Sashe 42
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
  A firgice yakaka ta farka lokacin da samy baby take tashin ta , "cikin inda-inda ta fara bata haƙuri bayan ta gaishe ta, tare da faɗa mata cikin ta ne yake ciwo amma yanzu ya lafa ,"ta daina jin ciwon sa sosai , sai dai lema-lemar da take ji ta ƙasan ta ya sa ta gaza miƙewa sai faman muskuɗawa take cikin ran ta tana Allah ya sa dai ba fitsarin kwance tayi ba , toh amma ai ita bata fitsarin kwance tun da ƙuruciyar ta bare yanzu da ta zama ƴar budurwa ,
Tunanin ta ya katse lokacin da samy baby tayi mata umarni bayan ta miƙa mata kuɗi akan ta sayo mata soyayyar  indomi da ƙwai tare da shayi haɗin murtuku ya ji sugar sosai ,"
A sanyaye yakaka ta miƙa hannu biyu ta ƙarba tana mai taraddadin tashi kar samy baby ta ga yadda ta jiƙa mata kafet ," amma ba yadda ta iya haka ta miƙe tare da nufar bakin kofa
Bin bayan ta da kallo samy baby tayi tana tunanin me ya sanyayar mata da jiki ?ko cikin ke damun ta saboda ta san a wurin aiki da aike yakaka bata da sanya ," karaf idanun ta suka sauka a bayan yakaka inda shuÉ—in siket É—in yadin da take sanya da shi duk ya baci ,"
 Ke yaks dawo nan wai ke me yasa kin cika gidadanci ne ?? Yanzu har yau baki yi wayewar da zaki saka pad a jikin ki idan kina menses ba ? Haba mana yaks meyasa kullum ina kai ki kina dawowa , yanzu ba dan na gani na ƙira ki ba da kenan haka zaki fita ?? Ta ƙarasa zancen tana balla mata harara ,"
Ƙasa da kan ta yakaka tayi tana me satar kallon wurin da ta tashi domin ita duk bata wani gane kalmar pad da menses ba , ga zaton ta faɗa samy baby take yi mata akan fitsarin da ta saddaƙar shi tayi a kwance "ɓacin rana"
, sai dai ga mamakin ta wurin da ta tashin É—an alamun danshin kaÉ—an ne kuma bai wani fidda kala ba saboda kafet É—in ruwan kunkumadi ne ita ma da kÆ´ar ta hango danshin toh akan me samy baby take mata faÉ—a ?? Tunanin ta ya katse lokacin da ta ji samy baby ta ce ,"
   Ki buɗe ƙaramin akwati na ki ɗauki sabon pant da pad ki shiga banɗaki ki gyara jikin ki nan gaba kar ki sake zama babu pad alhalin kin san lokacin yin menses ɗin ki yayi kusa kina jin alamar sa ki tanadi pad idan ma baki da ita ki zo na baki koh kuma ki yi ƙunzugu da tsabatatatcen tsunma kin ji koh ,??
Da sauri yakaka ta gyaɗa kai tana rarraba idanu , domin ita har ga Allah ba wani fahimtar dogon bayanin samy baby tayi ba , koh ta so fahimta ma kalmomin da ta jefo guda uku da turanci sun hana ta gane kan maganar , dan haka kawai sai ta je ta durƙusa a gaban akwatin tayi zugui ,"
Fahimtar da samy baby tayi yakaka fa bata fahimce ta ba ya sa ta tashi ta zo ta buɗe akwatun ta tare da ciro sabon pant fil sai tashin ƙamshi yake ( ku sani mata tsabtace undies tare da wanke shi da kuma goge shi wani babban sirri ne na sanya nishaɗi a gangar jiki tare da bada kariya na musamman daga kamuwa da cututtukan da suke addabar mata daga ƙasan su a zamanin yanzu ,ki kasance kullum cikin wanke tare da goge panties ɗin ki bayan kin shanya su a rana sun yi a ƙalla awanni shidda a rana ) da kuma ledar pad mai guda takwas ta danƙa mata," ki shiga banɗaki ki gyara jikin ki ,"
Da sauri yakaka ta amsa da toh ,
  Kin iya amfani da shi koh ?
  Gƴaɗa kai ta yi sai kuma ta sake girgiza shi ,"
Samy baby wacce ta fara zowa wuya da gidadanci tare da jahilcin yakaka tace ,"
  Buɗe baki zaki yi kiyi magana ba ki dunga gƴaɗa min kai ya kadangaren gobara ba , kin iya amfani da shi koh na gwada miki ??
  A sanyaye ta amsa ban iya ba ,"
Karɓa tayi tare da nuna mata yadda ake amfani da shi ta ɗora mata da ,"ki wanke siket ɗin naki a banɗakin zan miko miki wasu kayan ,"
Ƙiris ya rage yakaka ta kurma ihu lokacin da ta ga yadda jikin ta ya ɓaci da jini ,"tashin hankali na shiga uku na lalace fitsarin jini na fara shikenan nima zan mutu na bi su abba wayyo Allah falmata waye zai kula min da ke ," wannan shine tunanin da yakaka take yi lokacin da take wanke jikin ta da kayan ta , tana yi tana sharar hawaye ,"
Ido jazur ta fito bayan ta shirya kan ta cikin kayan da samy baby ta miƙa mata na wata koriyar atamfa riga da siket , sun zauna mata ɗas kasancewar ita ma samy baby ƴar madaidaiciya ce tamkar ta ,"
Sumi-sumi ta wuce tana share guntun hawaye ta nufi wurin aiken da aka mata ,' samy baby ta bi bayan ta da kallo tana me jin tausayin yarinyar na zaunawa cikin ranta , ta fahimci yau ne ta fara tsintar kan ta a yanayi na al'ada saboda tashin hankali da damuwar da ta gani tare da yakakar wanda ba kome ya jawo hakan ba illa jahilcin addini da na boko saboda da tana zuwa makaranta kowacce daga cikin ta boko koh ta islamiyya a shekarun ta da take sha shidda da ƴan watanni ya ci ace ta san me wannan jinin yake nufi saboda ana wayar da kai a makarantu ," nan take ta ji tana son tayi yunƙuri domin ganin yakaka ta ɗan samu ilmi ko kaɗan ne domin ita kan ta harkar da take son ɗora ta akai idan kana da ilmin boko kafi samun kasuwa wurin manyan wayayyun mutane irin wanda take yi wa yakakar yangen su , domin su basu cika harka da jahila ba ," zamani ya zo da kome zaka yi domin cigaban kan ka sai kana da ilmin zamani ilmi shine gishirin rayuwa ,"
Tana tafiya tana rarrakaɓewa ta jikin gini tafiyar kan ta ba yadda ta saba take yin ta ba tana tafe tana mammatse kafafu domin ji da take tamkar ƴar audugar da take jikin ta zata faɗo wacce rashin sanya ta a dai-dai ya sa take jin hakan ," cikin ranta kuwa kalmomin wasiyyar da zata barwa falmata take haɗawa ,"
Yaks baby , yaks baby , ke yaks ji mana wai yane ina miki magana kina wani ƙara wuta tamkar baki ji na , zo mana magana za muyi ,"
Muryar babasho mai sayar da wiski da su matallah , zuwa kan taba sigari da sauran kwayoyin sanya maye a cikin ɗan shagon da yayi da tsoffin kwanukan rufi da katako ,ta katse mata tunani , babasho yayi masifar maƙalewa yakaka , yana bala'in son ta kamar zai yi hauka ,sai dai samy baby ta kasa ta tsare ta hana ya samu damar koh ɗan zantawa da yaks , duk kuwa da cewa kullum sai ya je rumfar saly baby ya sai burkutu dan kawai ya samu ya ga fuskar yaks ," samy baby ta kan faɗa mata ," ta wuce ajin babasho fintinkau , me zata yi da wannan sauran tabar ? Da duka-duka idan aka haɗa jarinsa da shagon nasa ba zai fice dubu goma ba ,?? Ai sama tayi wa yaro nisa tsakanin ta da ire-iren su babasho sai dai ta kira su ta aike su ,"amma ita kalar manya ce kalar hamshaƙan da suka ci suka tada kai da naira ,
," kar ki kuskura ki kula shi yaks bashi ma da isasshen hankali idan ya sha ta kai masa karo yana iya shaƙe ki ya kar ki ya kar banza atoh kiyi hankali,"
Ga yakaka kuwa ita ba ma babasho ba da take jin mugun-tsoron sa saboda chukurkuɗaɗɗan gashin sa da ya tara akai baya wani kula da shi duguzum-duguzum ya fenta kan kalar jaa shuɗi da kuma yalo , uwa uba faranta hannunsa zaƙo-zaƙo da suke cike taf da annakiyar dauɗa suna tsorata ta har su sanya ta hasashen yadda zai kafa mata farce a wuya idan ya shaƙo ta kamar yadda samy baby take faɗa mata , ita gaba ɗaya maza ma ƙarƙashin ranta tsoron su take , babu wani ɗa namiji da ta taɓa jin sa cikin ranta idan aka ɗauke dakta hamza wanda shi ma ta ɗauki tunanin sa da yake faɗo mata jifa-jifa a zuwan tana tuna sa ne domin taimakon da yayi a gare su ita da ƙanwar ta , bayan shi babu wani ɗa namiji da yakaka take ɗaga kai ta dube shi iyakar ta da su harkar cinikayyar su ta burkutu su , su zo saya ta je ta kawo musu ta karbi kuɗin ," bata taɓa buɗe baki tayi tsiwa koh rashin kunya ga kowa ba duk kuwa da yadda suke kai mata wawura tare da maganganun banza da ita bata ma kai ga fahimtar wasu kalmomin su na batsa ba ,"ita dai ba'a raba fuskar ta da tsadadden murmushin ta , dan haka yanzu ma da babasho yake kwala mata kira koh kallo bai isheta ba haka ta cigaba da tafiyar ta ,' shi kuwa ya bi bayan ta da kallo yana lashe leɓe tare da lanƙwasa ƴan yatsun sa cikin ransa yana fatan Allah ya kai damo ga harawa koh bai ci ba yayi birgima,",
Karo taji tayi da mutum wanda zurfin da tayi a tunanin ta ya sa bata ga tahowar sa ba ," da sauri tayi baya ,tare da durƙusawa ta ɗauko masa makullin motar sa da ya faɗi a hannun sa ta sanya bakin gyalen ta ta goge ƙasan jikin ɗan makullin bakin ta ɗauke da kalmar ban hakuri ta miƙa masa mukullin ba tare da ta ɗago kan ta ba ,