Sashe 30
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wanda su da kan su a duk lokacin da larki ta buɗe murfin durum ɗin domin ɗebo ruwan burkutun , tururin sa da warin sa yana bugar da su ta yadda har suke jin kan su na juyawa ," koh sau ɗaya basu yi gigin ɗanɗana burkutun sun ji irin ɗanɗanon ta ba hasalima ma ita yakaka koh ruwa bata sha ba abincin ma da madam sally ta saya musu ita nata juye shi tayi a leda ta kulle da niyyar sai sun koma sansanin su suci ita da ƙanwar ta , yagana ce ta cinye nata .,
Hankalin yakaka ya fara tashi ne lokacin da ta fara ganin hadari yana haÉ—uwa a garin , gashi kuma lokacin tashin su bai yi ba ,"
Zuciyar ta ta cika taf da tunani tare da zullumin halin da falmata take ciki , Allah-Allah take lokacin tashin nasu yayi ta tafi ga ƴar kanwar ta kafin ɓarkewar ruwan saman da ta san barazana ne ga lafiyar falmatan ,"
A karo na barkatai larki ta sake miƙawa yakaka dogayen kofunan da suke cike da barasa mai turiri , tare da umartar ta ta miƙa su ga mutanen da suka bada kuɗaɗen su yanzu , cikin rashin kuzari yakaka ta karbi kofunan tana mai ɗaga kan ta tana sake kallon ɓakin hadarin da ya shata layi a sama yake ta faman rugugi ,"
Dai-dai ta sanya kai cikin shagon taji wata irin ƙarar da ta razana ta sanya ba shiri ta saki kofunan dake hannun ta suka tarwatse ruwan ciki ya watsu a jikin mutane biyun da suke zaune daga farkon shagon akan kujeru suna kurbar ruwan su ,"
Zafin kakkarfan marin da ya sauka akan kumatun ta shi yayi sanadiyyar dawowar ta cikin hankalin ta da ta rasa na ƴan daƙiƙu sakamakon ƙarar tashin bom ɗin ,"
   Dan uban ubanki shegiya baki da hankali ne zaki ƙona mu ? Ƴar mahaukaciya ko yau kika fara jin irin ƙarar tashin bom ɗin nan kina maiduguri ? Bace mana anan kafin mu tattataka ki ƴar*
  Kusan dukkanin rabin mutanen da suke cike cunkus a cikin shagon suka kwashe da wata irin mahaukaciyar dariya suna nuna ta , ita kuwa sai wuri-wuri da ido take sam zafin marin bai ɗimautata ba kamar kalmar bom da taji mutumin da ya mare tan ya ambata ," bom aina kuma bom ya tashi ? Falmata ita ce kalmar da ta fara tasowa ta daga ƙarƙashin zuciyar ta ta kuma bayyana kan ta akan laɓɓan ta ,"
Da gaggawa ta sunkuya ta tsince kofunan da suke ƙasan kunnuwan ta sun toshe daga barin jin dararrakin mutanen da suke wajen , ta juya cikin sassarfa ta koma ciki ,"
A tsaye ta taradda yagana wacce itama alamun firgici yana bayyana baro-baro akan fuskar ta ,"basu samu damar magana ba sakamakon wayar da madam sally fara wacce take bullowa daga wani É—an lungu a tsukin wurin da suke zaton gida ne ta cikin lungun , wayar da take yi ta É—auki hankalin su ,"
     Ni sally naga ta kaina bom a post-office ? Na shiga uku kadda dai yayi mummunar barna ? Tabdi Allah dai ya kwashewa waɗannan mutanen albarka tsinannun banza kana zaman zaman ka su aika da kai barzahu ," toh yaya zaka shigo ɗin ne ? Ga fa ruwan yana jiran ka kar ya huce ," ta karasa zancen ta tana sakin shewa tamkar ba ita ta gama bayyana jimami ƴanzu akan fuskar ta ba ,'
Da sauri yakaka ta ƙarasa gaban madam sally ta durƙusa ," tare da sunkui da kan ta tayi shiru ," dukkan su idanu suka zuba mata suna sauraron ta , tare da kallon jikin kayan ta da burkutun ya jiƙa ,"
  Ganin tayi shiru bata ce kome ba ya sa madam sally fara jaan wani guntun tsaki ,"
   Ke ban son iskanci meye zaki wani zo ki tare min hanya kuma ki ƙi cewa kome, idan aikin ne baza ki iya ba ki faɗa min sai na baki iya kuɗin awanni da kika min ki kara gaba
Da sauri yakaka ta É—ago kai jin ana shirin korar ta , cikin karkarwar murya da inda-inda tace ,"
  Madam dan Allah ina ne inda naji ana cewa bom ya tashi ? Nan kurkusa ne ?
   Kallon banza madam sally ta yi mata , kina nufin baki san post-office ba kina garin nan toh ta ina kuka zo ? Ku da kuka ce kuna camp ? Inda mota ta biyo da ku daga camp zuwa cikin gari ta sauke ku nan ne post-office kusa da kasuwa monday market ,"
Zuruf yakaka ta miƙe tana rarraba ido , da sauri kuma ta sake durƙusawa ,
madam dan Allah ƙanwata falmata , ƙanwata falmata tana bakin kasuwa tana bara , kuma bata san ko'ina ba makauniya ce ," dan Allah ki taimaka ki min izni naje na zo da ita ," ta karasa zancen ruwan hawaye yana sulluɓowa akan kududdukin ta ,"
  Karo na farko madam sally taji ɗan tausayin yaran ya kama ta ,"
   Babu kome kina iya tafiya ƴar uwar ki sai ta ƙarasa aikin tun da bai wuce awa ɗaya da rabi ba masu aikin dare su iso ,ungo kuɗin sallamar ki ,kiyi sauri kije kar a fara rurrufe hanya a hana wucewa ,'
Kallon yagana tayi wacce ta so da madam sally ta bar su sun tafi tare kamar yadda suka zo , sai dai babu yadda zata yi ita ma alfarma aka yi mata domin duka aikin da suka yi bai wuce na awa uku ba ,"
 Yagana zan tafi zamu jira ku a tasha .
  Yakaka zaki iya gane hanyar fita daga unguwar nan ? Kar ki ɓata fa
  Zan iya ganewa yagana sai kun zo !
Daga haka ta matsa ta ɗauki ledar da ta ƙulle abincin ta a ciki , cikin sassarfa ta sanya kafa tana barin wajen ba tare da ta koh tsaya ta wanke wurin da ruwan burkutun nan ya bata mata zani ba ,"burin ta kawai ta iske ƙanwar ta a inda ta bar ta cikin ƙoshin lafiya ,"
  Zamiya da zilliya ta dunga yiwa kattin mazan da suka buge tatil da giya a cike da wannan filin da ake kaɗa kalangu ,suna ta rawar banza da fitsara sun kama ƙugun matan banza ,"tamkar dai basu da masaniyar halin tashin hankalin da garin yake ciki ,"
Bata bi ta kan kolo ba kawai ta ɗauki hanyar da suka biyo a yayin tohowar su tana tafe tana jefa kafa tare da share guntayen ƙwallar da suke silalowa lokaci-lokaci daga gurbin idanun ta , zuciyar ta cike taf da fargaba ta ƙagu ta isa wajen falmata ,"
Ji tayi kamar ana ɗan taɓa ledar hannun ta , cikin hanzari ta waiwayo ,"
  Shiɗewar wucin gadi tayi lokacin da tayi ido huɗu da wata mayunwaciyar karya baka kirin da ita tana dalalo harshen ta waje , ƙamewa tayi ƙyam tana jan numfashi da ƙyar suka yi kallon kallo na kusan minti guda da bakar karyar nan ," kafin yakaka ta zabura tare da yankawa da gudu cikin matukar gigita da tsorata ," karyar nan kuwa bata bata lokaci ba gurin rufa mata baya ita ma a guje tana haushi ,"
Gudun fanfalaki yakaka take yi tana yi tana waiwayon karyar nan da zuwa yanzu suka zama su biyu ne suke bin ta tare da wani Æ™aton kare ,"Â
Kutsawa take tsakanin layukan unguwar ba tare da tana lura da inda take bi ba , taimako take nema amma abun takaici duk da unguwar cike takd da mutane dattajai da matasa , cikin su babu wanda yayi yunkurin taimakon yakaka , sai ma dariya da ihun da matasan suke bin ta da shi har ta ƙulewa ganin su a guje , yara kuwa suma rufa masu baya suke yi da gudu suna ihu da dariya tare da kiran sunan kanukan suna tafi,"
Tahowa yake daga cikin siririn layin da baya bullewa , fuskar sa sam babu annuri da alama akwai abun da ke damun zuciyar sa ,"
Tun a nesa ya fara jiyo hayaniyar su kafin ya hango shawo kwanar da tayi a guje tana mai jefa kafar ta cikin dagwalon kwatami bayan ta karnuka biyu su ma a guje kafin ya ga bullowar zugar yaran da ya jiyo ihun su biye da ita,"
Gadan gadan ta nufo shi , yana yunkurin kauce mata , yaji ta taho gabaÉ—aya ta faÉ—a cikin kirjin sa tare da zagaye hannuwan ta tsam da jikin sa , dai-dai lokacin da karnukan ke karasowa .!
 Masoya me kuke tunani?
 me kuma zaku ce ?
Yaya kuka ga shafin nan ?
kar ku manta sharhin ku shine tukuici na , shi kuma zai bani karfin gwaiwar cigaba da sambaÉ—o muku hargitsin rayuwar Æ´an matan uku
#vote
#comments
#share
#fikrh
[6/24, 10:57 AM] +234 701 013 7848: Fikrah writers association
MAFARI.......
( Hargitsin rayuwa )
12
Cikin hanzari ya raba ta da cikin jikin sa ya sauya mata matsaya zuwa bayan sa lokaci guda ya sa kafa ya kaiwa bakin "karyar" duka ,a dai-dai lokacin da tayi nufin kaiwa ledar hannun yakaka wawura ,wanda hakan ya sa yakaka ta sake riƙe bayan rigar sa tamau tana me sake mannewa da jikin sa cikin karkarwa tare da runtse idanun ta ,batare da tayi la'akari da kyau gami da hasken lallausan yadin jikin sa ba ,
Ke dallah Sakar min riga koh bakya gani karnukan sun gudu ne ??
   Cikin hanzari yakaka ta buɗe idanun ta da suke runtse tare da sakar mishi riga gami da matsawa daga jikin sa kunnuwanta suna jiye mata kamar ta san muryar sa .
Ba tare da ya waiwayo ta ba ya cigaba da takun sa da nufin cigaba da tafiya inda ya nufa ,
Bayan sa ta bi da kallo bakin ta na son furta masa kalaman godiyar taimakon da yayi mata ,