tunanin ina zai samu layin ta ? Yana jin nawin Amnee da Khaalty Rahima ba zai iya tambayar su ba .
Rahima ƙarama ita ce ta faɗo masa , yasan muddin dai tana da waya zai samu layin ta wajen Rahima '
Yana ƙiran ta kuwa ta ɗaga , bayan sun gaisa ya ɗan yi gyaran murya kafin yace " Rahima kina da number Mata ta kuwa ?
ÆŠan shiru Rahima tayi kafin tace " eh Big bro ina da number Auntie Sofiya...
" Ba sofiya nake nufi ba Number My Pure Woman nake nema ai tana da waya ko ?
Murmushi Rahima tayi lokacin da ta fahimci wacce yake nufi amma dan ta sake tabbatarwa sai tace " number Yakaka ko Big Bro ?
"Yakaka ba suna bane ku daina ƙiran ta da wanan sunan ku dai samar mata da wani sunan da ya dace da ita mai daɗin saurare idan ba za'a ƙira ta da Aminah ba. Ya zarce da cewa "ki turo min da Number ta yanzu . bai saurari dariyar da take yi ƙasa-ƙasa ba ya sauƙe wayar sa .
Ba'a cika mintuna biyu ba Rahima ta turo number , cikin zumuɗi ya danna ƙiran yana fatan Allah yasa ta ɗaga da sauri .
Yakaka wacce tunda ta ji irin zagin da Sofiya ta biyo ta da shi , ta tsorata jikin ta kuma yayi sanyi lakwas daga haka tana iya hango kusancin da suke da shi da Matar sa tunda har tana iya ɗaga wayar sa idan an ƙira , wani sashi na zuciyar ta ma raɗa mata yake cewa duk a gaban sa sofiya ta ƙira ta da Akuya .
Hawaye ta ji yana neman zubo mata , ita kam wannan auren nata bata hango jin daÉ—in sa ba .
Jiki a sanyaye ta fito daga ɗakin, ta sauƙa ƙasa inda ta tarar Amnee na yiwa Falmata ƙunshi a ƙafafun ta da ƴan yatsu zama tayi tana taya Amnee gyarawa Falmata tsaruwar layin ƙunshin , fuskar ta babu walwala sosai tace " Falmata naso raka ki har ɗakin ki , na mayar da ke saboda ni nayi sanadin tahowar ki , amma ban samu dama ba Yaa Dakta bai barni ba , amma insha Allah idan kin haihu zan je kin ji ko ?
Gyaɗa kai Falmata tayi da ɗan murmushi tace " Yakaka ai daman nasan Yaa Dakta ba zai yarda ba Amaryar sa ta kama hanyar ƙasar Niger rairayin ƙasa ya turbuɗe masa ke ..
" ki min shiru , Yakaka ta katse ta tana 'yar hararar ta tare da satar kallon Amnee wacce tayi kamar bata jin me suke cewa ,
Dafe baki Falmata tayi kafin tace "to nayi shiruna Allah ya kai mu.
Daga haka tayi shiru daga ƙasan ran ta tana ji rashin daɗi da bata samu rakiyar Yakaka ba saboda duk guri idan har da Yakaka tana jin wata irin kariya ta musamman daga jiki har ruhin ta .
Bayan Yakaka ta idar da Sallar azahar tana zaune akan sallayar wayar ta ta fara ƙidan shigowar ƙira .
Da sauri ta miƙa hannu ta ɗauki wayar zuciyar ta na ƙirgo mata waɗanda zasu iya ƙiran ta a dai-dai lokacin , number da ta gani ta sa bugun zuciyar ta sauyawa, take zuciyar ta ta bijiro mata da tambayar "me kuma Sofiya ta ƙira ta sake cewa ? Ko cin mutuncin da tayi mata ne bai ishe ta ba ?
Har wayar ta tsinke bata ɗaga ba , a take kuma aka sake ƙira , tsoron ta ya sake ninkuwa da ta tuno ko dai shine yake ƙiran nata ? Kar kuma tayi laifi idan taƙi ɗagawa Dan haka kafin wayar ta kai ga katsewa sai ta ɗaga ƙiran a ɗan tsorace ta kara wayar a kunnen ta tayi shiru .
Doctor Hamza da ya ƙagauta da ya ji muryar ta ya saita sautin sa ƙasa kaɗan kafin yace " Hello Wafaa , ya kike ?
Shiru Yakaka tayi tana son daidaita nutsuwar ta dan ita gaba É—aya ma a gigice take da jin muryar sa dan haka sai tace " Salamu Alaikum Yaya Dakta , ba Wafaa bace ba ni ce .
Shiru ta ji yayi kamar baya kan wayar É—an dubawa tayi ta ga yana nan akan layin tsoron kar ya kashe wayar ba tare da ta faÉ—a masa abunda take son cewa ba yasa ta cigaba da cewa " Daman ina so ne Dan Allah.....
" Shiiit ki tsaya mu gaisa Wafaa , ko haka ake gaishe da Masoyi?
Saƙato Yakaka tayi da wayar tana jin mamakin sa a take tayi tunanin ko dai bacci yake yana mafarki da wata can wai wafaa ?
Dan haka cikin sanyin murya ta sake cewa "Yaa Dakta ni ce fa ?
Dariyar da take taso masa ya danne yana sake ƙasa da murya yace " ke ce wa?
Kamar zata fashe da kuka tace " Ni ce fa Yakaka yayar Falmata .
Murmushi yayi yana rufe idanun sa cikin ran sa cewa yake " tana son sunan nan tana kuma son ƙanwar ta .
" sunan ki ba Yakaka ba , sunan ki Amina kin ji ko wafaa ?
Shiru tayi , tana son haɗa kalmar da za ta faɗa a lokacin fahimta da tayi zuwa yanzu ya gane ta kawai walaƙanci ne ya sa shi ƙiran ta da wata wai wafaa , ɓata rai tayi kamar yana ganin ta tace
. "Ni dai daman iznin raka Falmata Niger nake nema a wajen ka ? 'Yan uwan mijin ta sun zo zasu koma da ita shine zan raka ta .
Wani irin bugu zuciyar sa ta shiga yi kamar tana gaban sa ya tattare girar idanunsa cikin muryar sa da bata cika ƙarfi ba yace " Wafaa me kike son cewa ? Da auren nawa akan ki za ki tafi har Niger ? Ki je ki ga wannan ɗan....
Shiru yayi yana son dawo da nutsuwar sa da kishi yake neman raba shi da shi nan take , da wani irin sauti yace " baza ki tafi ba kina jina ko ?
A tsorace tace " ina ji .
. "Good .
yace kafin ya kashe wayar sa .
Wani irin zafi yake ji a zuciyar sa kan cewa da tayi zata je Niger garin su wannan É—an iskan sojan har cikin gidan sa kuma ?
Alhalin da yau yana da iko bayan duk labarin da Malama Maryam ta sanar masa har auren sa da Falmata a halin yanzu ko Fatima ba zata sake kwana da igiyar auren sa ba , tunani ma ya dunga yi kan me yasa Baa ya ba shi auren Fatima ? Alhalin shi É—in bai can-canta ba .
Ko ma meye shi dai zai killace matar sa daga yin duk wata mu'amala da shi ko dangin sa duk kuwa da cewa yana auren ƙanwar ta ba zai jura ba ya ga ko da kalmar gaisuwa ta sake shiga tsakanin su.( anya kuwa likita ayi haka ?? )
Bai bari maganar da ta faɗa ta ɓata masa farin-cikin sa ba saboda zuwa yanzu yasan wacece haƙiƙanin ta , mace ce mai kyautayi da son kyautatawa mai saurin yarda da yawan sadauƙarwa halinta kenan halittar ta ce shiyasa ya raɗa mata suna ( Wafaa ).