← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 269

Sashe 107

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan gaisuwa da suka yi prof bai bari ya É—ora kome ba yace bari suyi sallah su ci abinci ,

Bayan sun ɗan taɓa abincin da ba sosai Biyamuradi Youssouf ya ci ba ,

Prof ya tattara hankalin sa ga Youssouf yana saurarar sa inda yake sanar da shi ,
   Yana so gobe ya zo ya ɗauki ɗiyar sa saboda a goben yake son komawa ƙasar su domin aikin sa ya kammala ,'

Shiru prof yayi yana É—an nazari

yayin da zuciyar yarima ta cika taf da taraddadi tare da fatan kar wata matsala ta taso domin zuwa yanzu ya gama tsara kome game da makomar rikon ƴar sa a tare da shi , ya gama tsara inda zai kai ta tayi rayuwa irin wacce yake so ƙarƙashin inuwar kulawar sa da kuma kariyar sa ,

dan haka baya jin akwai wani abunda ya isa ya hana shi ɗauke ɗiyar sa daga hannun waɗannan mutanen da bai kai ga sanin su ba basu kuma da kowacce irin alaƙa da shi da har zai iya barin jinin sa tare da su , ya shirya tsaf ko ta tsiya ko ta arziki zai tafi da ƴar sa !

Gyaran murya prof yayi kafin ya É—ora da cewa ,
    Ɗa na mai zai hana idan har ka amince ka bar jaririyar nan a hannun ƴar uwar mahaifiyar ta har zuwa lokacin da ta ɗan tasa tayi wayo shekaru biyu zuwa uku sai ka dawo ka ɗau ƴar ka , baka ganin yanzu idan aka raba yarinyar nan ƙanwa ga mahaifiyar ƴar , zata shiga damuwa me tarin yawa ganin cewa har zuwa yanzu ba ta kai ga gyagijewa daga ruɗanin da mutuwar yayar ta ya jaza mata ba ,bugu da ƙari bata da kowa nata a halin yanzu sai ita wannan ƴar ta ka , ka duba magana ta da kyau ,
   Ya ƙarasa zancen da bada zaɓi ga Biyamuradi ,

Ba domin tun ganin farko da Youssouf ɗin ya yiwa prof ɗin ya riga ya cika masa ido da ƙwarjinin sa tare da cikar kamalar sa ba , sannan halin dattaku da mutuntaka da ya dunga nuna masa a kowacce haɗuwar su , mafi muhimmanci kula da rayuwar ƴar sa da yayi na wani lokaci ,

bayan haka da babu abunda zai hana ya kartawa prof rashin mutunci , ya kuma gwada ƙarfin ikon sa na soja , sannan da ƙafafar su ta sarakai da koyaushe abunda suka so shi ake mu su ba'a musa mu su , ya ɗauke ƴar sa yayi tafiyar sa , to amma girma prof nada yawa a idanun sa dan haka ya sassauta murya tare da saita nutsuwar sa yace

   Baba nan ba kassa ta ba , sannan ni kuma ai ma'aikaci ne , idan na tafi na bar ɗiya ta nan hankali na basshi kwanciya , chan inda zan tahi da ita nan ai shi tushe da assalin ta , kayi haƙuri baba zan tahi da ɗiya ta na ɗau Alƙawarin zan wanzu ina kawo ta lokaci zuwou lokkaci ta ga innon ta da yardar Allah ,

Shiru prof yayi yana jin tausayin falmata na kawo masa , bashi da wani ƙarfin iko akan yaran , bai haɗa kome da su ba idan banda taimakon su da ya biyo ta hannun sa dan haka shi baya da ƙarfin hanawa Biyamuradi ɗiyar sa ,
    Toh bari a ƙira ita uwar riƙon ƴar ta ji daga bakin ka , kafin gobe da zaka dawo ɗaukar ƴar ,

Rahima ce ta rako falmata a yau da kallo ɗaya za'a mata a gane gaf take da ɓarkewa da kuka saboda ƙiran da aka mata ta kawo baby mama
  
Daga gefe ta gurfana bayan ta gaishe da prof , tayi shiru ,

Fatima ga baban jaririya nan ya sake dawowa yau , miƙa masa ƴar sa ya gan ta ,

    shiru tayi bata ce ƙala ba

    A hankali Rahima ta zare baby mama daga hannun ta wacce take ta wasa da hannuwan ta idanun ta tar a buɗe , shirye take tsaf cikin jar riga ta jarirai mai haɗe da wondo da safa , kan ta lulluɓe da farar hular sanyi mai ratsin ado da fulawoyi jajaye ,

Hannun Youssouf har rawa yake lokacin da yake ƙarbar yar jaririyar , yana ƙarbar ta ya zarce da ita zuwa fuskar sa inda ya sumbanci kumatun ta zuwa goshin ta , bakin sa ɗauke da addu'o'i ya kama wannan ya Sake waccen ,

Farin cikin sa ya yawaita da har ya gaza boyuwa ya bayyana akan fuskar sa dake ɗauke da murmushi mai bayyana haƙora ,

maida ita ƙirjin sa yayi ya rungume ta rungumar da ke bayyana tsantsar so da ƙaunar da yake mata , ji yake kamar ya buɗe cikin ƙirjin sa ya ɓoye ta ,
   Da dariya akan fuskar sa ya ɗago cikin cewa
    Ɗiya ta girma sossai , hala wanni sinadarin ƙara wa jarirai girma da lafiya kuke bata ?  Madallah Madallah da ku , "
  
  Ɗan murmushi prof yayi , kafin ya maida ganin sa kan falmata wacce ta ƙagu a miƙo mata baby mama suyi tafiyar su ,

  Fatima kina ji na ko ?
Ina ji Baba
  Ta amsa da ladabi cikin muryar ta ,

Baban jaririyar nan ne ya zo yau yake shaida mana ya gama aikin sa da ya kawo shi nigeria nan ƙasar mu , dan haka gobe yake son komawa tare da ƴar sa , a shiryawa jaririya kayan ta kafin gobe ,

Tamkar kunnen ta ya toshe haka ta ji dumm , cikin kan ta , tana jin yadda kalmar a haɗa kayan baby mama za'a tafi da ita gobe yana bin duk wata gaɓɓa mai kuzari a jikin ta yana kassarawa ,
 
wanne azzalumi ne yake neman ta ƙarfi da yaji sai ya raba ta da jinin ta ɗaya tal da ta rage mata a duniya , ?

Da wani nisasshen yanayi cikin muryar ta ta É—ago kan ta tana saita idanun ta inda ta ji tashin muryar youssouf É—in a É—azu tace

Wanene kai ? Me muka maka kake son raba mu ? Aina kasan yakaka na ?meyasa kake ƙarya ?

  Shiru tayi tana jin yadda fitar numfashin ta ke sauyawa kafin ta ce cikin ƙarajin kukan da ya taho mata ,

ƙarya kake baby mama bata da BABA kai ba baban ta bane , yakaka ita kaɗai ta haifi baby mama , ina kake lokacin da yakaka take rashin lafiya akan cikin baby mama ? Ina kake lokacin da yakaka take shan wahala alhali baby mama tana cikin ta ? Aina kake lokacin da Yakaka na ta mutu sanadin haihuwar baby mama ??  Ƙarya kake kai mugu ne , ba kai bane baban baby kana so ne ka gudu da ita ,

   rarrafawa tayi inda ta ji sautin baba prof yana ƙoƙarin son katse mata maganganun ta ,

Illahirin jikin ta rawa yake lokacin da ta dangana da jikin kujerar da yake zaune ,

   ba-ba-Baba bani da kowa sai baby yakaka dan Allah kar ku bari ya raba ni da ita wallahi ƙarya yake yi maka , Baba ni miskiniya ce dan Allah kar ka bari ya zalunce mu ni da baby yakaka dan Allah Baba ,!
 

Wani irin yanayi me wuyar fassara prof ya tsinci kan sa a ciki ƙwarai da yana da iko da yau ya hana youssouf ɗaukar jaririyar nan ya bar ta a hannun yarinyar nan , "

Idon sa ya sauke akan Youssouf ɗin wanda kan sa yake sunkuye yana kallon fuskar ƴar sa ,tamkar bai san da bulayin da Falmata ke yi ba, sam baya so tausayin falmata da ya fara tsirga masa ya sanya shi barin ƴar da Allah ya jarabbe shi akan ta  hannun mutanen da ba shi da tabbacin zasu iya riƙon ta har tsawon rayuwar ta ba , kar watarana ta walakanta ko ta sha wuyar rayuwa , ƴar sa mace ce ƙwarai tana buƙatar uba a halin tafiyar rayuwar ta nan duniya ,

shi ya barranta daga samari irin sa waɗanda zasu samu haihuwa ta haramtatciyar hanya su ƙarawa kan su zunubi ta hanyar yin watsi da abunda suka haifa ko ma su kashe baki ɗaya , yana so ya ubangiji ya yafe masa akan zunubin da yayi ma ta hanyar samar da ita baya fatan shaiɗan ya sake jaan sa ya aikata wani zunubin da yafi wanda ya aikata a baya muni ,

Mayar da ganin sa prof yayi ga Falmata cikin sigar rarrashi yace fatima ki daina cewa jaririyar nan bata da Baba , alhalin ga baban ta nan a zaune  yana jin ki babu kyau haka , kiyi haƙuri ki bari ya tafi da ƴar sa yayi alƙawarin zai dunga kawo ta nan gidan gurin ki kin ji ko ?

sai lokacin Youssouf ya É—ago kan sa ya dube ta ,
   Ƙwarai nayi alƙawari ƙanwa ta,  zan dunga kawo ta zouwa gare ki har girman ta , ke ai har abada uwa kike a gare ta ,

Zumbur ta miƙe tsaye , cikin takun da kafafun ta ke harɗewa ta nufi inda take jin tashin muryar sa ,

  Hannun ta duka biyu ta miƙa da zummar riƙe sa yayi saurin kaucewa yana sake boye baby mama cikin ƙirjin sa ,
    Gefen rigar sa tayi wa wani ƙaƙƙarfan riƙo ba da wasa ba , Cewa take

  Dan Allah ! Dan Allah ka ji tausayi na ka bar min baby , Dan Allah kar ka raba ni da ita , zan mutu idan ka ɗauke ta , dan Allah .....
       Numfashin ta ne ya fara tsarƙewa dai-dai da ƙarasowar Rahima wacce prof ya yiwa umarni da ta janye Falmata  , hawayen tausayin Falmatan suna zarya a kumatun ta ,

Luuuu ta tafi baya ta faɗi bisa jikin rahima suka ƙarasa bajewa a ƙasa tare babu alamun numfashi ga Falmata ,
Chapter 107 · 0% Book details