← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 269

Sashe 109

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina sake miƙa godiya ta bisa ga tarin saƙonnin ta'aziyar ku da suka iso min kan rasuwar ƙani na , nagode ƙwarai Yaa Allah ya amsa addu'o'in da ku ka yi masa , ya kuma baku lada Ameen thumma Ameen

   Nagode !

    
[9/3, 10:13 PM] +234 806 122 1116: Fikra writers association

MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )

umm'muaz

30

Babu kowa a harabar barikin sai masu gadi da suke daga kowacce kusurwa  , sakamakon dare da ya raba tsaka 2am , sai Biyamuradi youssouf da ke kai kawo a cikin hunturun sanyin da yake ratsa har ɓargon mutum gami da iska mai ƙura da take toshe ƙofofin hancin ɗan adam , a tsaye yake tsakiyar filin ya sunkui da kan sa jikin sa sanye da ƴar baƙar riga mai gajeren hannu da dogon wondon uniform ɗin su na soji ,

Ya zurfafa a tunanin makomar Auren da yake shirin karɓarwa kan sa nan da wasu ƴan awanni zuwa wayewar gari ,
    Ina zai dosa da auren yarinyar ?? Yarinya ce ƙanƙanuwa , sannan kuma miskiniya , ta wacce hanya zai fara tallafar ta , domin ƙwarai take buƙatar matallafi cikin rayuwar ta da bata da kowa sai ƴar jaririyar sa ,

    Me zai cewa iyayen sa su fahimce sa da dalilin sa na auren ta? Wanne irin hukunci maimartaba da hajiya umma zasu yanke masa idan suka ji ainahin abunda ya aikata da har ya kai shi ga auren yarinyar ?? Zasu su yi fushi mai tsanani da shi irin fushin da baya fatan ya gitta tsakanin sa da iyayen sa duk tsawon rayuwar sa ,

    Me zai wakana tsakanin sa da gimbiya maimunatu lokacin da ta san ya auri wata mace kafin ita , Yana riƙe da auren wata bayan ita ? Zata iya yi masa kallon mayaudari kuma munafuki , a ƙarshe soyayyar su zata gurgunce da zai iya datse alaƙar su shi da ita , bai fatan haka saboda ya shaida irin tarin ƙaunar da zuciyar sa ke yiwa gimbiya maimounatu,

Kalaman prof ya tuno inda yake ce da shi ,
    Madallah tunda ka amince da auren Fatima , ka zo da wakilan/waliyan ka, a gobe zan baka auren ta , daga nan idan kana buƙata a goben zaka iya tafiya da ita tare da ƴar ka ,

   A lokacin ya amsa masa da
    Toh na Amince
Har ya tashi zai tafi prof ya tsaida shi ,

To amma akwai wani lamari guda ɗaya , lamarin kuwa shine bazan iya ɗaukar yarinyar nan na baka ita , ka tafi da ita, ita kaɗai ba dole zan haɗa ka da mutum ɗaya wanda za ku tafi tare chan ƙasar ta ku domin a gano inda zaku zauna saboda sha'anin duniya , ta ka zo ta kan zo ko watarana wasu daga cikin dangin su zasu ɓullo su zo neman sanin inda ƴar su take , da fatan ka fahimceni da kyau kuma ka amince ?

   Jim yayi a ƙarshe ya sake amsawa da
   NA AMINCE

Waje ya samu ya zauna akan É—aya daga cikin dakalin da aka yi su domin zama dake a watse cikin barikin ,

Da farko yayi niyyar idan ya ɗauke ta ya kai su Niamey gidan ubbo a matsayin ƴar gudun hijirar da ya taimaka ita da baby mama idan ya so su kasance ƙarƙashin kulawar ubbo tare da shi har zuwa lokacin da zai samawa kan sa hanyar da zai bi ya bayyana su ga dangin sa ba tare da abubuwa sun rinchaɓe masa ba ,

Sai dai batun haÉ—a su tafiya da wani ya rusa wannan nufin nasa domin ko kusa ba zai so a san wasu dangi nasa ba , ba zai so asan ko shi wanene ba saboda kar watarana kome ya bayyana , a biyo sawu ba tare da sanin sa ba , kome ya lalace masa a lokacin ,

Idan kuwa har ya nuna ƙin amincewar sa , hakan zai sa a dasa ayar tambaya akan sa , ayi masa zaton marar gaskiya , wanda zai iya sa pro ya tsananta bincike akan sa wataƙila a ƙarshe kome ya isa ga masarautar su , bai fatan haka ,

Idan kuwa haka ne dolen sa ya yarda ya tafi da su da me rakiyar su ,

Ƙaunar ƴar sa da Allah ya jarrabe shi da shi ya sa duk yana ƙoƙarin fuskantar duk wani ƙalubale , burin sa ya tsira da ita , dan haka a ƙarshen tunanin sa ya ture duk wani ƙalubale gefe ya amince da mallakar baby mama tare da uwar goyon ta a lokaci guda da me rakiyar su ,

Yana tsaye a wajen aka yi ƙiran sallan farƙo na karfe 3:30am , kai tsaye ya nufi babban masallacin cikin barikin ya ɗaura alwala da sassanyan ruwan da iskar hunturu ta gama hura sa ya shiga masallaci ya fara jero nafilfili , yana roƙon Allah ya bashi nasara akan manufar sa ya kuma rufa masa asiri ya kawo masa warwaruwar al'amuran sa a sauƙaƙe , "toh ameen,"

ALƘAWARIN UBANGIJI ( MATAR MUTUM DAGA GARE SHI TAKE )

Da misalin ƙarfe goma na safiyar ranar Alhamis ɗin karshen sati ,  ƴan tsirarun mutanen da prof ya ƙira na cikin unguwa da basu wuce goma ba tare da wasu ƙarin mutane biyar da youssouf ya kawo a matsayin wakilan sa wanɗanda a zahiri abokan aikin sa ne daga ƙasar su , suka haɗu suka shaida ɗaurin auren FATIMA DILMARI , tare da YOUSSOUF ABDUL-AZIZOU BASKORE , wanda ya sauya suna zuwa youssouf Garba Malbaza Uzine,

Bayan ɗaurin auren babu ɓata lokaci su abokan aikin youssouf suka yi komawar su domin ɗaura shirin tashin su zuwa Abuja inda zasu wuce ƙasar su ta jirgin sama a yau ɗin ,, 

da shi kuma youssouf ya shigar da neman iznin a bada mota guda cikin motocin su na soji tare da direba da zai tuƙa su zuwa Niamey ta hanya , ba'a tsananta bincike ba aka bashi izni tare da shaida masa ya tabbatar ya samu isa niamey kafin ranar litinin inda za'a yi bikin dawowar su tare da yi musu ƙarin girma ,

Hajja me wurya," ita ce dattijuwar da prof ya zaɓa a matsayin wacce zata raka fatima ɗakin mijin ta daganan ta gano garin da zasu zauna a niger , kasancewar ita hajja mai wurya dattijuwa ce da a ƙalla ta tasamma shekaru hamsin , sannan kuma a halin yanzu bata da wani jigo cikin rayuwar ta iyaye duk sun mutu dangin kuwa kowa ta kai ta kai yake sannan tun asali bata da haula ɗan ta ɗaya ne tal da ta haife shi a shekarun girma bayan aure auren da tayi ta yi domin neman haihuwa ,

tana tsakiyar fara cin moriyar É—an nata da ya É—an fara tasawa shekarun sa ishirin da huÉ—u , Æ´an tawayen boko haram suka shigo har gida suka yanka mata shi , a cewar su yana zagin su tare da sukar akidar su , dan haka suka kawar da shi,

Tun daga nan rayuwa ta fara yi mata wahala , ƙunci da talauci suka dirar mata , zamani ne da kowa yake gudun wahala ba'a duban zuminci , tunda ta fahimci haka ta daina yin raragefe gidan ƴan uwa ta bazama neman na kan ta sanin da tayi da ɗan sauran karfin ta bata zama ƙarƙashin dangina ana zuba mata sharar walakancin ,

aikatau ta fara a gidajen saida abincin ,kasancewar ta gwanar girki iri iri ,musamman ma na ƙasar camaru da tayi farkon zaman auren ta a chan ,  amma sakamakon tsaurin ta da kuma tsayuwar ta kan gaskiya ya sa ba ta cika daɗewa a wajen aikin  ake sallamar ta , saboda bata zuru duk ta ga zalau sai ta tsinka ," 

daga baya ta koma aiki a gidajen masu hali nan ma gida biyu tana barin aiki saboda yadda take gwadawa uwargida iyakar ta a cikin gidan ta idan har ta ga abunda bai dace ba,  sai fa wannan karon da tayi dace ta samu aiki gidan Professor Mustspha dilmari 

Allah ya tsawaita zaman ta a gidan da taimakon tarbiyyar yaran gidan da basu cika raini da walakanci irin na sauran Æ´aÆ´an masu hali takwarorin su ba , babu kuma matar gidan shekaru biyu take nema da fara aiki a gidan a matsayin mai yin girki , musamman ma na shi prof .

A jiya da prof ya ƙira su ita da falmata ya faɗa musu hukuncin da yake ƙoƙarin yankewa har ma ya tuntunɓi ita falmata akan jin ra'ayin ta , ta amince zata auri baban ƴar da take riƙo su tafi ita da shi da ƴar chan ƙasar sa ko kuwa ??

Ga mamakin sa ba tare da shayin kome ba

Falmata ta amsa da ta amince zata auri baban baby ya tafi da ita tare da baby , 

  Ƙwarai prof ya ji daɗin amsar Falmata domin da farko har yana fargabar ko yarinyar zata ƙi gatan da yake son yi mata na aurar da ita tunda ƙuruciyar ta , ga mutumin da yake iya hango nagartar sa a cikin yanayin sa da mu'amalar sa , yana hasashen mutum ne na ƙwarai !

A sarari ya nuna jin daɗin sa tare da yi mata addu'o'in samun nasara a rayuwa , sannan ya juya ga hajja mai wurya wacce ita ma take durƙushe daga gefen falmata ,

Hajja Alfarma zan nema a gurin ki akan ki raka fatima É—akin mijin ta ki gano min wajen da zasu zauna ita da mijin ta a chan niger É—in daga baya sai ki dawo. Da fatan zaki min alfarma ?

Dariya hajja me wurya ta sa !
Chapter 109 · 0% Book details