Sashe 177
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙaunar Falmata ga Ƙuli-ƙuli mai sugar , ta tuno dan haka ta je ta saya mata shi na ɗari uku fal cikin ƙaramar baƙar leda ta ɗaure ,
Ba zata yi wasa da kuÉ—in ba saboda guzuri sanin da tayi basu da inda zasu samu kuÉ—in mota a Niger idan suka yi rabuwar baram-baram da Youssouf .
Ko da haka ta kasance wataƙila baza su shiga matsala mai yawa ba kuɗin hannun ta zai isa dawo da su Nigeria .
*****
Kwanakin da suka biyo duk tayi su cikin ɗokin zuwan ranar tafiyar su ne , daga Rahima har Hajja sun fara gajiya da sabanbatun ɗakin da Yakaka take musu daga sun zauna .
Ta ƙira Malama Maryam ma ta sanar da ita , inda ita ma dai Nasihar ce ta ɗora mata bayan ta mata addu'o'in kariya , daga nan ta ƙira Lubna wacce ta gama fushin ta har ta huce akan rashin zuwa auren ta da tayi , murna sosai Lubna ta yi mata tare da addu'ar dawowa Lafiya .
Ta so ta je ta yiwa Amnee Sallama amma Amnee sun yi tafiya tun wajen sati uku da suka wuce ita da Ƙanwar ta Khaalty Rahima ,
Wacce aka ce ta dawo , duk da cewa bata samu damar ganin ta ba , amma tayi murna ƙwarai da dawowar ta , har ma tayi fatan ina dai su ma Allah zai dawo musu da Mamar su haka watarana ?
Sai dai ta ji tausayin ta saboda yadda Rahima take bata labari ta sha wahalar rayuwa sosai har ta ƙurumce dan haka ne ma suka tafi jahar Lagos inda za ta ga wani Babban likitan kunne a wani shahararen asibitin cutar da ta shafi kunne zuwa maƙoro dake jahar Lagos ɗin ,
A yadda Rahima ta shaida mata daga zarar sun dawo , za su dawo nan gidan ne ita da Amnee baki É—aya inshaAllah ,
Duk da bata san me ya raba Amne da gidan ba , amma tayi murna sosai da ta ji cewa zata dawo , saboda irin ƙaunar da take nuna mata ,
***
Babu irin gargaɗi a fakaice da Hajja bata yi mata ba , tare da hannun ka mai-sanda akan kar dai fa ta je da zummar ƙulla wani mugun abu.
Har 'yar nasiha ta dunga yi mata akan ta rungumi kaddarar ta , ta haƙura Allah zai kawo mata wani Mijin
Sai dai kasancewar ta ba mai yawan magana ba ya sa bata tankawa Hajja har ta yi ta gama zantukan ta da ta É—auke su a sowar biri .
Amma cikin ranta ta kan yi mamakin Hajja a lokuta da dama , ƙarfin halin ta kuma na bata haushi , wacece Hajja ? Yaushe ta shigo Rayuwar su ita da Falmata ? Shin wai zato take ta fi ta ƙaunar Falmata ne ?
Sai dai ta haƙura ta binne ɓacin ran ta har zuwa ranar da zata gwadawa Hajja cewa lalle ita da Falmata sune ɗaya .
Kamar yadda suka shirya ana gobe ranar tafiyar su Direban da zai kai su ya iso da ƙarfe takwas na safe , saboda kwana da ya yi a garin damaturu
Aka sauƙe sa tare da ba shi wajen kwana , a kuma ranar ne da hantsi misalin sha ɗaya na rana Zainab da Hafsa da 'ya'yan su har ma da Sofi suka iso dukkanin su daga garin Abuja ,
Nan take gidan ya daina yiwa Yakaka haske , ta shiga hidima da su da 'ya'yan su , ba ji ba gani .
Ga daga Zainab É—in har Hafsan basa wani sakar mata fuska , bare kuma Sofi wacce ko giftawa tayi ta gabanta sai ta bita da zagi da harara , duk ta bi ta takura ta gaza walwala ,
Rahima ma da take jin daɗin ta yau ta ga 'yan uwanta ta ƙule a cikin su , suna hirar su ta 'yan uwa ,
Cikin hirar da suke yi ne ta tsinci suna maganar isowar Amnee da khaalty Rahima da Doctor Hamza a gobe wanda shine ma maƙasuɗin zuwan su .
Har ta juya zata fita a falon bayan ta durƙusa har ƙasa ta miƙawa Hafsa Feeding bottle ɗin jaririyar ta da ta wanke da ruwan zafi , ta tsinci Muryar Zainab tana ƙiran ta ,
"Ke , un wa ma kike da suna ? Ki zo zamu hau sama ki taya mu gyara , wallahi Hafsa dan dai kun Æ™i ne amma ai da mun taho da munnira da indo masu aikina , da wannan uban aikin da zamu yi , ba gara mun biya musu kuÉ—in jirgin ba mun zo da su sun yi aikin , aikin fa ba na wasa bane duk É—akunan saman nan uku da Falo sai mun wanke su mun gyara ,Â
Sofi ta katse ta ,
"To ba ga wannan balamar ba , meye amfanin ta da ba za tayi aikin ba ?
Rahima ta katse ta tana É“ata raiÂ
" a gaskiya Antie Safiyya Aikin nan ya yiwa Yakaka yawa kin kuwa ga yawan ƙurar da take sama ? Ɗayan ɗakin nan na gefe ni tun da nake ban taɓa ganin an buɗe shi ba ,
"mts kome yawan sa daga nan zuwa gobe ai zata gama ke baki san ƙauyawa horan aiki bane ?
"gobe zata yi tafiya ki...
"Auntie Zainab zan iya a nuna min wajen ,
Yakaka ta katse jayayyar da take neman ƙulluwa tsakanin Rahima da Sofi ,
" Rahima ki nuna mata ta fara aikin kafin mu zo ,
Ta ƙafar benen dake cikin Falon suka hau sama , Yakaka sau ɗaya ta taɓa hawa saman tun lokacin bikin Zainab sai fa yau ,
Bakin ta ɗauke da Bismillah ta ɗora da Sallama ta shiga Falon da yake ba kome sai tarin ƙura buɗu-buɗu da gidan gizo-gizo , hatta shimfiɗar carpet ɗin an naɗe su ,
"Yakaka ki ga fa aikin da Auntie Safiyya ke cewa zaki iya yi ke ɗaya ? Ita dai muguwa ce wallahi .
Rahima ta furta Hakan cike da jin haushi ,
Murmushi Yakaka tayi , lokacin da take sanya ƙasan hijabin ta ta ɗaure daga kan hancinta zuwa bakin ta ,
"zan yi iyakar Ƙarfina Rahima ,
Ta furta hakan lokacin da take sunkuyawa ta ɗau sabon abun cire yanar gizo-gizo da ta gani a jiye a ƙasa daga dukkan Alamu an tanade shi ne dan yin aikin ,
Da addu'o'i a bakin ta ta shiga aikin cire yanar gizo ,
**
Ba su suka gama aikin da mafi yawa Yakaka ce ƙarfin sa ba , sai kusan tara na dare ,
Iyakar gajiya Yakaka ta yi sa , duk jikinta ciwo yake musamman bayan ta saboda sunkuyon shara , ga ƙurar da ta shige mata hanci ta sa mata mura sai attishawa take yi .
Washegari dakyar ta iya tashi tayi Sallar asuba ita da Hajja suka hau shiri ,
Banda mita babu abunda Hajja take yi
"Ace wai Yaran mata da ku sai dai ku yi kwance shaɓe-shaɓe kuna jiran a girka a kawo muku ? Wallashi yau babu wacce zan yiwa hidimar girki , girkin Alhaji kawai zan yi , tafiya ce mai nisa a gabana ,
" Akwai sauran tuwon jiya shi zan ɗumama mana ni da ke da direba , shige mu tafi kitchen ɗin
' kafin su gama baccin su ta shi mu mun yi nisa , kiyi abu da jikin ki Niger ba nan kusa ba gara mu kama hanya tun da duku-duku ,
Da sauri Yakaka ta ƙarasa sanya Hijabin ta , ta bi bayan Hajja zuwa kitchen ,
***
Ƙarfe takwas na safiyar Ranar Talata , Yakaka da Hajja tare da direban da zai kai su suka kama hanya , bayan sun yi Sallama da Prof ya musu fatan Alkhairi tare da basu Dubu biyar -biyar su ƙara a guzuri .
Duk da cewa Yakaka ta yi tafiya mai ɗan nisa tsakanin Abuja da Maiduguri , amma ta riski nisan tafiyar tsakanin jahar Borno Nigeria da Niamey Niger da tazarar da ta shallake tunanin ta , tun tana zaton an kusa lokacin da ta ga Yamma tayi rana ta faɗi ,
Har ma ta tambayi Hajja ko sun iso ?
Hajja ta shaida mata ai yanzu ne ma zasu tsallaka boda zuwa Æ™asar Niger , sai ta maida kanta ta kwantar a jikin kujera tana me cigaba da kallon rairayin saharar da ya tafi iya ganin ta da tsilla-tsillan bishiyoyi ,Â
Cikin ran ta tana sake jin haushin Youssouf da ya shata tazara mai tarin yawa haka tsakanin ta da ƙanwar ta ,
Ba su suka isa Niamey ba sai sulusin dare , ƙarfe biyu saura , kai tsaye direban ya dau hanyar gidan Youssouf da su ,
Suka yi amfani da 'yan mukullin hannun shi direban suka shiga cikin gidanÂ
A babban Falon gidan da yake sashin Falmata suka yada zango ,kasantuwar akwai gajiya Mai tarin yawa tare da su musamman Yakaka da har wani tsuku take ji jikinta na yi mata saboda gajiya, ga idanun ta da suke cike da bacci ,
Nan falon suka yi rashe-rashe ita da Hajja Bayan sun sallami direban ya yi tafiyar sa a daren , suka kulle gidan ,
Direban da ya kawo su yana juya kan motar kafin ya ɗau hanya sai da ya ɗau wayar sa ya ƙira wani layi abunda kawai yace shine ,
" Ranki ya daÉ—e na kawo su gidan, matar da take kula da ita tare da wata mace da cikin hirar su na fahimci 'yar uwa ce gare ta ,
Ya É—an saurara kaÉ—an , kafin ya É—ora da cewa ,
"gobe ma zan dawo wajen su doumin jin ko suna da watta buƙata kamar yadda shi yace ,
"To ki huta Lafiya ranki ya daÉ—e .
****
Washegari saboda gajiya basu farka da wuri ba sai kusan ƙarfe bakwai na safe sallah suka fara yi , kafin Yakaka wacce tayi jugum daga inda take zaune tana ƙarewa taffaɗan falon kallo da yake wadace da kayan more rayuwa irin na zamani ,
Ji tayi zuciyar ta ta É—an rage zogi ganin kyakkyawan muhallin da Falmata da Mama suke rayuwa a ciki ,