← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 206

Sashe 109

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hannunsa daya na cikin aljihun wandon uniform dinsa ya kamo hannunta suka sauko kasa duk kaga nur zaka dauka laulayin ciki takeyi tsabar tana cikin wani irin yanayin da bazata iya fassarashi.

intay masa kuka da bori toh in ya zauna mata mezata bashi?
inkuma ta barsa ya tafi tasan dolene zataji zafi snn zatyi kuka ta shiga damuwa idan bai dawo ba.

cikin wann yanayin har suka kawo falo bata sani ba sai da taji alaman idon kowa ya koma kansu snn ta daga ido taga su anty suad sun tattashi sun bar kan chairs dinsu da mamaki suna kallon javeed dake sanye da uniform dinsa

suna karasowa nur tafara gaishesu ko kulata basuyi ba hnkli atashe anty suad ta fara tambayar javeed ko lafiya ta gansa da operation uniform?

baiko amsa ta ba sai ganan su simran suma sun fito dan tun dazu tagama shiri amma dakinsu anty suad kawai taje tay musu godiya kamar yadda hajy zubaida ta tsara mata komi..

wani irin kama kanta takeyi na musammn yau duk dama babu abunda ya sauya a dabbancin dressing inta na matse kirji da saka yan iskan kaya

sun iso wajen dede lkcin javeed yanakan kore tambayr anty suad da dan banzan miskilallen attitude dinsa tareda cemusu su zauna sai anyi breakfst tukuna kowa zaiji inda zaije..

yana gama furta hakan sai ga alhaj attah ya fito yana takowa da sandan girmansa dan yau kwata kwata ba dadin jikinsa yakeji ba dake tun mutuwar matarsa haifa saddam ya kamu da ciwon zuciya amma bai bari koda dansa javeed ya sani ba bare wasu na daban aboye yake shan maganinsa all these years in ciwon yaso ya tashi masa.
[27/05, 22:43] BLUE💙: _EPISODE 68_
AREWABOOKS@SURAYYAHMS.

Dakyar alhaj attah ya bar nashi tuhuman snn aka zauna aka ci abinci saidai gabaki daya nur firdaus ta kasa tabuka komi shine ma yake dan takura mata taci ayyin da idanun matayen kaf yake yawo a kansu...

sama sama taci ba don taso ba ana daf da gamawa hajy zuby da babu abunda ya dameta da saka operation uniform din javeed tay gyaran ta sako zancensu na cewa simran zata bawa nur firdaus hakuri tay wani dan guntun nasiharta.

simran dake kallon nur din tuntuni tana jin kamar kirjinta naci da wuta hakan tadanne komi tafara magana da wani kalar makirtccen salo
tana bawa nur din hakuri akan abunda ya farun agaban kowa
saidai tanayine su anty suad suna kan yabata.

nur ta dauke kai ta maida shi gefen javeed da already yasaka ruwa abakinsa yasha kadan yana dan kallon yanayin da dukansu suke yaba simran din da gefen idonsa.

da can kamar bazaice komi ba jin nur tay shiruuu yasakashi ya kalli nur din da wata muryan lallami ahnkli yace baby kinji ana baki hakuri ko, toh if you are not okay just tell me sai kawai tabar mana gida ko..

yadda yay maganan ahnkli zaka rantse nur ne kawai tajishi, caraf sai akaji hjy zuby ta harzuka tana cewa haba javeed, dan Allah ya zakace haka yanxu in yarinyar nan bata hakura ba shikenan ita simran bazata zauna lafya agidan nan ba kenan but atleast she is apologising in front of the family members.

kusan kowa a table din kallonta yay dan babu wanda yaji me javeed yace ma nur din sai ita..

wanda daga javeed din har nur din kallonta suke da wani irin yanayin da yay embrasing inta dan basuce mata komi ba
sai duk aka dauka ko haukan simran ne yake neman itama ya tabata lady sid kuwa harda mata tayin ruwan sanyi.

Da murdadden fuska kuma nitse alhaj attah yace "kedai zubaida kinfiye saka baki acikin maganan yaran nan just let her decide dan Allah waikome ne sai kun samusu baki?
..

yana gama furta hakan ya daga ido ya kalle nur yace my doter ga nan yar uwarki tana baki hakuri but dont worry if ure not okay with that karki takura kanki har sai kin huce pls..

simran batasan sanda ta dafe kirjinta dake mata zafi kamar zai faso waje ba kawai saita sunkuyar da kanta kasa tay shiru
ganin nur bata ce uffan ba.

tsabar takaici anty suad tay kamr zata tashi tabar wajen tsabar bacin rai

can nur tay murmushi da sanyin murya tace bakomi father inlaw since she is beggin for it she can stay if its okay by you.

hawayen da simran take dannewa atake ya sauka tay sauri ta shareshi tuna ranar saida nur tace mata she will beg her to stay in dis mufasa house tabbas yarinyar nan sheidan din gaske ce.

alhj attah da baiya ko kallon simran din yace ma nur no no my doter ,baza ayi haka na..gidan nan naki ne my dear, dani da zubaida dun mun tsufa yanzu kece rabbatul bait(queen of the house), duk wanda zaizo gidan nan domin ya kuntata miki har kikace mishi bazai zauna ba toh decision dinki ya zauna.

wani irin kallo nur tay ma idon simran dake ci da wuta bal bal hawaye na saukowa kasa dan koba komi tasan cewa saida izinintan zata zauna agidan wanda dama matsayin datakeso ta daurata akai kenan

ji tay javeed ya riko hannunta ta kasar table yana murmushin mugunta kamar yana so yace mata karta amince ne oho ita bata gane mai ba..

share naughtiness dinsan tay kawai ta kalle alhaj attah da girmamawa snn tace masa babu komi father inlaw ni bani da matsala da ita she can stay.

alhaj attah yace toh alhamdullah aina san ke baki da matsala dama gaki da hakuri, toh Allah ya miki albarka my doterm

nur tana murmushi tace ameen father inlaw

sai ya kalle simran ya dan mata nasiha kadan, snn yace mata already ya samo mata therapist dan haka bai son wani abu yaje ya sameta yanaso ta nitsu tay jinyarta sosai..

ranta na kuna amma hakanan ta masa godiya da ladabi snn ya sakata a position din da dan dole sai tace ma nur din ta gode badan ranta yaso ba nanma yace musu marmaza suyi musabaha agaban family shi baison ana fada da juna.

nur ce ta fara mika mata hannu ta kama sukayi sallama cikin ran simran tafasa yake har ya kone sai tanajin kamar ta balle kawai takasheta

kamar an dauke wuta haka manyan matayen gidan sukayi tsit a table din suna kallon ikon Allah kowaccen su tanajin baqin ciki kamarma ta tashi ta kama nur da duka

musammn ma hajiy zubaida datakejin kamr ta kasheta dan wano special tsana take mata bana kadan ba.

simran tana zama lady sid tafara lallashinta har tana ce mata itace babba itace me hakuri waye waye the table turns duk wata rana dai sai labari.

tun suna kammala cin abinci hajy zubby ta dinga ma simran ido akan maza ta shanye fushinta tay acting kamr komi ya wuce

which was very hard for her amma hakann ta sake fuskarta na dole har aka tashi akan table aka koma falo just Few minutes to 11am na sfiya

nur tana tsaye kusa da javeed yay gyaran murya ya kalle babnsa bai boye masa komi ba ya fara gaya masa cewa mission zaije..

kamar yadda yay zato hakanan kuwa suka rude anty suad tana yi Alhaj attah ma yanay har gara anty nata damuwar baifi da bai gayama kowa ba yay abunsa aboye, alhaj attah kam kai tsaye yace wnn mission din sam bada yawunsa ba..

Suka dau abun da zafi amma ji ko ajikinsa nur tuni taji cece kuce dinsun ya kara sakata acikin matsanacin tsoron rasashi.

jikin simran harna rawa ta mike ta tsaya ata bayansu itama dan acikin sabbin dokokin hjy zubby ta riga tace mata inhar
abu ya shafi lafyar javeed toh marmza tafi kowa zakewa akai
hakan yana daya daga cikin stratergyn data shimfida mata ayau wanda shiyasa basu iso wajen cin abincin da wuri ba kai hatta fitowa table duk ta tsara ma simran kuma tace mata kwrta sake shiga harkan wokers na gidan harsai sun kashe auren javeed da nur me gabaki daya.

Da kyar bayanin javeed ya qamsar da su anty suad, dake itama ta mugun gajiya da hunting insu da nagasa brotherhood sukeyi dan ita kanta plotting din kashe kashen ahalinsu da nagaza sukeyi akansu yana daya daga cikin dalilin da ya hanata yima danta kamil aure hmm gara javeed shi soja ne kuma sultan yana tare dashi.

tasan idan har basu rabu da nagaza brotherhood ba abubuwa dayawa zasu cigaba da kwabewa musu a kasa kasa..

shi kuma javeed wnn chance din kawai yake duba musu dan wnn ne karo na farko da sultan ya tabbatar masa cewa gabaki daya ahalin nagaza zasu fito yin wnn business din, kuma idan suka ci nasarar siyar da yara da mata mugayen makamai zasu siya wanda koshi alhaj attah dayake borin yasan idan nagaza suka farfado da arzikinsu ahalin mufasa zasu fara kashewa a duniyan nan.

javeed yace musu wnn ne kawai lkcin daya dace masa daya shafesu tun kafin suy business din bare ma ayanxu da basu tsmnin ganinsa zai dira musu ne ayayinda basu shirya masa ba..

Da kyar suka sauko suka fahimce shi duk dama alhaj attah is still finding it hard jin ciwonsa zai tashi yay sauri ya haura sama ya barsu a falon batare da ya yarje mishi..

abazata Nur tabi bayansa da sauri sauri sabida kallo daya tamasa ta gane cewa akwai ciwon dake damunsa akirji

daga falon kuwa hankali atashe anty suad tahau kirar lambar khaleefa, kamil, da haidar mufasas awaya wai koda akwai wani abu da zasuy ma javeed na taimako duk ta daga hankalinta sosai lady sid ne take kkrin bata baki..

simran da hajy zubby basuce uffan ba sai kallon da suke aikawa junansu, simran tafara shara kwallar karya tana wani irin jan jan zuciya har anty sid tazo ta wani riketa tana bata haquri

Nur tana isa dakin ta sameshi dafe da bango har ya dau maganin ya bude ya jefa kwayar abakinsa yana kan shan ruwa yana kkrin boye robar maganin kenan yaji muryan nur abayn sa cikin haki dadan sauri sauri tace asallam alaikum, father inlaw, meya faru are you okay are you sick??
Chapter 109 · 0% Book details