Sashe 71
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da jaan ƙafa ta ƙarasa bakin gadon ta hau ta zauna ,"
  Kallon ta likitan yayi lokacin da yake jona na'urar da jikin babban tv da yake kafe a gefe ,"
  Amarya gyarawa zaki yi ki kwanta mai kyau ki miƙe kafafun ki ,"
  A ɗarare tayi yadda ya umarce ta tana mai sake gyara rigar jikin ta da kyau ,"
  Da ido doctor ya yi wa hamza alama akan ya mata bayani yadda zata gane ,"
    Ki ɗaga rigar ki , ki buɗe cikin ki hoton jariri za'a yi ta haka za'a gane lafiyar sa ," ya furta hakan yana mai maida ganin sa ga fuskar wayar sa ,"
  Hoton jariri??
Ai kuwa zata so ta ga hoton abun da yake cikin nata ," wataƙila yayi kama sosai da baban sa ? ," tuno da hakan da tayi ya sa wani siririn murmushi ya bayyana kan fuskar ta ,
  ta tashi tsaye ta tattara doguwar rigar ta , dogon wondon da ta sa ta ciki ya bayyana ,"
   Cikin nutsuwa ya fara mata scanning É—in , yayin da shi da dakta hamza suka maida hankalin su baki É—aya ga fuskar tv lokacin da Æ´ar jaririyar da take cikin mahaifiyar ta ta bayyana tana ta hidimar ta hankali kwance, a yau tana da sati goma sha tara da kwanaki biyar , "komen ta yana lafiya Æ™alau a yanayin da ya dace ,hasashen ranar haihuwar ta ya nuna biyar ga watan goma ," nan da watanni huÉ—u da Æ´an kwanaki kenan ,"Â
   Wow what a beautiful busy baby girl , ? See those wee fingers are very close to the mouth,!
  Doctor ya karasa zancen da ƴar dariya a fuskar sa yana mai maida duban sa ga fuskar doctor hamza ,"wanda shima ya ga wutsilliyar da ƴar jaririyar take da hannuwan ta,"wani abu yaji ya taɓa ran sa , fuskar sa kadaran-kadahan yace ,"
  Yeah the baby looking super comfy and growing perfectly ,
ya furta hakan yana mai jefa kallon sa ga yakaka wacce ko kalma guda bata gane ba cikin Æ´ar gajeruwar mahawar da suka yi , sai faman raba ido take tana daga kwance ,
Congratulations once again Mr and Mrs Hamza Mustapha Dilmari
Likitan ya furta haka tare da miƙawa doctor hamza hannu suka yi musabaha , dai-dai lokacin da suka tashi domin tafiya , bayan da likitan ya kammala shigar da duk wasu bayanan da ya tattara akan yakaka da abun da yaje cikin ta zuwa cikin computer Ya aika da shi ainahin wurin wanda zasu cigaba da yi mata anti-natal , bayan ya duba duk wasu gwaje-gwajen da ya yi mata , yaga bata tare da wata babbar matsala ," nan ya miƙa musu takaddar magungunan da ya kamata ta dunga sha tare da wani ɗan kati wanda da shi zata dunga amfani wurin zuwa awo ,"
  Har sun yi taku biyu , yakaka ta tsaya tare da juyowa ta fuskanci likitan , bayan ta sauke idanun ta ƙasa tace ,"
   Likita toh ina hoton jaririn da ka ɗauka ?
      Ta furta hakan tana mai jin ƙwalla na cika idanun ta domin ta so ƙwarai ta ga jaririn , sai kuma ta ga har zasu tafi bata ga hoton na sa ba ,
  Tiris likitan yayi yana duban ta , domin shi a idanun sa bai ga alamun ƙyauyanci har haka a tare da ita ba ,
  Wani takaici ne ya rufe hamza , shi dai gidadancin yakaka na ci masa tuwo a ƙwarya ,"
     Lokacin da ake hoton ina hankalin ki yake ?? Wuce mu tafi gaba idan mun sake zuwa kya ga hoton , ya furta hakan yana mai kokarin danne ɓacin ran sa akan tsantsar son cikin da yake hangowa cikin idanun yakaka ,
   Waye uban cikin ?tabbas yawan soyayyar ɗa wurin uwar sa tana da alaƙa da son da take yiwa mahaifin sa ,"
  Bayan sun kama hanyar komawa gida yakaka ta katse shirun da suka yi da faɗin ,"
  Inaso na je bakin kasuwa na ɗauko kayan mu da suke shagon da muke kwana a bakin sa ,"
  Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba saboda zuciyar sa da take ta kai kawo akan son sanin ko yarinyar tana da wata alaƙa da uban cikin jikin ta ,? ko zaton sa ba gaskiya bane , ? ko dai da amincewar ta ta bada kan ta ga wani ƙato ??
   Babu buƙatar ki ɗauko kayan , ki bar su kawai zan saya muku wasu nan gaba !
   Ta bar kayan ? Yana nufin rabuwar ta da duk wani abu da ya shafi bature kam silum ɗin ta ,!' bata jin zata iya ,'domin kome da ya shafe sa abun so da ƙauna ne a wurin ta , baya ga haka kuma ba ƙaramin taimakawa suke wurin ɗebe mata kewar sa da ke cin zuciyar ta a kullum ba ,
 Ni dai Dan Allah ka kai ni na ɗauko , akwai abu masu muhimmanci a cikin jaka ta,"
  Duban sa ya mayar kan ta
 Abu masu muhimanci , meye su ?
Agogon sa da hoton sa ta amsa masa kai tsaye babu ƙunbiya-ƙunbiya ,!
  Gangarawa yayi gefen titi ya tsaya , tare da maida hankalin sa baki ɗaya kan ta ,"
  Agogo da hoton wa ??
 Ya jefa mata tambayar yana mai tsare ta da idanu ,"
  Ɗago da kan ta tayi tana kallon tsakiyar idanun sa , ƙwarai yayi mata kwarjini kuma tun farko shi ɗin bai taɓa zuwa mata da sigar wasa ba , uwa uba zuwa yanzu ta san cewa abun da suka aikata da bature kam silum har ta kai ga samun ciki ba abu ne mai kyau ba , dan haka ya zama dole ta koyi boye ainahin yadda kome ya faru da dangantakar ta da shi ,"
  Da inda-inda tace masa
Hoton baa-baban mu ne da agogon sa ,
  Tsai yayi yana kallon cikin ƙwarar idanun ta a koƙarin sa na son gano gaskiyar ta ,"
  Dan Allah ka kai ni
Ta sake yi masa magiya tana marairaicewa,"
  Ɗauke kan sa yayi tare da tada motar , sashi guda na ran sa na tabbatar masa da bata da wayo da wayewar kan da zata iya masa ƙarya , sam alamun ta bai yi kama da na wacce zata iya lanƙwasa zance ta sauya masa launi ba ,"
A dai-dai ƙofar shagon ya tsaida motar ƙarkashin umarnin ta da tace masa nan ne shagon ,"
Ba ƙaramin farin ciki abuwar mai shago yayi ba da ganin yakaka cikin ƙoshin lafiya , ya ɗora da tambayar ta falmata , domin labari ya isar masa na abun da ya same ta , ya kuma ga shaidar jini a bakin shagon sa washegarin ranar da abun ya faru ,
Ya shiga dumuwa sosai ta yadda yake ganin har da rashin taimakawar sa ya sa suka afkama masifa ," ga yadda suka samu labari falmata ta riga ta mutu , hakan ne ma ya sa bai ko je neman su asibiti ba ,"
Bayan gaisuwa tare da jajantawa yakaka ta buƙaci ya bata jakar baccon su , nan kuwa ya fiddo mata da su , suna nan yadda suka bar su , " a cewar sa yayi niyyar cigaba da ajiyer su domin ya san zata dawo ɗauka , nan dai suka rabu suna mutunta juna ,!
  Daga yanzu baza ku sake dawowa bakin kasuwa da sunan zaman kan ku ba ," idan ƙanwar ki ta samu sauƙi zan tafi da ku gidan mu ku zauna tare da su rahima , har zuwa ....
   sai kuma yayi shiru gami da juyowa ya dube ta , ta nutsu tana saurarar sa ,"
  maida duban sa yayi ga tukin kafin ya jefa mata tambaya
  ko baza ku bini gidan mu ?
  da sauri ta ɗago kan ta , ita kuwa da daman kullum da tunanin inda zasu samu mafaka bayan barin su asibitin take kwana take tashi ,Ta yaya zata ce baza su bi sa ba ? To ina zasu da ya wuce inda zai kai su ?? Babu !
   zamu bika yaya dakta , kuma mun gode Allah ya saka da alheri ya baka abun da kake so duniya da lahira , yadda ka taimaka mana kai ma Allah ya ɗaukaka ka ,!
 sosai kalaman ta suka burge shi tare da dadaɗa masa rai , a yadda yake mata ganin bagidajiya bai taɓa zaton ta iya kalamai masu nutsuwa haka ba ,"
  da murmushi a fuskar sa ya amsa a bayyane da ,
     Ameen Nurii .
Bayan sati biyu
Falmata ta warke ras kamar ba ita ake sallama daga gadon asibiti a yau ɗin ba , tayi ƴar ƙiba mul-mul , fatar ta mai ɗan haske ta sake washewa , fes da ita cikin jar doguwar rigar da yaya dakta ya saya mata , kafafun ta sanye cikin sabon farin silafa ɗan madina , ta ɗora ɗan bakin hijabi akan ta ,"
Duk wani abun da ake kafin a ba wa mutum sallama daga gadon asibiti doctor hamza ya gama yi inda likitocin ta suka buÆ™aci ta dawo bayan sati shidda su sake duba ta , "Â
Rahima ita ta taya su suka harhaɗa ƴan kayan su domin tafiya da su gida , sai dai da zuwan doctor hamza yace duk su bada bokitaye zuwa buta tabarma da sauran tarkacen kayan ciye-ciyen da basu riga sun cinye ba ga marasa lafiyan da ba'a riga an sallame su ba masu ƙaramin ƙarfi ,