← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 269

Sashe 67

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da gudu ta tako ta fito daga Æ´ar rumfar , yanayin da ta ga falmata a ciki ya mantar da ita duk wani halin fargaba da tsoron soji da suke ciki ,

Tana kuka ta nufi bakin titin inda ta hango gungun soji da wasu mutane farar hula suna tsaye , tun kafin ta karaso gudun da ta taho da shi ya É—au hankalin su ,tare da ihun da take faman yi

Tana ƙarasowa ta zube a gaban su ba tare da ta ji tsoron bakin bindigar da ta ga sojojin suna gyarawa ba tare da saita ta da ita ,"

    Da rishin kuka take cewa kun harbi ƙanwa ta , zata mutu , kun kashe min ƙanwa ta me tayi muku ? Mu ba boko haram bane , meyasa zaku harbe ta wayyo Allah ƙanwa ta ,"

Wasu daga cikin su sun fahimci abun da tace dan haka wani daga cikin su fararen hula ya É—an matso kusa da ita ,
    Ina ƙanwar taki take ?

Waiwayawa tayi tana nuno masa ƴar rumfar da suke ciki , tsabar kuka da ruɗanin da take ciki har numfashin ta sarƙewa yake yi ,

Su biyu suka nufi rumfar
   Yakaka ta take musu baya

Nan take suka fahimci bullet ne ya samu falmata a kafaÉ—a cikin rashin sani ,"

Da gudu gudu suka koma wajen sojojin tare da neman taimakon su akan a kai yarinyar asibitin kurkusa , ba tare da gaddama ba soja É—aya ya amince zai jaa su a motar su ta soji .

Dan haka suka ciccibo falmata wacce ta riga ta suma suka ɗora ta bayan hilux ɗin sojin tare da yakaka wacce idan banda sambatun kiran sunan falmata babu abun da take gaba ɗaƴa ta ƙanƙame falmatan a jikin ta .

Da isar su babban asibitin gwamnatin jaha ( general hospital ) wanda bashi da wani tazara mai yawa da bakin kasuwar , aka shige da falmata bangaren bada taimakon gaggawa ( Accident and emergency)  nan suka tarar da mutane dayawa da suke cikin hali makamancin na falmatan wanda tarzomar jiya ta ritsa da su birjik , wasu sun ji munanan raunika , wasu babu hannu , wasu ba ƙafa , likitocin da suke kan aiki sai kai kawo suke , da alama sun gaji likis ga har zuwa yanzu akwai waɗanda ko kai ga fara basu taimako ba'a yi ba ,

Nan suka ajiye falmata akan dandaryar siminti bakin kofar domin duk gadajen da suke cikin É—akin a cike suke ,

Bayan sojan ya shiga ciki yayi musu bayani , likitocin suka ce a ajiye ta kawai zasu zo kan ta domin aiki ya musu yawa , ko kuma idan likitocin safe sun zo su duba su tun da sun ce harsashin a kafaÉ—a ya same ta da sauki akan waÉ—anda bam ya tashi da su ,

Tsayuwar da bata fi ta rabin awa ba mutanen da suka kawo su suka yi , suka matso kusa da yakaka wacce har zuwa lokacin idanun ta zubar hawaye suke har sun kumbura ,
     Yarinya mu zamu tafi , domin muna da aiyuka a gaban mu , su kuma likitocin nan ƴan walakanci ne basu da niyyar zuwa su duba ta , ki cigaba da jiran su , sannan ki dunga leƙawa kina damun su akan su zo su duba ta , idan kuwa ba haka ba har jinin jikin ta sai ya ƙare ta mutu anan indai likitocin nan ne babu abun da ya dame su , mu mun tafi ,

ga wannan ki rike a hannun ki ko zasu ce ki sayo wani magani ,suka miƙa mata dubu ɗaya suka kaɗa kan su suka yi ficewar su ba tare da sun sake kallon inda falmata take yashe a ƙasa ba ,"

Wani sabon kuka ta sake fashewa da shi tana tattaɓa fuskar falmata wacce tayi sanyi ƙalau ,"
    Falmata na dan Allah kar ki bar ni , Falmata dan Allah ki tashi ,'
  Kamar mahaukaciya ta yunƙura ta tashi ta bazama ta faɗa cikin ɗakin da ake duba marasa lafiyan ,"
   Tana shiga nurses ɗin da suke taya likitocin aiki suka yi mata chaa ,"
   Mata meye hakan ? Baki ga aiki muke ba zaki zo kan mu da ihu ? Ki koma daga waje ki jira a fito da marar lafiyan ku , ba'a shigowa nan idan ba mu muka kira mutum ba fita-fita dallah ,"

  Kuka ta fashe da shi
   falmata na zata mutu dan Allah likita ki zo muje ki duba ta jini sai zuba yake daga jikin ta jinin ta zai ƙare ta mutu idan ta mutu bani da kowa ,"

    Kalaman ta suka doki kunnuwan sa yayi tsai daga aikin ɗinkewa wani mutum mummunan rauni da yake yi ,"
    Tabbas ita ce , ita ce da kullum damuwar ta yake ga falmata ƙanwar ta ita ce da kullum hawayen ta yake zuba akan ƙanwar ta falmata , bata da wani abu mafi muhimmanci da ya wuce ƙanwar ta falmata , ita ce wacce ya kwashi watanni yana neman ta har ya zo ya haƙura ,

   Cikin nutsuwa ya waiwayo yana duban inda take lokacin da nurse ɗin ta sanya wata security guard da take tsaye daga bakin kofa , tayi waje da ita domin tana son bata musu aiki ,"
    Security guard ɗin ta cukuikuyo hijabin ta tana tura ta waje ,
   Ita kuma tana sake ƙara karfin kukan ta tare da neman su taimaka mata ƙanwar ta kar ta mutu ,"

Hey jumai let her come in .

Suka tsinkayi muryar babban likitan su da yake duty , ya bada umarni

A tare suka waiwaya da yakaka wacce jin muryar sa ya sa ta waiwayo da fatan son kasancewar shi ne da gaske a wurin ai kuwa tayi arba da shi jikin sa sanye da korayen kaya ,'É—an siririn farin gilashin da yake É—ore saman karan hancin sa bai isa ya sa ta gaza gane shi ba ,"

Da ƙarfi ta fizge jikin ta daga riƙon da security tayi mata , ta tako da gudun gaske ta ƙurɗo ta tsakanin gadajen marasa lafiya tana zuwa ta kamo hannun sa da yake cikin safar hannu ta duba marasa lafiya ta shiga jaan sa tana cewa
    Dakta ƙanwata falmata ai ka san ta ko ? Ita ce harsashin bindiga ya same ta , ta suma kamar ta mutu jini yana ta zuba a jikin ta , dan Allah ka zo muje ka duba ta ,kar ta mutu dan Allah ka taimaka min !

  A hankali ya zame hannun sa daga riƙon da tayi masa , ya maida duban sa ga nurses ɗin da suke tsaye

   Ku sa a shigo da ita !

Doctor bamu da gadon da zamu ajiye ta ,"
    Yana mai komawa bakin aikin sa yace
     A nemo gado a ɗaura ta akai yanzu zan duba ta ,'

   Biyu daga cikin nurses ɗin suka fita tare da security guard ɗin , yayin da ɗaya ta aunawa yakaka harara ,
   Ai Sai ki fita mata , domin ba'a tsayuwa anan ,'

   Ba tare da ya juyo ba yace

Sister kalsum ki bar ta ta tsaya anan , yanzu za'a shigo da ƙanwar ta ,!

Tashin hankalin da ya hango a fuskar ta ya taɓa masa zuciya sosai ,"yana jin  tausayin ta mai ƙarfi yana taso masa , ita kullum a cikin kuka da wahala take !

MokaÉ—e baki nurse kalsum tayi ,
   Cikin ran ta tana son sani alaƙar dactor hamza da wannan kucincinannar yarinyar ƙazama !

Cikin mintoci goma sai ga falmata an turo ta a gadon marasa lafiya an shigo da ita ," da hakan ya zo dai-dai da kammala aikin da yake yi ,
   Ya tako ya zo gaban gadon falmatan ya duba ta tare da yin aune aune , nan ya fahimci ta zubda jini dayawa da ya sa dole sai anyi mata ƙarin jini , bayan an cire harsashin da yake cikin jikin ta
   Dan haka yayi umarni a kare gadon falmatan a kuma sauya mata kaya zuwa na tiyata," sannan ya juyo da ganin sa ga yakaka , cikin tausasa murya tare da sigar lallashi yace ,
      Ki nutsu ki daina kuka haka kin ji ko ? Ki samu wuri ki zauna a waje ,ki sayi ruwa ki sha ,insha Allah babu abun da zai samu ƙanwar ki , ɗan rauni kaɗan ta ji kuma yanzu zan cire mata harsashin na ɗinke mata wajen na sa magani zuwa anjima zata farka kuyi magana kin ji ko ?
   Gƴaɗa kai tayi tana duban fuskar sa
 cikin son samun tabbaci ta ce
" Ka ce zata samu sauki har ta tashi anjima koh ?
    Sosai kuwa insha Allah
ya bata ansa yana mai duban ƙwarar idanun ta da tsabar kuka ya sauya musu launi ,"
    da jan ƙafa ta fice tana waiwayan inda falmatan take ,
   Shi kuma ya juya ya ɗau wata ƴar takadda yayi rubuce rubucen sa ya kira ɗaya daga cikin ma'aikatan da suke tura gadajen marasa lafiya/kujerar marar lafiya , ɗauko file da sauran su , ya miƙa masa takkadar bayan yayi Signature ya buga Stamp .
      Ka je blood bank ka kai musu , ka tsaya ka ƙarbo jinin ka kawo .
    Toh sir
  Cikin gwanancewa ya fara aiki ga falmata !
Chapter 67 · 0% Book details