← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 269

Sashe 54

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta warware É—ayar bacco ta buÉ—e ciki ,
Ta fiddo kuɗaɗen ta tare da agogon da ya bata ta saka kuɗin a cikin bacco , ta riƙe agogon a hannun ta , ta tsura masa ido , " kyakyawar fuskar sa tana mata yawo a zuci , ƙamshin da yake manne da jikin agogon ya mamaye mata hanci , ta ji wani irin nishaɗi tare da shauƙi suna huda ta, ina ma ina ma da ace har yanzu suna tare tana kallon sa tare da shaƙar ƙamshin sa ? , a hankali ta kai agogon hancin ta ta sunsuna gami da rufe idanun ta , shi ma'abocin ƙamshi ne kome da ya dangance shi ƙamshi yake hatta kuɗaɗen da ya bata ƙamshin sa suke ," a hankali laɓɓan ta suka motsa cikin yaren ta tace,"Bature kam silum ," ( baturen baƙaƙen fata ,)

Motsin da ta ji yana nufo É—akin ya sa tayi saurin ajiye agogon a gefen kuÉ—in ta fara jera kayan ta bisan su ,"

******************
Iya adadin nisan da yake yi da yarinyar iya adadin daɗuwar rikicin da yake ji cikin zuciyar sa tare da gangar jikin sa baki ɗaya ji yayi masifar da yake zaton ta ƙare tana sake taso masa ,'

Addu'o'i ya shiga yi iri-iri idan ya kama wannan ya gama ya kamo wancen ,

Ga mamakin sa kamar sake ƙaruwa lamarin yake domin zuwa yanzu karfi da yaji yake jin ana son sarrafa gangar jikin sa ya juya kan motar ya koma wurin ta , kamar yadda zuciyar sa ta riga tayi tsalla ta koma gare ta , "

Karfin addu'ar da yake yi ita ta duƙushe tasirin ko ma menene , har ya samu ya kawo inda suka yi masauki a bakin dajin ,

Bai kula kowa ba duk kuwa da gaisuwar ban girman da suke yi masa ta hanyar ƙamewa su sara masa ,

Kai tsaye ya shiga bayin sa ya É—auro alwala , ya dawo cikin tantin sa ya sauke farillar sallar asubha da take kan sa ,

Yana idarwa baiyi ƙasa a guiwa ba ya ɗauko alqur'anin sa ya buɗe murya cikin nutsuwa ya fara tilawa ,

A hankali nutsuwa tare da amincin da suke tare da alqur'ani suka fara ratsa shi tare da yin tasiri ga wannan yanayin da yake tunzura shi ,'

Jingina kan sa yayi da jikin karfen tantin nasa lokacin da yaji wani irin bacci mai nawi yana son fusgar sa ,'

Ƙiran wayar sa shi yasa shi buɗe idon sa daga son yin bacci da yake ,'

Ami Tafeêdah

Shine sunan da ya bayyana à fuskar wayar ! 

Da rashin kuzari biyamuradi ya amsawa tafeedah sallamar sa, bayan nan suka É—ora da tambayar lafiyar juna ," ?

  Ɗan ouwa da dama kou ? meke damun ka ? lalle cikin yanayin ka akwai damouwa yi gaogawar sanar da ni ?

Shiru youssouf yayi , yasan tafeedah yayi masa farin sani , yana kuma iya karantar kowanne irin yanayi yake ciki ," to amma baya jin zai iya faɗa masa damuwar sa, toh yace me wai ??   Ya sake dulmiyewa cikin alfasha bayan wanda tafeedan ya san yana aikatawa, ya ƙara da wata ??

   Ɗan ouwa bani jin daɗin jiki na ne kawai , ciwon kai na damu na ,!

  Babu kome ka ɗaure abokina idan har ka cigaba da ƙaurace mata a hankali ahankali duk wasu yanayi masu wuya da kake shiga idan baka sha ba zaka ji ka daina jin yanayin , sannan ka sake dagewa da addu'a .

Uhum

ita ce kawai kalmar da youssouf ya furta
   
Da ace tafeedah ya san abun da ya aikata da babu abun da zai hana abotar su ta samu tangarÉ—a

Nagode ! Cewar youssouf

Daga haka suka ɗan yi hira sama-sama , ganin youssouf ɗin bai tare da nutsuwar sa sosai ya sa suka yi sallama tare da sake ƙara masa ƙarfin guiwar gujewa burkutu !

Yadda youssouf ya ga rana haka ya ga daren yau ," tsafi gaskiyar mai yin sa ne ,"

Da ita yake son kasancewa a yanayi irin na daren jiya , rashin samuwar hakan a gareshi ya haifar masa da masifaffan ciwon ciki da amai bayan masifar da yake ji a ruhi da ƙwaƙwalwar sa , ji yake kamar ya zura da gudu yayi ta gudu har ya tadda ta , ko kuwa dai yayi fiffike ya sauka gare ta a cikin daren ,"

Shajaran majaran ya wayi garin a halin jikkata , da ya sanya tilas likitocin da suke abokanan aikin su suka shiga bashi taimakon gaggawa , ƙarin ruwa zuwa magunguna ,"

ba laifi lafiyar jikin sa a zahiri ta dai-daita amma shi kaÉ—ai ya san halin da yake ciki a ruhin sa ,

Zuwa azahar ya É—an ji karfin jikin sa , dan haka yayi wanka ya É—au shiri , zuciyar sa ta gama samun galaba akan sa tare da taimakon shaiÉ—anin da yake tare da shi yana bibiyar sa tare da ingiza shi ,

Karfe biyar na yammaci tayi masa dot a ƙofar su yakaka ,'

Kan sa tsaye ya shiga gidan yana mai fatan cin karo da ita kawai su tafi , sai dai kuma inda gizo ke saƙar shine , shi fa bai wani tantance da kamannin yarinyar nan ba ," alhali kuma ya gama shawartar kan sa akan ya tsaya tare da ita kawai ta dunga biya masa buƙatar sa tun da shi ne mutum na farko da ya fara sanin ta ," shi kuma zai ɗauki duk wasu hidindimun ta har sai zuwa lokacin da ya fita a masifar da ya faɗa ,'

Da wannan tunanin ya sanya kai cikin rumfar madam saly , ya tadda babu mutane dayawa mafi yawa suna wurin chasun da ya gitta a yayin shigowa ,"

Wuri ya samu daga gefe ya zauna , zuciyar sa na fatan ganin ta kamar yadda yake yawata idanun sa akan Æ´an matan da ke kai kawo ta gaban sa , baki É—aya bai ga fuskar ta ba acikin su ,

Ina take ?

Ya san fara ce tas , bayan haka babu abun da zai É—orar na daga suffar ta ,'

Yagana ce ta ratso ta cikin rumfar cikin shirin tafiya gida, yakaka biye da ita da nufin yi mata rakiya ta dawo ta ƙarasa aiyukan da take kaiwa har dare tana yin su daga wannan zuwa wancen !

Tana sanyo kai ta ji ƙamshin sa ,' tabbas wannan ƙamshin "bature kam silum " ne , a take bugun zuciyar ta ya sauya tare da wata kewar sa mai tsanani da ta taso mata

Ina yake !  Tambayar zuciyar ta

Tun da suka bullo ya gan su , a take zuciyar sa ta shaida ta tabbas ita ce abar kwaÉ—ayin sa ita ya zo nema ,!

Hankalin ta ya rabu biyu É—aya yana ga hirar da yagana ke yi mata É—aya yana ga son gano inda yake , dan haka bata samu nasarar ganin sa ba har suka zo giftawa ta gefen sa ,"

Ganin zata wuce shi ya sa shi miƙa hannu ya kamo hannun ta ,"

Da sauri ta juyo domin ganin waye ne ,"duk da cewa an saba yi mata haka ,"

Idanun su suka sarƙe cikin na juna kowannen su ya gaza ɗauke idanun sa , a yayin da suke fassara kallon da suke yiwa juna a zuciyoyin su ,"

Kallon da yakaka ke bin biyamuradi kallo ne na nayi kewar ka , na kuma yi farin cikin sake ganin ka ,

Yayin da take fassara kallon da biyamuradi yake jifan ta da shi a nufin.!
   Gani na dawo ki sake taimaka min .,'
    Zan taimaka maka ta ƙudurce cikin ran ta ,!

  Har yagana tayi ɗan nisa ta waiwaya bata ga yakaka ba dan haka ta dawo da baya

nan ta tadda ta suna kallon juna da wani mutum da bata kai ga sanin sa ba , da ido ta bi hannayen su da yake manne ,!

Dafa kafaÉ—ar yakakan tayi ganin irin shagalar da tayi ,bata san ma ta zo wurin ba

Da sauri yakaka ta zame hannun ta daga cikin na biyamurdi ," Ina zuwa ,' tace da shi !

A bakin kofar shigowa ainahin gidan ta dogare
yagana  zan koma daga nan kin ga ana jira na !

Da ido yagana take bin ta cikin ranta tana mamakin farin ciki tare da murnar da yakaka take yi wanda kafin fitowar su a É—azu babu shi,'

A karo na huÉ—u ta sake tambayar ta

Wai yakaka sai tambayar ki nake kin share ni waye wannan É—in ko Æ´an uwan ku ne ?

Bature kam silum ne ,
   Ɗan uwan mu ne

Daga haka ta juya da sauri har tana haÉ—awa da É—an gudu ta koma ciki ,

Ta bar yagana da mamakin ta fal cikin rai ,
" bature kam silum' ta maimata sunan ,!
sashi guda na zuciyar ta yana shakkun ambaton sa da tayi da É—an uwan ta , kai wannan daga gani ba yaren mu bane !

Da murmushi akan fuskar ta ta ƙaraso gaban sa ,

  Ki kimtsa ki taho mu tafi ,kadda ki ɗau lokaci

Ya furta hakan yana mai É—auke kan sa daga kallon ta ya mayar ga agogon hannun sa ,"

Kalmar kimtsawa tai mata tsauri wurin fahimta , amma da yake tana jin sa cikin zuciyar ta , sai ta kintata ta  hasaso abun da yake nufi , dan haka ta shige ciki ,"

    Ƙasa-ƙasa ya bi takun kafafu da kallo wanda yake halin sa ne kallon ƙasan ido ,"
        nan ya hango dauɗa tare da taron kursashin da yake danƙare ƙasan kafafun ta . Cikin sauri ya ɗauke kan sa !

A gurguje ta shiga ta É—ibi ruwa tayo wanka , ta dawo É—akin su larki ta hau shiri ," falmata wacce take zaune shiru kamar yadda yake al'adar ta ce killace kan ta wurin da babu kowa tayi shiru ,"
  Motsin da taji an taɓa musu jakar kayan su , ya sa takai hannu tana kamo jakankunan nasu ,"

    Waye anan ?
Chapter 54 · 0% Book details