← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 206

Sashe 93

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin datsar numfashinta nur tace ohh please to meye aciki, jibeki fa? aibaki da wani maraba da su masu aikin gidan waima ba abincin kika kawo ba tunda kin gama aikinki you can
now leave. .and hey dont u ever come to this kitchen and talk to my maids like this..

da wani irin diri simran tace oh haka ko? toh bakomi zan kuwa koya miki hankali zaki asalin sanin matsayi na agidan nan

nur tay banza da ita looking composed ta fara zuba hadadden water melon juice dinta a hadadden glass jug snn ta zuba like 4 cups more ta ta bar sauran a cikin container din

Simran sai masifa take tana cewa zata nuna ma nur iyakarta agidan nan saiga nam janet takaraso itama ta dauke kai tay kamr bataga simran ba tazo
gaban nur da ladabi tace i am here maam.

calmy nur tace mata ta dau tray din takai ma javeed daki she wll be der shortly

babu musu janet ta dau tray ta fita..

sauran daya rage ta rabawa naima faiza tabawa junior staff din da liyatu data karba da kyar ta rike sabida tsoron idanun simran dake huci kamar zaki..

in sha Allah yau ya zame miki last day na girki a kitchen din nan kenan i promise you this..

nur tay karamin dariya
cikin jan tsaki tace we will see...

tsaki simran tay a fusace ta karbi drink din hannun liiyatun ta yar akasa ta kwabar a fusace.

nur ta karaso da wani irin rashin kunya kusa da simran tace chill chief...ko haushi kikaji dan ke ban baki ba.

kafin simran ta amsa taji an watsa mata sauran juice din ajiki,

ihu tay ta daga kai ta kalli nur da fusata taga ashe wanda yake hannuntan ta watsa mata

zatay mata tsawa nur ta fashe da dariya ohh u want more? tasake daukar wanda ya rage a roban salon maida ta mahaukaciya ta kara watsa mata ajiki

ganin simran tafara ihu kamar tabbabbiya yasaka naima ta janye hannun nur sukabar kitchen din suka koma sashenta tun bayan nan basu sake sanin ya simran ta kare a kitchen din ba
[21/05, 21:36] BLUE💙: EPISODE 58
AREWABOOKS AY SURAYYAHMS

bazaka san ran nur ya mugun baci da kalar gadara da rainin da simran ta mata akitchen din ba saida suka koma site inta dan duk da na'ima tay kkarin bata haquri amma ko kadan nur bataji alaman zata sauko ba.

babban burinta baifi ta san javeed yaci abincinta ba ynxu sabida yau so take ta girgiza ma simran zuciyarta sabida wani rainin ya ragu tasan kuma cewa itama tana da kalar haukar datakeji dashi.

after like two hours da faruwar haka nur bata samu labarin ko javeed yaci abincinta ko baici ba duk taji ta damu sosai koda taje site dinsa saida taci karo da janet a kofa haka zata mata ai javeed bai isa ba bayan kuma yana ciki yanakan ayyana abubuwan dake gabansa a computersa saidai baiso ne kawai yay gaggawar bata fuska yanxu dan sosai nur ta bashi
mamaki dayaga kalar effort din datakeyi harda masa girki hmm

wanda tun yana jan aji wa girkin har ya hakura ya janyo ha cinye tass snn yace ma janet ta tsaya a kofa tace kawai be dawo ba cos he is going to be busy koda ace yanason suyi magana bazai iya ba dan yasan baida wnn lkcin yanxu

hakanan nur ta zauna da damuwar javeed bai dawo ba bare yaci abincinta...

ata fannin simran kuwa tunda ta koma sashenta da borin hauka yau ko zama batay ba tanata kulla maganganun da zata kai karar nur da shi dan gani take nur bata kai wance zata kirata karuwar gida agaban maids dinsun ba.

tun tuni kawai diri take dan hajya zubby kawai take jira tadawo daga offshore meetings a Egypt dataje wanda is just four hours flight to return a private jet so tasan da yamma haka duk tsiya hajya zubyn tadawo gida, dan yau ta riga ta rantse sai taje da case har gabansu hajya suad da lady sid takai karar nur firdaus dan araba musu raini duk a tunaninta ai yanzu itace da ragamar komi kuma kowa ya shaida.

saida yamma anrd 5:00 pm snn javeed yay wanka ya sace jiki ya fita a gidan me gabaki daya ko janet bata san inda yaje ba.

nur data gama cire rai tana zuwa tasamu har janet ta fitar da kwanokan takai kitchen wajen faiza an wanke amma dake oganta ya hanata cewa komi sai tace ma nur itama haka kawai tagani empty bata san ko shine ya dawo yaci ko yabawa mr aqeel ne ba

duk dama abun bai qamsheta ba amma dai is a bit of reliave for her tunda dai anci sai kawai ta haqura beside koma miyene yayimata ai ita tace masa bata son ganinsa dama so she os not suprise dayaki zuwan tasan lefinta ne data koresa ajikinta.

zuciyarta akarye ta koma estate dinta, daga nan taje tay wanka tasako wani irin plain blue gown inta mai kyau tay rolling da farin veil yau ko naima bata gayyata ba takai yammaci wajen father in law da evening snack masu dadi data saka chef faiza tay

tanayin sallama a sashen bakaramin dadi dataji shikadai ne ya amsa mata ba dan dama bataso tazo ta samu su anty suad.

cike da ladabi ta karaso ciki ganinsa zaune akan dadduma yana karatun qur'ani sai ta rusuna kasa ta jirashi har saida ya idda da girmamawa da kuma biyayya a muryanta ta gaishe sa snn ta bashi snack din takuma nuna masa ai komi yawuce tsakanin ta da javeed din.

yaji dadin hakan afarko amma dake shi din babbane bai wani gama aminta ba har saida ya fara mata tambaya akan snacks din, nur tay kamar bata san metakeyi ba tafara bashi labarin shirme dana girkin da takeyi acan agidan iyayenta.

yana cin snacks din yana murmushi yana kuma jin dadin hirar kamar da wasa tajawo mind dinsa akan abunda tazo da shi aikuwa yana tuhumarta batun kitchen tafara cemai ai mai aikinta tariga tace mata watace agidan nan take basu oder akan kayan food stores da management shiyasa ma ita take jin sanyin jikin yin abunda take so a kitchen

nan dai ta shigar da maganan awani yanayi datasan zai gane abubuwan dake faruwa game da ikon da simran takeyi da kayan abinci batare da ambaci sunanta afili ba.

shikuwa atake sai yaji ransa ya mugun baci sosai ganin wai surkuwan sa akewa gadara da kayan abincin agidan atake ya bari akan duk wann lefin matar sa zubaida ne amma kuma yacigaba da mumurshinsa yanajin hirar nur din datakeynshi normal amma da hikima take soka masa maganan simran aciki batare da ta ambace sunan kowa ba har tagama hirar gabaki daya.

kirar sallahn magrib ne ya katsesu tana shirin masa sallama zata koma sashenta kenan sai ga hajy zubbyn tasha wani irin lullumi da tsadadden lafaya yanayinta adan gajiye ganin nur zaune da mijinta suna magana yasaka ta dauke wuta tawani hade rai..

nur kuwa ko ajikinta ta tsuguna ta gaisheta, da wani irin harara da kallon banza hajya zubyn ta amsata ciki ciki batare da sanin cewa idon Alhji attahn duk yana kanta ba

nur tay kamr bata san ma an mata kallon banzan ba tay murmushi ta musu sallama ta wuce sashenta.

alwala kawai tay ta hau sallaya tay magrib ta zauna anan ko wani sallahn isha bata karkare ba sai ganan naima tazo tace mata ma neman ta anan falonta yanxun nan

sake gyara fuskarta tay kirjinta na bugawa amma ta riga ta rantse zata nuna ma simran iyakarta

da hijabin dake jikinta ta fito tana hango hajy zubby atsaye ta sauya taku tafarayinshi cikin yauqi har ya karaso ta samesu ita da liyatu kowa ya hada gabar da yamma ga liyatun ta kwaso dukka spare keys din food stores da komi na gidan harda sauran tarkacen abubuwan daya danganci dokoki a hannun simran sunzo da shi..

bacin rai dake kan fuskar hajy zubyyn ya kasa boyuwa dan koda taga nur din ji tay kamar ta rufeta da dukkka tuna irin azaban masifar da alhj attah ya gama mata yay mata fata fata yace kuma ta amshi duk wani keys a hannun simran in takai ma wacce ya dace ta rike su dan baiga dalili da za afara raina ma surkuwan gidansa wayo ba...

cewa ma dayayi wai ba hurumin simran bane rike keys da saka doka agidan snn kar simran din tasake taba wani abu daya shafi welfare na maaikata bada izinin nur ba duk shiyafi hatsalata dan all these year da simran keyi baiga kkrinta ba har yana da bakin cewa ai bawani ya dorata ba tanayi ne radin kanta yanxu kuma tunda akwai matar javeed shi baison jin wani magana kuma ya masifeta tasss yace mata komai lefinta ne bata san respinsiblites dinta na uwa bane agidan da wn maganan ma basai angaya mata ba.

gabaki daya batasan waya kai cunen simran gabansa ba amma kuma sosai jikinta yake bata kamr nur din ne tunda dai tare ta samesu kuma tana barin wajen ne ya rufeta da masifar

nur tadan tsaya kanta na kallon gefe kadan muryanta ciki ciki tace hajiiya gani nan.

wani tsaki mai sauti hajy zubby taja...tace ke liyatu bata duka keys din..

da ladabi liyatu ta kawo cikin jan ajk nur taki karba tama naima ido akan ta amsa snn tace hajiya wai keys din meyene kuma wann?.

Da wani irin kallon banza hjya zuby tace " nima bansani ba, Kina matsayin surkuwan gida ai yanzu kika fara rike keys..but lets see if u can hold them well tunda mu ance bamu iya ba

ahnkli nur tace uhum..

ta kalli naima tace kaisu ciki ki ajje su tukun sai nayi nazari

wani fuuuu hajya zubaidan ta juya tabar sashen tsabar ranta ya baci har bata ganin gabanta.
[22/05, 17:56] BLUE💙: EPISODE 59
Arewabooks@surayyahms.
idanun hajiya zuby a rufe dan tsabar bacin rai har ta karaso shashenta da wani irin huci ta rufe kofartan kirif.
Chapter 93 · 0% Book details