← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 206

Sashe 142

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ga rent inta ya kare, ga shi bata da ko sisi ga shi an bata just 2 days akan ta kawo sauran kudi...kuka kawai takeyi tarasa mema yake mata dadi dan tasan duk giginta dai bazata taba iya kiran babanta ko mamanta ba, molly tun tana rarrashinta harta fara bata shawarar cewa ta kirawo nur firdaus since she have more than enuf kuma tasan zatama iya siya mata kamfanin show din gabaki daya amma razia taki sam tace bazata iya kirar kowa ba kawai tasaka aranta cewa Allah ne kawai yake nuna mata kuskurenta gara kawai tanitsu ta nemi bashi a bank da wajen wasu friends dinta tabiya mutanen nan ta koma gida ta nemi gafarar iyayenta...

molly dataga razia ta riga ta karaya ta fara kawo batun komawa gida duk sai tausayin ta ya rufeta at same time tanajin dumbin haushin da razia tace bazata kira nur firdaus ta gaya mata komi ba after all what they have done for nur ita anata mind in gani take kamar nur ne tay abndaning din razia ai koda razia bata neme ta ba ita ya dace ta nemeta duk bayanin da razia ta mata akan nur sam taki aminta sai kusheta kawai takeyi tana dora mata lefin komi.

she dont belive dat javeed zai hana nur rike wayar kanta agidansa da har za'a ce bazata neme yan uwanta taji labarinsu ba. tun razia tana mata bayani akan yanayin tsaro da takuri dake cikin ahalin mufasan har ta gaji ta kyaleta.

kawar dr simran tana gama bawa simran labarin matsalolin razia suka dinga kwashewa da dariya suna shewa da jin cewa an rama musu cin mutuncin da razia tamusu dan har videon yadda fans suka dinga jefin razia akan stage ta turo ma simran ta gani.

washe gari sassafe simran tafarka taga babu zawon jini sai dai kuma ta rame kam babu laifi, tun da taga haka sai tay wanka dan tsabar son gulma hakanan sasaafe taje tsohon wajen aikinta ta samu kawarta Dr sukahau hirar lamarin
razia.

saidai ramar da simran din tay yasaka Labarin abunda yake faruwa da ita akan javeed ya dan fito fili

aikuwa nan da nan kawarta ta kitsa mata shawara akan suje su gwada luck dinsu suji asalin labarin meyasa javeed bai aure razia ba ya aure nur firdaus suga ko zasu samu wani abun kamawa

tun simran na jajjan baya da plan din hardai ta amince sukaje gidan razia da offer na 1million us dollars dan suji info akan lamarin javeed da nur nan ma suka samu gidan a kulle dan tun sassafe razia ta fita neman kudi

molly kawai suka samu awaya, wacce a farko farko tana jin sune tamusu kaca kaca da zagi tareda barazana takuma razanasu amma dataji sun kawo batun kudi sai tace musu zata nemesu da yamma taji dame sukazo...

aikuwa tunda taga razia ta dawo bata samu komi ba kuma gobe za'axo asake kamata yasaka tay ma razian wala wala ta fice takirasu simran
akansu hadu acikin children park da yamma.

koda suka hadun simran duk a tsorace take dake mollyn taki sam ta sake musu fuska dan tun bataji offer dinsu ba tace bazata musu wani aiki akan nur firdaus ba sai sun sakar mata like 2-3 million us dollars tunda matar javeed ne ai sunsan hatsarin dake ciki

tun suna cece kuce akan kudin yayi yawa har molly taci galaba akansu musmn ma datace musu she knw everything abt nur firdaus past and she also doesnt like her.

badon ransu yaso ba suka kawo mata kudin da ajaka da daddare

by then ita kuma ta hada musu clean report na sirrikn rayuwar nur gabaki daya dan anan ne ma simran tasan cewa all this while razia was just a cover up nur ce asalin budurwansa.

tsabar zumudi ko zafin uban kudin data bawa mollyn yau bataji ba suka dawo da file din gida duk ta kasa nitsuwa jikinta sai rawa rawa yake dan yau bata samu daman zama ba marmaza ta kira best private investigator dinta ta kara biyansa 1million us dollar for express verification of information yana kan investigation ta shirya tsaf ta kama hanyar airport aranar kafin ta iso abuja ta sameshi da yamma original file din nur har yasamu shigowa hannunta.

ata bangaren nur kuwa yau tun safe da suka farka take hada musu private dinner da zasuyi da dare wanda anan ne take shirin gayamai komi which she is hoping it will be their first intimate nite ko kuma ranar rabuwarsu in bai fahimceta ba..

tay duk wani shirinta privately batare daya sani ba, she make all the arrangemnt all the flowers and candles while suna rayuwarsu agidan me dadi dan yau horse riding da gun shoting suka dingayi atare cikin nishadi with other outdoor activities

yau tun sassafen da suka farka nur tay inviting dinsa to d private dinner and he has been wondering what is it about tunda yaga yau din bata saka komi aranta ba

ata fannin molly kuwa kasa kai kudin ma razia tay dan tasan in razia ta tutsiyeta hala zataji tsoro ko guilt tafadi gaskiya..

kawai zuwa tay ta clearing debt din snn tay settling damages tabiya rent din razia sauran kudin tay kkri ta nemi fake bank loan papers dan tay convincing raxia cewa a bank kawai ta karba intaso koda razia tazo ta biyata daga baya is a win win....

hakanan kuwa ta kammala komi razia bata dawo daga yawon neman kudi ba dan already taje kasar dubai tanata jiran wata famous muslim fashion woman sayyida hanifah abdallah wacce data ga abunda ya faru da razia marmaza tasa aka kirata saidai koda taxo she met a very long waiting list na models masu neman alfarma itama hakann dai ta zauna ga yunwa ga rashin isasshen kudi tana jiran matar nan shiyasa har yamma ya rufa yay liss bata saka himman dawowa cikin UK ba...
[11/06, 16:23] BLUE💙: Arewabooks@surayyahms

daga lagos kuwa tun Bayan isha'i nur tafara shirya kanta for the confession dinner da wani hadadden sexy hot red gown dinta me off shouldera tay kwalliyarta mai kyau ta haska sosai wanda baxaka kalleta kayi tunanin cewa cikin kwakwalrta a rikice yake da fargaba da kuma dumbin tsoron abunda take shirin furta ma javeed yau ba.

tana kammala shirinta tawuce dayan dakin inda ta gama hada musu romantic dinner
ta zauna akan chair daya sha ado da white linen da kuma red roses ,bonquets da candles tanajiran shigowar mijinta javeed dan tunda ya tafi masallaci sallahn magrib haryanxu bai shigo gidan ba.

bangaren simran kuwa sai kusan 7pm jirgin daya daukota daga Abujan ya sauketa a garin lagos, 7:40 on the dots ta iso mufasa mansion da wani irin karfin gwiwa dan tsabar zumudi ma batama iya aje file din ajakarta ba a hannu ta rikeshi kamar trophy har ta iso gidan dashi

kai tsaye ta haura sama ta samu hajy zubaida a daki jikinnta na rawa rawa wanda ita kanta hajy zubbyn saida tay mamakin ganin simran a wann yanayin uban xumudin
data jima bata ganta aciki ba.

simran ko zama batay ba tana aje handbag dinta ta mikawa hajy zubby file din bakinta har na rawa tahau zuba mata bayani frm A-to Z akan bunda ya faru batare da ta boye mata komi ba.

hajy zuby dataji kanta na wainuwa sabida uban kudin kamfanin ubansu da simran tay wasa dasu sai batace komi ba harsaida ta kammala karanta file din tass tasss snn tadau wayarta ta kira one of her trusted private investigators ta gaya masa sunan file din nur din and within 7 good minutes yay hacking source na information ya tono mata komi tuntun na news din pregnancy news na nur da aka goggeshi a internet yay verifyn mata komi tareda kara mata wasu kanun labarai....

saida taji hakan daga trusted source kafin nan ta fashe da dariya ta rangada wani irin shewa jikinta harna bari bari ta dau file din tace ma simran basuci ta zama suje yanxun nan su fasa kwai dan dama irin wann ranar take jira

yau ko mayafi bata saka ba tafice tay hanyar dakin su anty suad ayayinda simran din kebinta abaya yau farin ciki a fuskokinsu kamar zasu tashi sama dashi dan murna.

saidai tun daga kofar sashen su anty suad din simran taga hajy xubby ta kame ta kuma bala'in shanye zumudinta, atake ta sako wani kalar fuskar makirci da jimami mai tsanani

sunayin sallama ta damke file din a hannunta tay lumi kamar ba komi tazo dashi ba.

koda sukayi gaisuwa anty suad din ko wani kulawar kirki bata musu ba lady sid ne tazo harta dan jawo simran din suka xauna tanamai tambayarta inda ta shiga kwana biyu.

mafi akasari shiru simran tay dan sam bata gane kan hajy zubaida ba dan a tunaninta daga sun shigo labari kawai zasu hau zuba musu
da rawar jiki sai kuma taga hajy xubbyn tay amfani da wann daman tawani siga na daban daya mugun bata mamaki kuma ya burgeta..

bada tashin hankli ba taje har gaban anty suad da file din ta rusuna kai kamr mutuniyar kirki duk jikinta yay sanyi.

cikin salo na makirci tafara zubda hawaye tanamai cewa anty suad ita taxo ne da wata magana me nauyi akan auren javeed sabida gaskya ita bazata iya boyewa ba dan ya shafi mutunci da datajar ahalin mufasa gabaki daya..

jin antabo zancen ahali yasaka nan take anty suad ta hatsala tanamai tuhumarta akan abunda ke tafe da ita.

hjy zubby tay shiru tana sim sim yadda tasaka duk suka xaku sunason jin maganar abakinta sosai

aikuwa kamr an taba brain din simran kawai saita fashe da makirtaccen kuka tana ambatar wai a rufa ma javeed asiri tana wasu irin makirtn maganganu tana kuka

babu yadda lady sid batay dan ta gaya mata meke faruwa ba amma taki sam tana ta kukan karya kusan karamar fargaba da hatsaniya suka kunna musu a dakin inda matayen suka xafafa tambaya agaresu..

nan kawai sai hjy xubby tafara cewa ita dai da bakinta bazai iya furtawa ba dan gaskiya batason abunda zaizo ya hadata da muguntar javeed tunda dama ba mutuncinta yake gani ba kuma ubansa yana goya mai baya an maidata bakomi ba.
Chapter 142 · 0% Book details