Sashe 101
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yamutse fuskar ta tayi cikin salon su na rikicin jaririyar zata yi kuka ,
 Â
 Da sauri ya ɗago ta zuwa dai-dai fuskar sa ya sanya kan karan hancin sa yana goge mata ƙwallar sa dake kan kumatun ta da yake zaton ita zata sa ta kuka ,
  Ai kuwa tamkar ya kunna ta sai kuwa ta sa kuka ,
  Kukan ta ya zo dai-dai da fashewa da kukan falmata wacce da kyar Rahima ta banbare hannun ta daga cukumar da tayi wa rigar Youssouf , cewa take wanene anan ?
Rahima waye ya kwace min baby ?
Ka bani ita dan Allah ka bani ita kar ka sa ta kuka ? Kai waye , ? Rahima kika ce min Baba ne yake ƙiran mu ,? To waye ne ya karɓe min Yakaka na ?
 Muryar prof ta sa ta ɗan samu nutsuwa har ta sassauta riƙon da ta yiwa youssouf , rahima ta samu nasarar janye hannun ta ,
 Amma kukan yarinyar da take jin sa kamar ɗigar narkakkiyar dalma ya sa ta kasa tsayar da kukan ta , "
 Â
  Ganin kukan ta yayi yawa ya sa Tafeeda tasowa ya dafa kafaɗun Youssouf , yana kallon fuskar sa , muryar sa babu ƙarfi sakamakon halin da ya ga Youssouf ɗin ya shiga tunda ya ɗaura idanun sa kan ƴar , yana nufin ɓullowar wani gagarumin lamari Masarautar Maradi .
Ɗan ouwa bada ɗiyar nan ga mariƙiyar ta , ga ta sai kuka take , !
Dauke idanun sa yayi da kyar daga fuskar Æ´ar ya mayar kan Tafeeda , da wata muryar da bata da amo yace ,"
 Ɗiya tawa ce Tafeeda , wagga Ɗiya jini na ce , Ɗiya ta ce , A yau ni Uba ne , Uba ne ga wagga ɗiya da tsautsayi tare da kaddarar zuwan ta duniya ya sa kome ya faru kamar yadda ya faru ,"
 Ɗan satar kallon prof , Tafeeda yayi yaga yadda hankalin sa baki ɗaya ke kan su , amma kasancewa falon me girma ne da ƴar tazara a tsakanin su ,
  Wallah ka lura Ɗan ouwa idan ba hakka ba kana iya ɓata mouna kome ,
Hannun sa ya kai da nufin karɓe ƴar daga hannun sa , wata irin zamiya Youssouf ɗin yayi ya janye ƴar jaririyar sosai zuwa cikin jikin sa ,"
Baka ganin kuka take ?? Ka bari na lallashe ta ,
 Haɗiye firgicin sa Tafeeda yayi , ka bada ita Yarima uwar goyon ta zata mata lallashi , akwai abubuwa dayawa a gaban mu ,
  Ina uwargoyon ta ?
Yace yana mayar da duban sa kan su Falmata da duk budurin da tayi na cukume sa da kalmomin ta duk bai ji su ba , ruÉ—anin da yake ciki ya toshe masa kunnuwa daga barin jin hayaniyar ta ,
  Da ɗan yatsa Rahima ta nuna masa Falmata wacce tayi shaɓe-shaɓe da hawaye sai ajiyar zuci take ,
 Ga ta nan ,
Matsowa yayi , ya miƙa mata ƴar
  Karɓe ta , ki kula da ita kar ki bari kome ya cutar da ita , kar ki bari tayi kuka ban lamunta ba ,"
  Hannun ta miƙa saitin inda take jin hucin sa , ta karɓi ɗiyar tana jin wani sanyi na ratsa zuciyar ta yana kore tunanin da zuciyar ta ke son kawo mata akan kamar ta taɓa jin amon murya kwatankwacin wannan ,!
Da kallo Rahima ta bi shi , kamar shine ? Kamar fa shine na jikin hoton cikin kayanYakaka , babu shakka ma shine ,"
  Ku koma ciki Rahima , prof yace ga su ,"
  Toh ,
suka ce suna kama hanyar barin falon ,"
  Youssouf zai magantu , Tafeeda yayi saurin yunƙurowa yana faɗin ,
 Mun gode Mun gode Baba , Allah ya saka da Alheri ya bada ladan Taimakon da kayi mana , yanzu zamu koma saboda a bakin aiki muke amma muna dawowa cikin kwanaki biyu masu zouwa da yardar Allah ,"
Ameen toh babu kome Allah ya nuna mana kwanaki biyu masu zuwa Allah ya ƙara muku haƙurin jure rashi, idan kun sake dawowa zamu yi magana ,..
Youssouf zai yi magana ,
 Tafeeda ya sake katse shi yana jan hannun sa
  Ɗan ouwa tashi mu tafi ,
Jaan hannun sa yayi suka fito daga gidan suna fitowa Youssouf ya zare hannun sa daga na Tafeedah ,
A tare suka haÉ—a baki wajen tambayar junan su ,!
ÆŠan ouwa meye haka kake shirin yi ?
Kana nufin nan zan tafi na bar ÆŠIYA TA ?
  Hannun mutanen da ban san su ba ?
Kallon baka da hankali Tafeedah ya yi mass kafin ya fara taku ya nufi wajen motar su , ',kazo muje muyi magana a tsanaki ,
  Ran sa bai so ba ya faɗa motar ya shiga Tafeeda ya fara ƙoƙarin tada motar lokacin da yake magana da sojojin nan akan su bar su madam saly an samo inda yarinya take ," ya sauƙe wayar yana hawa kan titi ,
Da fitar su Prof ya ɗaga waya ya ƙira Doctor Hamza bayan sun gaisa , yace
   Yanzu mijin yarinyar nan ƴar gudun hijira mai rasuwa ya bar nan gabana tare da ɗan uwan sa , ka ga ikon Allah ashe shi bai mutu ba , ya zo ya ga gan ta tare da ƴar sa yana...
  Wani mummunan cin birki da Doctor hamza yayi wanda hatta prof sai da yaji ,
 Subahananlahi , Hamza ban hana ka ɗaukar waya alhalin kana tuƙi ba ? Da fatan dai baka yi haɗari ba ? kana jina ?
  Muryar sa ƙasa ƙasa ya amsa bayan ya ɗauke kan motar zuwa gefen hanya bakin daji ya tsaya ,
Ina ji Baba , a bashi ƴar sa tare da ƙanwar matar sa ya tafi da su kar su sake dawowa Baba ,"
  Jimm prof yayi ,
Kafin yace
Toh babu kome idan sun nemi hakan ai sai a basu daman ai hakan ya kamata , ka dunga kula hamza ka daina ɗaukar waya alhalin kana tuƙin mota , kana ina ne yanzu ?
  Ina jigawa Baba , insha Allah zan kula baba , ka min addu'a baba , zamu yi magana idan na isa .
 Toh Allah ya tsare hanya daga ka isa ka sanar da ni ,
 ,"To ," yace yana sauƙe wayar
Cije gefen leben sa yayi , watau dai kome gaskiya ne , ga shi nan duk yadda suka shirya yana faruwa daki-daki , watau har sun yi auren ta turo shi ya zo ya ɗau ƴar sa da ƙanwar ta ,
  Zuciyar sa tayi duhu , me na miki da zaki yi wasa da zuciya ta irin haka ? Ashe sakayyar da zaki min kenan ?
Wani irin kishi mai ɗaci yake ji a ran sa , shan alwashi yake daga yanzu bai ƙauna sake jin ko me suna irin nata , bai ƙaunar sake jin duk wani abu da ya shafe ta , bashi da wani sauran uzuri da zai iya bata kariya da shi , ya yarda ya amince ta yaudare shi .
Tada motar yayi a hankali ya hau titi , yana nisawa cikin tunanin mace a yau !
Sojojin nan basu bar su madam saly ba sai da suka sake chasa su yadda ran su ke so ," Ah soja birgimar hankaka ne fa ?
   Suka yi ficewar su suka hau motocin su wasu a tsaye a bayan hilux wasu a zamne , suka yi tafiyar su ,"
illahirin gidan a ruÉ—e yake da kururuwar matan da aka lallasa , sai É—uruwa ake ganin su ana tambsyar me ya faru ? Me suka yiwa sojoji ?
Ɗan liti wanda muryar sa ta dashe saboda tsabar ƙwarmato , ya dubi madam saly wacce bakin ta ya kumburo yayi suntum sakamakon haƙorin ta ɗaya da ya fita ,"
 Cikin dusashiyar muryar sa yace saly fara yau wacce rana ce ? Kuma a wanne wata muke nawa kuma ga watan ??
  Da ido kawai madam saly ta bi shi tana jin yadda raɗaɗi yake ratsa tsokar jikin ta ta ko'ina gefe guda ga bakin ta da take ji kamar an cusa garwashi ,"
  Ya cigaba ,
Na rantse ki rubuta ki ajiye ido na idon wannan tsinannan yarinyar yagana sai dai uwatta tai naƙudar wata , wai ace kana zaune da makashin ka baka sani ba ? Ashe tuntuni ita ta san ana nan ana shirin far mana da yaƙin basasa ,amma tayi funfurus ta ƙi faɗa mana bare muyi ta kan mu ,ki tsoraci ɗan adam ƙuzazje mai tafiya da ƙafa biyu saly fara ,
wai yanzu ace tsawon lokacin nan ashe shegiyar yarinyar nan mai kama da takanɗa ta san inda yaran nan su yaks suke , shine bata taɓa yunkurin faɗa ba "ko daya ai yake hannun hagu ba baƙon duwawu bane ,"duk jirgi ɗaya ya kwaso su ," to ƙwaranƙwasa ba'a daki bulus ba, farautar ta zan shiga yi ba dare ba rana ," wayyo wayyo ni liti du mazauna na sun yi tsami sun ɗuri ruwa , saly gane min ko dai farfashewa mulamulai na suka yi ?
  Ya juyo mata duwawu ,
Kawar da kan ta tayi tana miƙewa da kyar ta nufi cikin gidan tana aiyana irin mummunan matakin da zata ɗauka akan Yagana , ai ita ba'a zubebeniyar ƙwaryar rashin mutunci da ita mutum ya kwashe ƙalau ,"
*****
Bayan komawar Biyamuradi Youssouf tare da Tafeeda ɗakin hotel , kowannen su shiru yayi yana saƙa cikin zuci ,