← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 269

Sashe 1

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[6/24, 9:46 AM] +234 701 013 7848: Fikrah writers association 

*MAFARI* .....
              ( _HARGITSIN RAYUWA_ )

*Umm'muaz*

      

بِسْــــــــــــــــمِ اللَّهِ الرَّحْمَ
الرَّحِيْم.......

*In The Name Of Allah, The Beneficent, The Merciful.*

*Da Sunan Allah Mai rahama Mai Jinƙai* .

  

_MAFARI...komai yana da farko, komai yana da tushe, komai yana da asali, HARGITSIN RAYUWA kan faru cikin kankanin lokaci_ .

_Duniyar daka saba da ita zata iya birkicewa zuwa baquwa a gareka cikin kankanin lokaci._

_Tafiya mabanbanciya da sauri, a cikin kaddara da dai-daito._

              1

*SHIMFIÆŠA*

Ƙauyen Mairambiri , wani ƙauye ne , ko kuwa "ƙaramar Alƙarya" da yake tsakanin ƙananan  hukumomin bama da konduga, wanda suke a karkashin jahar  ( BORNO )
Mutanen garin mafi akasarin su barebari ne " kanurai", sai kuma shuwa, da fulani, tsilla-tsilla, babbar sana'ar mutanen garin shine noma, suna da makarantun primary da secondry na gomnati, sai  kuma makarantun allo da mafiya yawan yaran garin  shi suka fi zuwa ,tsiraru ne suke zuwa bokon da suke kira karatun "Malam nasara", kasancewar garin nasu yana tsakanin manyan-manyan hukumomi biyu ya sanya suke da kasuwar su a bakin babban titin da yake tsakanin garin bama da konduga" wacce take ci duk ranar Alhamis.

                       **************

Cikin wani ƙwarababben gidan kasa , wasu yara ne su uku mata,  suna cin wani zazzafan damalmalallen tuwon hatsi miyar kuka shar cikin wani tsohon kwanon da duk lamba da tsatsa suka gama munana shi , babbar baza ta wuce shekaru 16 ba ,sai ta tsakiyar me kimanin shekaru 14, sai kuma ƙaramar su me kimanin shekaru 8.

Cikin nutsuwa babbar ta ke kai lomar tuwon bakin ta bayan ta sanyawa ƙaramar su ita ma a bakin ta ,saboda zafin tuwon ta kasa sanya hannu taci ,"alama yanzu aka sauke dumamen tuwon daga wuta "duk da yanzun farar safiya ne ko 6:30am bai cika ba.

Wata doguwar mace siririya me ɗauke da wata irin farar fata sol-sol kamar ta so ta zama zabiya " Albinism" dan hasken ta yayi irin nasu, wacce da ganin ramar da take da shi na tsabar wahala da talauci ne ,tana zaune kofar wani taƙwarƙwasashiyar rumfa da alama madafi ne ganin yadda duhun wajen yafi na ko'ina a gidan, hannunta riƙe da wani jariri namiji kansa tanƙwal da aski , ta ciro yamushashen siririn maman ta tana kokarin cusawa yaron a baki shi kuma daga ya kama yayi tsotsa ɗaya-biyu yake sakewa ya cigaba da tsala kukan da yake da alamun yunwa ce ke addabar sa .

Wani baƙin dogon mutum ne, ya bullo daga bayan durkusassun ɗakunan nasu guda biyu ,hannun sa rike da babbar robar ruwa (table water ), wacce aka yanke daga wuyan ta zuwa sama gefen ta daga kasa yana ɗan ɗigar da ruwan ciki daidai inda ya ɓule aka toshe da bakar leda .

Duƙawa  yayi tare da   wanke baƙaƙen kafafuwan sa da suke sanye cikin waɗansu ratattakakkun silifa (da guntun ruwan )  ,ya ɗago tare da kallon sashin da ƴaran nan suke zaune ya ɗan ɗauki wasu daƙiƙai yana kallon su cikin nazarin yadda babbar cikin take ta ciyar da kannan nata domin ya zuwa yanzu dai su duka biyun ita take sanya hannu tana zaƙulo tuwon da ya dilmiye cikin tsululun ruwan miyar da ta haura tuwon yawa har ta shaa kansa ,tana zaƙulo shi sannan ta hura iskar bakin ta ta gutsurawa ɗayar a hannu ta sanyawa karamar sauran abakin ta ,
kuma a take ta sake mayar da hannun ta cikin kwanon da hanzari tamkar dai ita bata jin zafin tuwon .

Yakaka " _nyidin biri bun" baa ? Duwan "bii lanyen wande kausuzuin_ (yakaka ke baza ki ci abincin bane ? Kiyi sauri ki ci mu tafi kar rana ta yi ) cewar wannan mutumin ga babbar É—iyar ta sa da ya kira da suna yakaka cikin yaren su na " _KANURI_ .

Amsa masa tayi da "toh" ,dai-dai lokacin da ta miƙe da hanzari ta zagaya ta bayan matar nan da hasken fatar su yake yanayi ɗaya da nata ,ta ɗauko wani bakikkirin ɗin tiren kwano da yayi fatsa-fatsa da lamba ta nufi fasashiyar randar su da take binne a kasa sai iya fasashen bakin ta ake gani a waje "wanda za'a iya zaton rami ne"  ta sunkuya tayi goho ta kwarfi ruwa a chan kasa ta ɗauraye farantin ,

Ta sake kwarfo wani  ruwan a cikin bulalliyar moɗar da ta sha liki da leda , cikin gudu gudu ta je ta juye tuwon a kan farantin tare da ajiye musu ruwan , har ta yunƙura ta tashi ,sai karamar ta riƙo hannun ta ,a hankali ta ɗago idanun ta ta dubi kanwar tata wacce idan aka dauke kamanni irin na jini , da kuma siraran zane ( _Shunkurai_ ) da yake kan fuskokin su guda tara-tara "wanda yake bayyanawa a sarari daga ƙabilar da suke na barebarin usul " bayan hakan kowaccen su kamannin ta daban ne ,

Babbar su tana ɗiban yanayi da uwar su "watau fara ce sol yanayin hasken mutanen da suka so zama Zabiya ( albino ) yayin da ta tsakiyar take da rangwamen hasken fata ,karamar kuwa baka ce sosai kamar mahaifin su , Da alamu dukkanin su dogaye ne samɓala-Samɓala duk da cewa suna kan shekarun kuruciya sosai "yara ne " .
Cikin yaren su  karamar ta cewa babbar ta kawo mata gurji daga gona, shafa kan ta  tayi cikin nuna kauna tace zata kawo mata daga haka ta juya ta nufi ɗakin su tare da sako wani ɗangalallen hijabi cukurkuɗaɗɗe yagagge bakikkirin da shi ta kuma zagaya bayan ɗakunan nasu ta ɗauko wani buhu da alama abubuwan bukata a gona ne a ciki.

Duk abun da ake mahaifiyar  su  tana zaune bata umm "bata a ah ,sai faman girgiza jaririn ta take da sigar lallashi "shima fari ne sol irin ta amma  ita fuskar ta babu zane irin na ƴaƴan ta ga alamu ita ba babarbari bace , kamar yadda yaran da mahaifin su kana kallon fuskar su zaka shaida yaren su .

Sun zo zasu fita ita da mahaifin su  mahaifiyar  su ta miƙe ta rako su bakin zubabbiyar katangar da baza'a  ce mutane na rayuwa cikin zagayen ta ba , a bakin labulen tsunman da aka kare wawakeken giɓin da ya kasance mashigar gidan ( ƙofa ) , ta tokare sannan ta ɗaga hannu cikin maganar kurame tana musu alamar a dawo lafiya ta hanyar jujjuya tafufukan hannun ta ( _bye-bye_ ) tare da yin gwalatu cikin maganar bebaye," wanda hakan shi yake bada tabbacin KURMA ce "kallo ta bisu da shi fuskar ta ɗauke da murmushin da sai ita kadai ta san dalilin yin sa a cikin wannan yanayin da su ke ciki" .

Sun dauki tsawon lokaci suna girbi cikin ƙatuwar gonar su da take wajen gari ,Suna hirar su da kana ji kasan akwai soyayya da shaƙuwa me karfi tsakanin uban da ƴar sa kafin lokacin da yakaka ta cewa mahaifin su zata je kama ruwa (Ban ɗaki )  , ta juya gami da shiga cikin dogayen shukokin masarar da suka fidda kai suna jiran girbi , tana tsugunne cikin duhun gonar ta fara jiyo kabbara tare da iface-ifacen mutane .

Ta miƙe da sauri tana sanya ɗan kanfai (wondon ta ) , lokacin da taji mahaifin ta yana kwala kiran  neman ta da sauri ta nufo wurin da taji muryar sa , ita ma ta buɗe murya tana kiran sa tare da shaida masa ta dai-dai wurin take , wata razananniyar karar da taji tare da sake kusantowar kabbara da hayaniyar mutanen nan shi ya sake sa ta ruɗe .

Duk da bata san bindiga ba a zahiri amma tasan karar nan da take ji na abu me cutarwa ne , har zuwa lokacin da taji muryar mahaifin ta cikin ƙaraji yana cewa ta kwanta kar harbin bindiga ya same ta , ai sai ta sake ruɗewa ta nufo inda ta ji muryar sa cikin gunjin kuka da kiran sunan sa .

Shi kuma jin ta nufo shi ya sanya ya miƙe daga kwanciyar da yayi dan gujewa harsashi ,ya nufi inda yake jin kukan ta cikin tsoron kar harsashi ya same ta ko kuma ƴan tawayen su ganta su harbe ta ko su tafi da ita ( kamar yadda suka samu labarin hakan na faruwa a sauran garuruwa da ƙauyukan borno *ƳAN TAWAYEN BOKO HARAM* sun addabi mutanen ƴankin arewacin nigeria musamman jahar Borno da kewayenta wanda a nan mafarin abun ya ke. ) yana miƙewa yayi taku ɗaya biyu a na uku yaji kamar wani abu me karfi ya wuce ta jikin sa ya ɗauke shi yayi jifa da shi , yaji jikin sa kamar ba nashi ba .

Dai-dai lokacin da Yakaka ta ci tintiɓe da shi da sauri ta sunkuya gami da kamo shi ihun da ya ga ta sa tare da daura hannun ta akan kirjin sa yaga ta ɗago hannun na ta face-face da jini, shi ya tabbatar masa cewa harsashi ne ya same shi ,a take ya fara salati da karanto ɗukkanin addu'o'in da suka zo kan sa a lokacin  .

Ita da kanta baza ta iya kiyasta tsawon lokacin da ta É—auka a zaune rungume da gawar mahaifin nata , wanda tun bayan da harsashin ya same shi bai sake ko minti goma ba ya rasu . ( *Yaa Allah ya jikan dukkanin Æ´an uwa musulmai da suka rasa rayukan su a sanadin annobar Boko haram Ameen* )
Chapter 1 · 0% Book details