Sashe 146
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙarfe baƙwai na dare suka fita a motar Samy baby dukkanin su sun ɗau kwalliyya ta gani a faɗa ,
Duk da fuskar Yakaka a tamke take da bayyanannen ɓacin rai hakan bai hana kyaun da tayi ratsowa ba , dai-dai tana karya kan motar ta fito kan titi sosai Samy baby ta dubi sashin Yakaka a kaikaice ,
  Yanzu ke Yaks meye haka ? Dan asara akan na hana ki saka wannan uban barigizan hijabin naki shine kike wannan ƙuncin ? Mts!
Ji wannan ƙatuwar jakar da kika ɗauko kamar wata wanzamiya na faɗa miki bata dace da ƙwalliyar nan ba , ƙwalliyar nan taki ba ta babbar jaka bace ta ƴar ƙaramar jakar hannu ce amma kin ƙi ji , ai daman ɗan ƙauye sai ya shekara hamsin a birni yake barin ƙauyenci da gidadanci , ke kika sani sautun mahaukaciya !
Ta danna motar da gudun gaske suka cilla kan titi cikin manyan unguwannin abuja da ko sau ɗaya Yakaka bata taɓa kai ƙafar ta bigiren ba tun zuwan ta garin .
Bata cewa samy ƙala ba illa sake rungume jakar ta da tayi wanda a ciki ta saka hijabinta da niƙab ɗin ta , ƙwaƙwalwar ta a hargitse take da sabon tsoron da yake mamayar ta ,
Ƙofar wani tafakeken gida samy baby ta tsaya tare da zaro wayar ta ta latsa lamba , bugu ɗaya ya ɗauka
Gamu mun iso tace tare da sauƙe wayar daga kunnen ta ,
ba'a yi mintuna uku ba sai maigadi ya buɗe musu ƙofar gidan , samy baby ta danna kan motar a hankali
shigar su gidan yazo dai-dai da ƙaruwar firgici a fuskar yakaka , saboda girman gidan da ya wuce hankalin ta ga fitulu da suke a watse birjik a harabar gidan haske ya wadata tamkar tsakar rana ,
Gefen wasu tsirarun motoci da basu wuce guda shida ba samy baby ta ajiye motar ta ,
Muje Yaks ,
A tsorace ta fito tana bin gidan da kallo , ba tare da samy baby ta kula ta ba tayi gaba , cikin jaan ƙafafu ta bita a baya maƙale da jakar ta , suka dumfari katafaren ginin da yake tsaye a gaban su ,
Babu yalwar mutane a babban ɗakin hutawar da suka shiga , mata da mazan da suke harkokin su a wajen babu wanda ya kula su ,
Samy baby ta jagorance su suka zauna , basu jima da zama ba aka murɗo ɗaya daga cikin ƙofofin da suke ta cikin falon aka shigo ,
Kamal ne ya shigo yana ɗan gama hanya ya ƙaraso tare da sakin jiki ya faɗa kan kujerar kusa da yakaka , rigijib !
a tsorace ta miƙe tana raba ido .
  Idanun sa da suka yi nawi saboda kayan mayen da ya ɗibga ya ɗaga ya watsa mata wani kallon ƙasƙanci ,
Ke wai ji mana , ya kike wani safurewa haka kina wani ƙoƙarin waskewa , ? Kamar baki da sanin cewa na biya kuɗin ki , zo nan na fara morar kuɗi na dallah
Ya miƙa hannu ya fisgota ta koma da ƙarfi ta zauna ,
Ganin sa ya mayar kan Samy baby
Yane to yawa kike fa, Zaman me kike ? Ko kina neman me tayi ne ? Nan duk suna da chicks ɗin su dan haka ki ƙara gaba ,..
Ke kuma zo muje ki fara tausa min gaɓɓai da waɗannan tausasan hannuwan naki tuɓus-tuɓus , wayyo laushi!
   Ya fisgi hannun Yakaka suka miƙe tsaye ,
Fuskar samy baby ta kalla , idanunsu suka gauraya cikin na juna ,
 Ga mamakin samy baby ba kamar yadda ta zaci zata ga hawaye a idanun yakaka ba , saɓanin ta idanun ta a bushe suke ƙyamas ,ɗauke da wani irin yanayi wanda yayi tasiri ƙwarai wajen rage mata kuzarin tashi ta bar gurin kamar yadda aka mata umarni ,
Kallon da yakaka take mata kallo ne me kaifi da yake É—auke da fasasarori da dama ,wanda ta gaza É—aukar masa fassara guda ,Â
tana ganin lokacin da ta fisge hannun ta daga cikin na kamal ɗin ta nufi ƙofar da ta ga ya nufa da ita , ba tare da ta sake waiwayowa gare ta ba ,
A sanyaye ta miƙe cikin ran ta tana harhaɗa kalmomin da zata yi amfani da su wajen kalmaso kan yakaka ta rarrashe ta kamar yadda ta saba yi mata a duk lokacin da tayi mata wani gagarumin laifi ,
gefe guda tana tunanin ware wani kaso me ɗan tsoka daga cikin kuɗin da kamal ɗin ya bata ta danƙa mata su duk domin su taimaka wajen shawo kan ta cikin sauki.
 Da wannan tunanin ta faɗa motar ta bar gidan tana duban agogon hannun ta da yake nuna ƙarfe tara saura ƴan mintoci , sama ta haskaka da hadarin da yake haɗuwa da ke nuni da koyaushe cikin dare ruwa zai iya sauƙa .
Kar ka kuskura ka sake taɓani ,
Ta ce da shi lokacin da take samun wajen zama bisa kan kujerar gaban tafkeken gadon É—akin na alfarma .
 Wata dariya ya kwashe da ita yayi sufa ya faɗa gadon rubda ciki .
  Kai yarinyar nan salon ki na burge ni , wat....
  Zan sha BURKUTU ,
Ya tsinkayi muryar ta ta katse masa kalaman sa , waigowa yayi yana daga kwance ya dube ta , fuskar sa na bayyana mamaki yace :
Burkutu ?
Eh
tace da shi tana tsattsare shi da idanun ta ,
Ni bana shan giyar gargajiya ,"blue moon ," ita ce giyar da nafi ƙauna , yanzu ma ita na sha ƴar kaɗan , kin san tana da ƙarfi shegiyar giya ce , ko za ki iya sha na zubo miki kaɗan ki taɓa irin ta ?
Kawo min
ta ce da shi a taikaice .
Miƙewa yayi ya fita
Yana fita ta miƙe tsaye ta shiga kai kawo a ɗakin tana yarfe hannu , da tayi zaton zata iya , a zaton ta tana da ƙarfin zuciya , ya kome yake shirin kufce mata ? Me zai faru da ita idan har shirin ta bai tafi dai-dai ba , ??
 Jin motsin taɓa ƙofar ya sa tayi saurin komawa ta zauna ,
Ya shigo hannun sa ɗaya riƙe da kwalbar giyar blue moon ɗaya kuma kofin gilashi da ya zubo ƴar ƙanƙara a ciki ,
Zuba giyar yayi ƴar madaidaiciya ya miƙa mata ,
 Idanun ta na duba ƙasa ta ce da shi ka fara sha ,
Jim yayi riƙe da kofin sai kuma ya kai bakin sa ya ɗan kurɓa ,
Ya Sake miƙa mata ,
Ka cika min taf
Tace da shi ba tare da ta bari sun haÉ—a ido ba ,
Keeeee hahaha , wannan fa blue moon ce ba'a mata haÉ—ama yanzu nan za ki ji ki warwas kin gaza motsi, ba ta wasa bace wannan , ke kin san kuÉ—in ta kuwa ? Yafi jarin baban ki .
Bana shan wannan , warin ta bai min daɗi ba ka kawo min wata idan akwai , nafi son wacce zata ƙara min kuzari ,
 Æata rai yayi ! ya tsaya kallon ta sai kuma ya kwashe da wata dariyar sakarci ,
Tunda ta ƙara kuzari kike nema bari na kawo miki Amstel kina shanta yau ji za kiyi kamar an miki allurar da ake yiwa dawakai ,
  Ya ƙarasa zancen yana kafa kai ya sha fiye da rabin wacce ya zuba a kofin ya ajiye sauran ya fita yana gama hanya tare da jaan wani siririn fito irin na wanda duniya ta yiwa daɗi .
Yana fita ta miƙe tare da murɗa ƙofar ta fito , ɗan yawatawa tayi da idanun ta cikin daƙiƙoƙi ta fahimci ɗaukewar ƙafar da ya ƙaru a wajen domin mutum ɗaya ta hango a zaune ya tasa kwalaban giya a gaban sa ,
Da sassarfar da take harɗe kafafun ta ta taka tana nufar ƙofar ficewa daga wajen bakin ta ɗauke da addu'o'i iri-iri ,
  Siit ji mana , ?
Numfashin ta ya nemi siƙewa da jin muryar wani yana dakatar da ita , bata juya ba sai ma ƙaimi da ta ƙara ba tare da ta bari ta ƙarasa jikin ƙofar ba ta miƙe hannuwan ta duk biyu ta tura ƙofar , ta jefa ƙafar ta waje .
Tana jin sa yana sake sanar da ita ba fa nan kamal É—in yake ba ,
Ba ta saurare shi ba , ta kara da saurin da yafi kusa da gudu tana keta farfajiyar gidan ta nufi ƙofar da suka shigo gidan ,
Ƴar ƙaramar kofar da take maƙale da babbar ƙofar gidan ta nufa kai tsaye ta tura ta , cikin sa'a ƙofar ta buɗu da gudun gaske ta ƙarasa ficewa daga gidan ,
Tsawa tare da rugugin hadari da ya karaɗe sararin sama bai toshe mata kunne daga barin jin tashin muryar kamal ba , hakan ya sa a diririce ta tura ƙaramar ƙofar gidan da yake daura da ita ta faɗa ,
Ga babbar sa'ar ta babu kowa a harabar ɗan madaidaicin gidan me tsari , dan haka cikin sauri ta cire hijabin ta daga cikin jakar ta ta zira akan kayan ta , ta sake zaro niƙabin ta ta fara ƙoƙarin ɗaurawa ,
Gurnanin da ta ji daga gefen ta kaɗan shi yasa zuciyar ta dokawa da ƙarfi , tare da taimakon hasken ƙwan lantarkin ta waiga da sauri idanun ta suka shiga cikin na wani ƙosasshen kare da yake kwance daga gefe kusa da ita ,
ÆurÉ“ushin tsoron daga Æ™asan ran ta ya fara toroÆ™o kafin baki É—ayan jikin ta ya É—auki rawa ,
Cikin abunda yake gaza da minti guda ta juya da gudun gaske ta fita a gidan tana banko ƙofar , karen kuwa bai jinkirta ba ya rufa mata baya da ƙaƙƙarfan haushin sa , suka zuba ƴar tsare akan titin da yake shal babu kowa saboda dare da ya fara yi ƙarfe goma saura , haɗi da garin da yake gangame da hadari .