← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 161 OF 269

Sashe 161

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   So take tace masa akwai hanya mana ,  sai dai tana cike da tsoro , da jin nawi tare da zargin ko matsayin da take da shi a wajen sa bai kai wannan matakin ba , mafi girman lamarin ya tambayeta ƙarin bayani , to tace da shi me ? Ko a mafarki bata jin ta san amsar da zata iya ba shi .

Cikin sanyin jiki ta tashi , da gudu mama ta sauƙa daga jikin Baban ta ta zo ta kama hannun Falmata , sannu kan hankali tayi mata jagora zuwa ɗaki  ,

Ajiyar zuciya ya sauƙe bayan shigewar su ɗaki , bai ji daɗin sanyin da jikinta yayi ba kan amsar da ya bata ,

Mayo clinic

Doctor Omer Berat ɗan asalin ƙasar turkiyya ( Turkey ) da aiki ya kawo shi Amurka , shine ƙwararren likitan ido da zai duba lafiyar Idon Falmata ,

Bayan sun shiga wajen sa tare da taimakon na'urar fassara yare suka gaisa ,

Babu ɓata lokaci ya nemi da ya fara zantawa da marar lafiyar sa ,

A hankali Youssouf ya kamo hannun Falmata da take zaune a kujerar da take fuskantar ta shi yace ,

  "Fatima ki saurara da kyau likita ke son yin magana da ke kan lafiyar ki .

" Lafiya ta ko ta Mama ?

"Lafiyar idon ki Fatima .

Ya amsa yana sake tabbatar mata ,

Mayar da hankali tayi ga likitan lokacin da ta ji ya ƙira sunan ta ,

Ta amsa , tana mamaki daman ita ya kawo asibitin a yau ?

Tambayoyi ne sosai Likitan yake yi mata da mafi yawan su Falmata bata da takamai-mai amsar su domin tambayoyin sun shafi asalin dalilin sumuwar rashin lafiyar idon nata da ita bata sani ba , amsar da ta bashi a ƙarshe ita ce

  " Je ne sais pas, je viens de vivre dans la cécité , mes parents sont morts sans me dire à quel point j'étais aveugle . ( nima ban sani ba kawai na tsinci kaina cikin rayuwar makanta kuma iyayena sun mutu ba tare da sun bani labarin yadda makanta ta ta samo asali ba . )
  Biyamuradi Youssouf da amsar ta ta taɓa masa zuciya , ya sake runtse hannun ta cikin nashi , yana jin yadda tausayin ta ya kawo masa .

bayan É—an guntun rubutun da likitan yayi ya umarci Falmata da ta zo kan É—an wani gado da yake daga gefe a ofishin ya duba idanun nata ,

Har bakin gadon Biyamuradi ya kama hannun ta , ya kaita tare da kama mata ta hau gadon ta kwanta  ,

Doctor Omer ya haska ƙwarar idanun nata da penlight , ya ɗora da tambayar ta ko ta ga haske ? Tace ita bata ganin kome ,

Cigaba yayi da haska idon yana dubawa , a ƙarshe ya kunna slit-lamp ya dallare mata ido da haske ,

Wani irin kaifi ta ji ya soki idanun ta da ya sata kifta idanun da sauri tare da kai hannu biyu ta riƙe kanta da ya sara mata ,

"washh kaina .

" Sannu ', ita ce kalmar da Youssouf ya furta da sauri yana riƙo hannuwan nata ya sauƙe daga kan ta ,

  Bata amsa ba illa riƙe hannun sa da tayi saboda yadda har yanzu take ji ba dai-dai ba a ƙwarar idanun ta .

  Bayan likita ya gama dube-dube a ainashin cikin ƙwarar idanun ta ,

Biyamuradi Youssouf ya kamata suka dawo wajen zaman su suna fuskantar likitan da yake rubuce-rubucen sa cikin kwamfiyuta ,

Turo ƙofar ofishin akayi wata mace ta shigo , babu ɓata lokaci ta jagoranci su Youssouf zuwa wani sashi na daban inda aka yiwa Falmata hoton ƙwarar ido aka tura ga sakamakon ga Likitan ta ta kwamfiyuta kamar yadda ya turo musu da bayanan irin hoton da yake so su yi mata ta kwamfiyuta .

Kafin isowar su hoto tare da bayanan da duk suka dace sun riga sun iso masa , dan haka bayan ya kammala binciken sa  , ya zunkuɗa yana mai gyara zaman gilashin idon sa , ya shiga yi musu bayani dalla-dallah cikin turancin sa yayin da su kuma pilot-in-ear yake fassara musu cikin faransanci ,

Iritis shine ciwon da ya haddasawa Falmata matsalar idanu da har ya kai ga ta rasa ganinta , shi iritis wata cuta ce da take samun ƙwayar baƙi/brown na tsakiyar idon ɗan adam , da take kumbura ƙwayar idon , sa ciwon ƙwayar idon da disashe gani ,gaza ɗaukar haske da sauran matsaltsalu da dama ,

wanda ake iya samun sa ta hanyoyin da suka haɗa da ƙwayoyin cutar maɗamfari ( infection ) , jin ciwo kai tsaye ga cikin ido , kamar bugu zuwa ƙwarar ido na daga kowanne irin abu , da kuma cutar da take kama ƙwayoyin halitta na jini tana kashe su.

Bayan dogon bayanin da likitan yayi musu ya ɗora musu da bayani kan matakin da cutar ta kai ga idon na Falmata wanda rashin samun maganungunan da suka kamata a kuma lokacin da ya dace , ya kai ga ta rasa ganin ta na tsawon wasu shekaru  sakamakon mutuwa da wasu daga cikin jijiyoyin ƙwarar idon suka yi .

kai tsaye bazai yuwu ba ganin ta ya dawo kamar na sauran mutane masu lafiya , duk da cewa akwai yuwuwar kaso É—aya bisa uku na ganin nata ya dawo tare da taimakon magunguna da allurai zuwa kan aiki na musamman da za'a iya yi mata a idon idan har magunguna da alluran basu taimaka yadda yakamata ba , wanda zai É—ora ta akai da zarar ya kammala binciken sa a yau .

Cigaba yayi da yi musu bayani har zuwa lokacin da ya tabbatar sun samu gamsuwa sun kuma fahimci duk bayanan da yayi musu ,

da kan shi ya jaa jinin Falmata ya fita da shi zuwa É—akin gwaji saboda ya auna ya san irin magunguna da alluran da suka dace yayi mata bisa ga mataki na farko .

Basu bar asibitin ba sai da aka mata allurai biyu ta babbar jijiyar hannun ta tare da yi mata É—aya a jijiyar da take daf da idonta na dama ,

Ba ƙaramar juriya ta nuna ba wajen tsayuwa da tayi cikin nutsuwa aka huda mata jikinta babu zilliya bare ihu da hatta shida kansa likitan sai da ta burge shi sanin da yayi allurar gefen idon tana da zafi  ,
       Ya dube ta bayan ya ƙare mata allurar gefen idon , 
" sorry It'll hurt but just for a few minutes .

   Gyaɗa kai tayi tana jin yadda idanun nata suka yi nawi ga wani irin yanayi marar daɗi da take ji a idon ,

" Baban Mama , ta ƙira sunan sa tana lalubar hannun sa ,

  Da sauri ya riƙo ta

" Na'am Fatima , sannu kina jin ciwou ? comment vous sentez-vous en général ? ( How are you feeling overall ? )
"  Idona yayi jini ne ?
"bai yi jini ba Fatima , sannu  .
  

****

Misalin ƙarfe tara na dare suka bar asibitin bayan sun ci abinci sama-sama daga kitchen ɗin cikin asibiti .

Suka yi bankwana da likita omer bisa ga yarjejeniyar sake dawowa asibitin nan da kwanaki huɗu masu zuwa , bayan ya haɗasu da mugunguna ɗore da dokoki da sharuɗɗan da ya gindaya musu  .

Baki É—ayan su sun gaji Mama tayi bacci a jikin Babanta , Falmata kuwa tsukun da idanunta ke yi yana damunta wanda yake ta zubar hawaye , gaba É—aya bata jin daÉ—in kome ,

damuwarta ta tayar da Hankalin Youssouf da yake amfani da kalmomin rarrashi iri-iri yana jera mata sannu , har suka dawo gida , kai tsaye ya zarce da mama ɗakin baccin su ya kwantar da ita ya lulluɓa mata bargo tare da kunna hutar ɗumama daki ya fito falo inda ya tarar da Falmata ta rufe fuskarta da hannu biyu , ta jingina kanta da jikin kujerar da take

A sanyaye ya ƙaraso wajen fuskar sa na nuna damuwa ƙarara  ,

Zama yayi a kusa da ita jikin sa na gogar nata , ya kai hannu a hankali ya sauke hannun ta daga fuskar ,

Hawayen da idanun ke yi ya goge da hankicif É—in da ya zaro a aljihunsa ,

"Fatima yaya ne ? Ciwo ne har yanzou ? Kou zamou koma ga doctorat ?

" Baban Mama idanuna ciwo suke kamar zasu fita , idona bai taɓa ciwo haka ba , bazan warke ba kar kayi asarar kuɗi dayawa , lafiyar Mama yafi samun lafiyar idona muhimmanci kuma ..

"  Shittt , yace yana kai hannun sa kan ɗan bakin ta .
  " Fatima baki ji abounda Doctorat ya faɗi ba ? Zaki warke ko ba du ba , waye ya faɗi miki zata zam asara doumun nayi jinyar ki daga jakka ta ?

" kiyi ta addu'a Allah shi sa a cimma nasara bissa ga neman lafiyar ki kin ji kou  ?

Shiru tayi , ita ganin zancen likitan take soki-burutsu tayaya idanun ta zasu fara gani ? Bayan a iya sanin ta bata taɓa ganin hasken duniya ba .

Muryar sa ta katse tunaninta "

Kou baki so watarana ki ga fuskar mijinki ? Kou baki so watarana ki ga fuskar É—iyar ki Mama tare da 'É—iyan da zaki haifa nan gaba ?

Jin ya sosa mata inda ke yi mata ƙaiƙayi sai ta ɗago kanta , '

" inaso , amma nafi son na samu ɗa domin ya sadauƙar da ɓargon sa ga Mama , ta warke kamar yadda likita ya faɗa ,

  Sai yayi shiru yana kallon ta da taimakon hasken da bai cika yawa ba da ya hasko daga jikin ƙwan fitilan dake ajiye saman teburin gaban su ,

zancen ta ya zo masa a bazata , ya ratsa ƙwaƙwalwar sa a jirkitatcen yanayi da ya kasa tantancewa .

Ita ma shiru tayi cike da fargabar kasassaɓar da tayi , kada dai tayi masa laifi ? Ko dai zantukanta basu dace ba ? Tayi masa tsaurin ido ko ?

Sauƙar hannun sa cikin nata ya katse mata tunanin zucin da take yi  ,
Chapter 161 · 0% Book details