Sashe 111
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tace da shi cikin ƴar ƙaramar muryar ta ,
  ,'Bata iya buɗe ƙofa ba ? Ya tambayi kan sa ,"
 Hajiya batta cikin ɗakin ??
 Tana sallah ,
   ta ce masa
 Bai ce kome ba ya gyara tsayuwa gami da jingina da jikin bangon ɗakin ,
  Cigaba tayi da tsayuwa tana ɗan laluba jikin ƙofar ko zata ji wajen buɗewa ,
  Ba'a ɗauki lokaci ba hajja ta idar da sallah ,
  Ke kam wannan yarinya anyi bagidajiya , yanzu ace buɗe ƙofa ma kin kasa ? Ni gusa ki ban guri ,
 buɗe masa ƙofar tayi ya shigo suka gaisa ,
  Hajja akwai abunda kuke buƙata ne ?
  Babu abunda muke buƙata ɗan nan , mun gode ƙwarai da hidima ,
  Idon sa ya ɗora kan baby mama ,
 Â
Ta daina rigimou kou ? Ba ku buƙatar kome kou ?
Shiru falmata tayi domin bata ma san da ita yake ba ,
Hajja ta ce
fatima maigidan na magana
 Â
  Wanne maigida hajja ??
Wata ƙatuwar harara hajja ta wurga mata , tamkar falmatan tana ganin ta a ƙufule tace
  Baban jaririyar ta ki
A sanyaye ta ce me yace ? Wai zai tafi da baby ?
 Da sauri youssouf yace
Ban faɗi hakka ba fatima cewa nayi ba ku buƙatar kome ?
Eh !
  Ta bashi amsa tana zama bakin gado ta shiga laluben baby mama, hannun ta ya sauka bisa kan ta ta shiga shafawa a hankali ,
Ya juya ga hajja , ni zan shiga gari wajen aiki na , akwai yiwuwar gobe sai yammaci zan shigo , duk idan kun buƙaci wanni abu ku ƙira ma'aikatan otel ɗin ta kan wayar tarho ,
 Ga ta nan ,"
ya nuna mata telphone ɗin dake ajiye daga saman ƴar durowar gefen gado "
madallah hajiya ina sake godiya
Mune da godiya ai É—an nan mune da godiya , to to babu kome Allah shi taimaka muna nan muna addu'a
Ameen hajja sai gobe
  Ya juya yana barin ɗakin
Da sauri hajja ta zunguri falmata ,
  Ke baki san ki gaishe da miji ko kiyiwa miji addu'a bane ? yau ni hauwa'u na ga abunda ya fi ƙarfi na me zan gani haka ? Yanzu ashe haka za ki dunga gwada rashin hankali a gidan auren na ki ? Ko kuwa taƙamar yarinta kike ? To bari ki ji na faɗa miki ni lokacin da aka min auren fari ma ban kai ki cika ba , kin fini ƙugu da ƙirji da sharaɓa da kome ke har shekaru ma domin ni lokacin da aka min aure ma sha huɗu nake ko nonon arziƙi bani da su , amma billahil azeem ban yi irin wannan haukar da na hango somi-somin ta a tare da ke ba ,
  Ke kenan sai ƙwalafacin ƴa , alhalin kina gwadawa uban ta halin ko in kula , idan taƙamar ki son ƴaƴa ai sai ki kwantar da kai kema ki samu ki tara naki ba ki dunga gwada naci akan ƴar wasu ba ,
  Falmata wacce ta fara jin haushin hajja akan takurar da ta ke mata, muryar ta a cunkushe tace ,
 To a ta ya zan tara nawa ƴaƴan ??
  Sororo hajja tayi ,
 Ah lalle abun naki na yi ne, 'an biyawa bazaura hajji , to sai ki cigaba da tambaya ta , ranar bada amsa tana zuwa , aikin banza yarinya sai sokonci kika iya ,.
 Â
Washegari biyamuradi youssouf bashi zaune bashh&
har sai da ya samu wani É—an madai-daicin gida irin wanda yake so a unguwar ,(Banifandou 2) ya kamawa su falmata hayar sa ya biya kuÉ—in shekara guda cif ,
Ƙarfe hudu tayi masa a shahararren company ƙera kayan katako da shirya gida ,(sunwe) inda ya faɗa musu buƙatar sa na son a kai masa kaya dai-dai da tsari da fasalin gidan sa ,
Basu yi ƙasa a guiwa ba suka tashi ma'aikatan su har su huɗu suka je ganin gidan ,
Hotunan gadaje , kujeru da sauran kayan adon gida aka dunga nuna masa tare da kuÉ—aÉ—en su ,
Bai yi zari ba ya zabi dai-dai kudin sa , tare da matsayin Falmata a wajen sa ,
Ma'aikatan da kan su suka kwashi kayan a motar su zuwa gidan inda gobe zasu je su shirya kayan da safe ,
Sai sha biyun dare Youssouf ya koma hotel ɗin saboda tun ƙarfe takwas na dare yana tare da manyan su suna wata ganawa ta musamman da lieutenant-Gènèral da Major Général , waɗanda sune ƙashin bayan samun ɗaukakar sa a fannin aiki ,
Ya so ya je ya ga ɗiyar sa da yadda suka wuni amma ganin yadda dare ya riga yayi sai ya yi wucewar ɗakin sa kai tsaye , da zummar gobe zai gana da su cikin rashin sanin sa yini baby mama tayi da matsanancin zazzabi tare da mura , banda kuka babu abunda take , tun falmata na rarrashi ita kaɗai har hajja ma ta karɓa , duk da haka ta ƙi shiru , zuwa dare har shiɗewa take gaba ɗaya hankalin su ya gama tashi banda kuka babu abunda falmata take ko abinci sun gagara ci ,
Ganin duhu ya sawo kai ga youssouf bai zo ba ya sa hajja me wurya fitowa daga É—akin ba tare da ta san takamaimai ina zata nufa ba , Allah ya taikaita mata wahala ya gama ta da É—aya daga cikin ma'aikatan otel É—in da ya kawo musu abincin rana ,
Nan ta tsaida shi ta tambaye shi ina ne ɗakin wanda ya kawo su ? Suna buƙatar taimakon sa , bai gane inda ta dosa a maganar ta ba saboda haka ya yi mata jagora zuwa gun manyan su , inda cikin kwatancen hajja me wurya tare da duba sunan ainahin wanda ya kama musu ɗakin da suke suka fahimci colonel youssouf take nema ,
basu da number wayar sa dan haka suka shiga ƙiran layin telfo na ɗakin sa nan ma basu ci nasara ba domin wayar tana ta ƙara ba'a ɗauka alamun da ke bayyana babu mutum a ɗakin .
Ganin yadda hajja ta damu tare da sanin matsayin wanda ya kawo su ya sa suka tambaye ta matsalar su ?
Nan ta shaida musu Æ´ar shi wanda ya kawo sun ne jaririya bata da lafiya suna neman a kai ta asibiti ,
Nan take ma'aikatan hotel É—in suka jagorance su zuwa wani asibiti me zaman kan sa mafi kusa duba da halin da Æ´ar jaririyar take ciki na wahalar numfashi,
bayan sun haɗa su da likitoci da nan take suka karɓi baby mama suka fara bata taimakon da ya dace ,
Sai suka dawo suka cigaba da ƙiran layin ɗakin youssouf lokaci-lokaci ko ya dawo ?
Dan haka da shigar sa ɗakin bai rufa mintoci goma ba fitowar sa daga wanka kenan , kan wayar ɗakin ta fara ƙara ,
Nan ya É—auka bayan sun gaisa suka sanar da shi halin da Æ´ar sa ke ciki tare da asibitin da suka kai ta ,
A gigice youssouf ya sanya kayan sa gami da ɗaukar ɗan mukullin motar sa , kai tsaye ya tasamma asibitin da ba baƙon sa bane domin fitatcen asibiti ne da duk ƙasar aka san sunan sa ,!
Bai wani sha wahala ba illa tashin hankalin da yake ciki lokacin da ya samu ganin babban likitan da aka tabbatar masa shi ya kula da jaririyar a daren ,
A kiɗime youssouf ke tambayar sa ina ƴar ta sa take ? Kuma a wanne hali take ciki ? Nan likitan ya kwantar masa da hankali inda ya shiga yi masa bayanin abunda ke damun ƴar sa tana da ,( single pneumonia ) wanda kuma shi ya kawo mata wannan wahalar numfashin tare da zazzaɓi me tsanani , sanadin shaƙar ƙura me ɗauke da ƙwayoyin cuta da tayi,
Dan haka likitan yayi ƙira da a kiyaye sosai a kula da ita , a ƙarshe ya sanar da shi an shawo kan matsalar ta a halin yanzu har ma ta samu bacci zuwa gobe idan aka ga yanayin jikin ta ana iya sallamar ta ,
Tare da likitan suka nufi É—akin da aka kwantar da baby mama É—aki ne na musamman ( side room ) inda falmata da hajja suke tare da ita ,
Lokacin ƙarfe ɗaya saura na dare dan haka nuna masa ɗakin ya yi , ya juya ,
A hankali ya murɗa kofar ɗakin ya shiga , da haske wal a ɗakin dan haka ya hango falmata daga kan gadon tana zaune ta jingina bayan ta da jikin ƙarfen gadon tana riƙe da baby mama a hannun ta , ga alama bacci take ,
Hajja kuwa tana kwance akan Æ´ar shimfiÉ—ar da ma'aikatan asibitin suka bata sai sharar bacci take saboda gajiya da tayi da kuma jikin girma !
A hankali ya tako cikin ɗakin ya ƙarasa bakin gaɗon gami da rage tsawo ya leƙa fuskar baby mama , ya yi haka ne saboda baya son tashin su a bacci,
Falmata kuwa tun taɓa ƙofar da yayi ta ji sa , hasalima ba nisa baccin na ta yayi ba saboda sam yanayin wajen da yayi shiru sosai yana bata tsoro , tun tana ƙiran sunan hajja lokaci zuwa lokaci tana amsa mata har dai ta ji hajjan tana mitar ta dame ta da ƙira cikin magagin bacci dan haka ta haƙura ta ƙyale ta , Tayi shiru tana sauraran sauƙar numfashin baby mama da take yin sa cikin nutsuwa alamun sauƙi ya samu gare ta ,
Hannun sa ya kai a hankali da nufin ƙara rufe jikin baby mama da ya ɗan buɗu kaɗan ba tare da sanin falmata ba ,