← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 206

Sashe 13

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaj ya juyo yace hmmm toh ai antynka suad da ita kanta ancestral mother suna tsammanin zaka kawo mata daga ahali me girma da kuma mutunci and hence they have made a list of famous families da zaka iya dauko matar aure aciki, but i wll ignore it for now sabida ina so naji ra'ayinka ...what did u have in mind? tun be amsa ba ya juyo cikin kuresa da ido snn yace javeed, wacece wann yarinyar, snn daga wani ahali take..who is her father...?.
.
[23/04, 23:03] Anne-Aurora🦋: EPISODE7🦋
Dadai javeed yabude baki kenan zai amsa cikin tsaresa da ido baban nasa 'yace the girl's name is not what interest me, menene asalin su??nan javeed yamike tsaye with that cold signature pause dake mugun karamai wani salo na kwarjini ya kalle baban nasa very calmly snn yace Dad,i am talking about the Family of Al'QADIS na zaria, lineage dinsu na zuriar jinin Al'khadi muhammad ciroma.

da yanayin gamsuwa Alhaj attah ya gyada kai snn yace mmmm "okay,........and the Biological assets?..

javeed ya dan yi shiru sai can yace Dad ynxu dai progeny biyu ne kawai suka rage suna zaune duka ahannun Alhaj abubakar ciroma

atake baban nasa yajuyo yace and which one wears ur interest acikinsu ina nufin wacce ce surkuwan tawa.

Daga jikin banqo wani mugun bugu kirjin hajiya zubby yakei dan har wani tsayawa cak numfashinta yay tana jira kawai taji javeed ya fito fili ya ambaci sunan yarinyar..

dan tsabar kirjinta na tafarfasa har wani rawa rawa jikintan yakeyi shikadansa.

dan shiru javeed din yay cikin aiyana wasu tunani aransa duba da shidin kwararren jami'in millitary pol. intellingence ne, ya sani sarai the walls has ears, gashidai nan din gidan ubansa ne amma kuma har cikin ransa yakeji bazai iya tafka kuskuren kama sunan nur firdaus a fili wa mahaifinsa bawai dan be yarda dashi ba saidan sabida tsaro don har aransa ji yake duk wanda ya kuskura yay mafarkin yunkurin taba masa yarinyar can bazai barinsa lafiya batare da ya masa mummunan lahani ba

numfashinsa ya saukar kasa wrapped in calculated enigma snn yace Dad ban yanke wani hukunci ba tukuna, snn bazan iya yanke hukunci akan komi ba har sai ka qamsu...but, all i know is i will marry the best one frm dat family.

cikin sauke ajiyan zuciya tareda jin dadin kalamansa Alhaj attah yace toh Shikenan. uve made ur request kuma naji idan nima nagama bincike na zan neme ka..kabani nan da sati biyu or so pls.

javeed ya gyada kai baice masa komi ba cikin ladabi ya mike tsaye cikin masa sallama snn ya kama hanya cikin sanyin kasaitacen takunsa me aji yafita daga falon cikin nitsuwa.

yana ficewa jirgi ne a sama can na jiransa dan yay ma sultan alkwarin cewa zaizo egypts ya sameshi zasu dan tattauna gameda wasu lamari ma sirrin daya shafi wani sabon aikin yan ta'adda a niger delta state daya farayi kwananan.

Yana ficewa Cikin yanayn mugun sauri da sanda hajiya zuby data labe ajikin kofar tanajinsu ta sulale tabar wajen taje can cikin dakinta dake nan kamar aljannar duniya dan haduwa nan da nan tadau tsadadden wayarta tafara kirar yar uwarta Dr Simran sai wani jeka ka dawo take cikin tsananin tashin hankali gamida safa da marwa har saida simran din ta dauka..

da wani irin masifa ta tarbeta babu shiri tafara bata labarin abunda taji javeed yau yana furtawa wa mahaifinsa game da matar aure.

tun awayar Dr simran tafara mata karamin hauka sai ihu take tana zage zage ita de sede anemo mata cikakken history na familyn al'khadi za taga wacce shegiyar yarinya ne da har javeed yagani yake considering aurenta bayan ita tana nan a raye tana famar jiransa shekara da shekaru, har ta fara tunanin ma kode itace na auren qaddarar da aka gaya musu basu sani ba..

gabaki daya ranar sun kasa samun wata nitsuwa, Dr simran already har tafara tunanin daukar hayar private investigator dan anemo mata duk wani information akan familyn khadi, dan koma wacece yarinyar she dont care, she wll deal with her har saita fita mata a harkan javeed mufasa dinta by fire by force dan bakaramin jin ita wata bace takeyi har gani take kamar kowama ai tsoronta yakeyi.

hajiya zubby kuwa tun daga wann ranar tafara kkrin shawo kan mijinta domin taji karin bayani abakinsa

saidai duk yadda ta kankanro makirci da iya magana saitaga alhaj attah ya bugota kai kamar ma a tafin hannunsa ya sakata.

farko ma yi tay kamar bata san da maganan ba, sai tana masa labe ayayinda yake waya da wanda zasu mai binciken dan kowa ya sani baya daukar duk wani abu da ya shafi rayuwar dansa javeed da wasa.

ahaka ahaka harta fara tsoma masa baki akan maganan javeed sosai, acikin satin nan kawai tambaya akan zancen auren javeed da familyn al khadi da tamasa yafi sau a kirga amma saidai kawai yayita wasa da hanklinta yanamai dismissing din magana yanamai nuna mata kamar irin be dauke abun da muhimnci din nan ba

kokuma ya cemata ai da wuya ne ma hakan yayu bayan already akwai kanwarta Dr simran, snn kuma antynsa suad tay wani list acan dan haka ko simran ko a cikin list din kawai zasu zabar masa matar aure.

tunda yafara mata wann wala wala akan maganan familyn khadi tagane cewa bazai gaya mata komi bane kawai sai ta haqra ta kyaleshi, duk dama abun bakaramin kona mata rai yay ba

sabida ta gama lura da akwai wani salo na tsantsan rashin yadda da ahalin mufasa suke nunawa bare
wanda indai kai ba jininsu bane is like no matter what you do or say kai ko tsuliyarsu kake lashewa bazasu taba aminta dakai haka nan kawai ba.

sai kuma maganan matsafiya saratu manny volkner daya dinga fado mata arai a wann satin duk sai tazama so tensed bata da nitsuwa bare sukuni.

yadda basa shiri da javeed mufasa da kuma yanayin mijinta da bai aminta da ita ba kenan da alama abunda ake hango mata na mutuwa a hannunsu anan gaba shine zai iya faruwa da ita in asirinta yazo ya tono

abun duniya ya taru yay ma zuciyarta mugun yawa kirjinta kamar ma zai fashe haka take ji, ganan simran ta harxuka ta kasa haquri tafara neman suwaye ne yan mata biyu dasuka rage a familyn alkhadi dan ta fara da su...

******************

Bayan sati biyu ana neman shigewa na ukun ranar talata da sassafe Nur firdaus ta fito cikin takunta me sanyi dakuma nitsuwa daga cikin hadadden princess theme bed room dinta tanamai sanye da wata mayyar doguwar riga mai launin calm burgundy colour wanda ta hade da golden colour veil datay rolling akanta neatly sai wani classy rayban sun-glasses data kwamashi das das a idanunta wanda already babu wani designers logo din ajiki yay mata mugun kyau kuwa dan shape dinsa rectangular ne fari bame duhu sosai ba.

tsadadden Wayarta na hannun damanta, sai kuma hadadden golden colour side bag dinta na original balmain shima bamai tarkacen design ba amma mai tsada wanda ta rataya a kafadarta wani irin nitsatsen qamshin turaren bold rasasi me hade da launin creed aventus ke bibiyarta

bawani kwalliya tay me yawa ba amma kalar kyaun datay kai Duk wanda ya ganta sai yakalle ta sau biyu.

a cikin sabon kwarjini da annuri ta sauko falo inda ta samu duk matan gidanne su biyu zaune sun hallara wajen breakfast,acikin nitsuwa da sanyin aji takaraso takara musu wani sabon gaisuwar
snn tace musu ta gama shirinta zata wuce Abuja. babu yadda basuyi taxauna suci abinci ba amma taki sam sabida sauri da take zataje abujan domin tay represnting din kawunta alhaj abubukar ciroma da already asatin nan ya wuce dubai urgent business meeting.

jiya da dare sukay waya dashi ya mata bayani akan tunda razia nakan rubuta exams dinta kawai itace zataje abujan ta wakilceshi awani taro na humanatarian conference of United nation international children emergency fund da ake shiryawa yara da suke fama da childhood trauma and porvety...

Duk sauri datake sai da hajy bilqis ta mata box up na kananan chops bayan sun mata addua snn ta wuce dashi filin jirgi

Humanitarian Conference da hukumar UNICEF da wasu kungiyoyi suka shirya kowa yasan Wannan tafiya ba karama bace, kuma wann ne karonta na farko da zata yi ita kadai kuma cike da kwarjiini da kwarin gwiwa da familyn kawunta suka bata,

gashi bakaramin bude mata idonta kawayen razia sukayi ba. they made her believe cewa takai duk yadda take zato, and she have nothing or no one to fear. barin ma da molly ta riga ta koya mata yadda ake magana acikin taro dan haka duk dama fitan ta na farko kenan ko alaman wani dar dar bataji acikin ranta ba.

wani sabuwar confidence dinma yana zuwa mata ne daga yanayin yadda yanxu taga tasauya makanta takara zama wata first class babe me shegen aji kuma kyakwwan gaske koinanta fess koina ajikinta yana baza kyalli da qamshi

saiyanxu take dada yarda da cewa looks dinka, skin care da yanayin dressing dinka tabbas yana kara maka jin dumbin karfin gwiwa a mind dinka.

koda ta shiga jirgi a sashen first class take zaune sitting pretty elegant ko inata a killace yake gashi time to time tana dan mika hannu tana sipping green juice dinta a glass cup very calmy ayayinda take karanta debfriefing package na taron acikin pdf na wayarta acikin nitsuwa.

fadin yawan idanun hadaddun maza dake yawo akanta awajen bazai girku ba amma ko saudaya bata daga ido tama kowani da namiji kallo daya ba dan haryau dai data duba bataga namiji wanda yay mata kusa da haduwa irinna javeed mufasa ba...

akoyaushe fuskarta acike da kwanciyar hankali yake saidai wani bin zuciyarta na bugawa da irin girman da rayuwa ke son bata da wani irin hopeless tunanin datake yawan yi akan javeed mufasa

hmmm mutumin da haryau ma beneme ta koda awaya ba, ita kuma sai tunanin sa take as if she is going to see him anytime soon. kullum ta raya haka aranta sai taji haushin kanta data kasa iya ciresa gashi yanxu duk mazan datake ganinsu she keep comparing him to them amma haryau de bataga kamarsa ba.
Chapter 13 · 0% Book details