← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 206

Sashe 99

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nur tay kamar bataji ba tama shareta har saida Janet din ta fita takama hanyar sashen javeed kafin nan tay wasu nazarin tace ma naima kije kice mata ta dawo nan.

da wani irin sauri naima ta mike tana godiya da gudu ta kira janet wanda har hawayen datake dannewa tun jiya ya sauko mata..

naima tace hajiya tace kizo yanzun nan

janet ta share tsillin hawayenta jikinta a sanyaye ta biyota suka taho.

har lokacin nur na tsaye tana tunanin nata rayuwar, yadda ta taso yarinya me ilimin addini, tarbiya na abun kwatance kamun kai ga shiru shiru bata san ma me ake kira da rashin kunya ba bare amsa magana wa babba amma with time duk saidata zubar ta aikata wasu abubuwan da ita kanta saida tay tuhume kanta da samun tabin hankali

in all of these ta gama lura cewa komin ilmi da kwarewa da kuma nitsuwarka akwai wani lokacin da zaka iya tafka wani rashin hankali da sokonci wanda ka cancanci ayi maka duk zagin duniyar nan sabida kayi abu marar kyau. amma fa game cikkaken hankali da nitsuwa yasan hakan bashine zai saka ayi amfani da moment na rayuwarka guda daya ayi measuring ko ayi condeming din efforts dinka na baya gabaki daya dashi ba dan hakan ya kaucewa Adalci ya kuma sabawa koyarwan Addini sabida shikan sa gyara da nasiha da jan hankali duk suna da cikakn ladubansu a musulunci, dan ba ayi da zuciya, ba ayi da zafin kai, da kuma kakkaursa lafazi, anayi ne da tunani me zurfi da horarsawa, da kuma tuna in irin abun kaima tazo ta sameka agaba ko wani naka toh yaya zakayi??

janet tana dawowa nur ta rufe idonta tay mata fada ta kuma gaya mata cewa tay wawanci da sakaci me girma akan aikinta amma tunda wnn ne na farko kuma ta gane ta amshi laifinta zata bata wani dama har ta jawo mata wani hadisi na manzon Allah dake cikin ibn majah hadith number 4251 dake koyarwa kowani cikakken musulumi da ya zama me nisan tunani da gabatar da sharhi cikin tattausar lafazi. idan kaga kuskure awajen wanda is sincerely remoseful ko is willing to repent toh amatsayinka ma musulmi anaso ne kayi understanding dinsa snn ka zamo very supportive domin wnn shine koyarwar manzon Allah S.A.W.

Har kasa janet ta tsuguna ta gode mata tareda dada jin tsarin musulunci ya kara burgeta, lafuzan nur yasaka sosai taji wani abu ya ragu mata aranta atleast her efforts where not compltely condemed just bcos of one single mistake wnn kmr wani babban dama ne agareta na kara jajircewa akan tsaro da saka ido da kuma daukar babban darasi akan mutane irinsu simran.

bayan an gama da wann
nan suka fara tattauna yadda zasu saka simran tay admiting na lefinta da bakinta sabida su samu shaida akan hajy zubaida nan gaba duk dama nur ita ba wanan take hanga ba tafison taga taci uban simran tay mata abunda kwakwalrta bazai dauka ba cos how dare her??ita ranta sosai ya bata cewa simran tay wasa da ran javeed ne dan kawai ta mata sharri tasaka a walakantata.

cikin kuskus suka gama shirya abunda zasuyi tace ma janet ta koma bakin aikinta snn ta nemo mata Air bag, ita kuma naima in lokacin daukr fansa yay tazo da scizzors.

***
Bayan nan kowa ya koma bakin aikinsa normal janet tana jin abun aranta amma dai batace ma javeed komi ba sabida nur tace mata karta fada komi tukuna sai tay tunani.

wajajen 9:00am na safen lokcin nur ta gama shirinta tsaf ta saka wani plain saki material custard yellow aka mata dry natural make up irin marar lip gloss din nan tay kyau kamar amarya, tasaka wani golden cover heel na valentino garavani snn ta yafa wani karamin golden veil shima irin kalar talkaminfa veil din kamr chantilly yake amma kuma material na turkey ne me mugun tsada.

tana zauna agaban madubin kenan naima tana gyara mata zaman abun wuyan gwal dake wuyarta sai ga aika daga javeed cewa ta fito nan da 20 min zai kasance a waje yana jiranta domin suje karyawa.

Duk da wani irin dadin dataji ya lullume but cewa dayay wai zai tsaya awajen ya dada karya mata zuciya watoh dai shi sarkin pride da ego irin tunda takoreshi a dakin shi bazai sake shigowa ba hmmm..

tunda taji zaizo saida ta kara tabbatawa cewa fuskarta yay masifar kyau agabn madubin.

Ata dayan fannin kusan kowa ya shirya amma dake 9am sai ba afara fitowa ba

simran ce cikin wata shiga ta girgio armani suit wandon ya wani irin dameta ta saka wig dogo kai babu marabarta da arna ta dauko wani labcoat fari ta rike waita shirya zuwa aiki dan tasan tsoron janet ma kawai bazai kyaketa ta iya zama agidan yau ba

tagama shirin kenan ta debo kafafunta tazo dakin hjy zubaida tafara tambayarta abunda ake ciki nan hajy zubaida ta labarta mata cewa ai taje ma ta same janet din tay gaslighting inta ta komar da lefin dukan kanta bata tsammanin zata kara dago maganan sabida tamata barazana sosai

wani irin tsallen murna simran tay ta rungumeta yaa zuby ohh my goshhhh thank you ure best sister in the world and i promise u bazan sake miki irin haka ba

da wani irin harara hajya zuby tace ke dalla matsa can Dakikiya kawai..ki rasa ma wanda zaki yi dashi sai janet? ke wai baki da brain din yin tunani ne ai dama ita amaryan javeed din kika tunkara da wnn makircin kai tsaye amma dan hauka kika kama janet dake ke bakisan cewa duk wanda suke zageye da javeed makisa bane. u have no idea mata wawaye irinki nawa janet ta binnesu da ransu tsabar karfi da mugun zuciyarta yasaka aka dakatar da ita daga base na sojojin boader snn aka kaita Rehab, daga nan aka kawota aikin kare rayuwar javeed mufasa bawai dan kin ganta anan abanza tana binsa tana masa aikin gyaran daki tana masa girki ba ki dauka itadin jakace kamarki wanda batasan metake yi toh nikaina na mata barazanar ne amma idona nakanta dannasan wllh janet

bazata kyaleki ba.

Wani irin tsorataccen hadiyar yawu simran tay sai batace komi ba dan dama jikinta ya jima yana bata cewa mr aqeel, na'ima da kuma janet duk cikin ma'aikata sune kawai suke mata abu kai tsaye kamar basujin tsoronta tunda yau tasan janet soja ce tasan hala wata rana zaa ce mata naima special agent ne it feel like they is too much undergrond secrets in this mufasa mansion.

duk a tsorace take amma tacije ta kaucar da abun akan fuskrta batace komi ba ta jira hajy zubby ta gama cakkara daurinta data saka na wani mayen code lace na soltis of london baki da ash sai walwal kake gani wasu manyan gwalgwalai na gwal na haskawa a wuya da hannunta taci wani uban kwalliya.

9;28am dot javeed ya karaso sanye da wata neat dark blue kaftan ajikinshi datasaka ya zama soo calm and irresistbly handsome

shigar datay na kamala har da lullumi sosai yay dede nashi shigar na jumfa ta samesa a waje yana kan jiranta da sabon salon girmamawa ta gaisheshi ya amsa yana mamakinta duk dai ta kasa dauke ido akansa shima kuma taga satar kallonta kawai yakeyi amma yake basarwa kadan kadan.

hannunta cikin nashi suka shigo falon lkcin su anty suad duk sun fito ita da lady sidd da alhaj attah, suna yin sallama ko numfashi matayen basu barsa yaja mekyauba suka rufeshi da ya jiki? ya jiki, da mamaki nur taji basu gaya mata wani baqar magana ba infact basu sake sun dago zancen jiyan akanta ba.

tana gaishesu taga bason kulata sukeyi ba sai kawai ta koma gefen alhaj attah ta tsuguna takara bashi hakuri akan abunda ya faru jiyan shikuwa sai albarka yake saka mata yana dada kwantar mata da hankali.

sosai anty suad ta kulu ganin nur batazo gabanta itama ta bata hakurin ba duk ransu sai ya dawo kan hakan kuma suka fara bambami ciki ciki. har aka kai kan dinning table da aka cikesa da abinci kala kala dat are soo sumptious and well seasoned with clinical precision ba tarin junks ba.

ana zama sai gasu simran yaune karo na farko da suka yi latti lady sid tanata tambayarsu hajy zuby tace ai simran dinne bata jin dadi shiyasa ma jiya bata fito ba kwata kwata.

da wani irin kinibibi ta gaida kowa sai kuma tabi tahau yima javeed jaje tana cewa ya jikinsa bayan kowa yasan bata wajen jiya da abun ya faru..

anty suad dake da shegen kwakwala aikuwa ta kasa hqura ta tambayeta ya akayi ta sani

caraf hajy zuby ta amshe maganan tana washe baki tace ai da safen nan ne ta gaya mata komi.

da uhmmm kawai anty suad ta kashe maganan aka fara cin abinci javeed na kusa da babansa nur tana kusa da javeed dinta

Dan kadan kadan yake taunawa kamar me koyon cin abincin dayaga kuma nur ta dan bata rai tana satar kallonsa sai ya faraci da dan yawa ana hira kadan kadan atable din shidai baice komi ba har gara nur in alhaj attah yayi da ita tana amsawa.

abazata wani abu ya shake masa wuya tari yadan kufce masa marmaza simran ta dau glass din ruwa tahau zubawa zata miko mai saidai kafin tagama nur ta dauki nata na gabanta ta mika masa tana dan cemai sorry kai tsaye yace mata tabashi ruwan abaki tukuna

hannunta tasaka abayansa tana patting kadan snn ta fara bashi ruwan abaki yana karba

simran ta tsaya cak da nata ruwan a tsakiyar jamaa tana kallonsu ayayinda suke tamfasa rashin ta ido, ga tulin abun kunyar datayi dayabi ya isheta har bata iya motsi ba saida hajya zuby ta mutsineta da karfi snn tabi tazauna da ruwan ahannu ahnkli cikin sadda kai kasa.

sanyin muryan nur ne ya ratsa table din tana kallonsa kamr ranta tace mishi "are you okay?cikin lumshe ido da budewa yace "i am okay baby, thanks.

da wani irin mugun uncontroble borin kishi me tafasa zuciya simran ta tashi very coldy tabar kan table din wanda atake wani irin silly coments ya fara tasowa awajen kadan kadan
Chapter 99 · 0% Book details