← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 182 OF 206

Sashe 182

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mother ta kara jadaddawa ahalin mufasa cewa nur is like thier blood now, she wll bear the future of the next mufasa generation, dan haka dutie ne akan kowa ya kare rayuwrta da mutuncin ta, a dau fansa domin ta, sann kuma abunda zata haifa na farko acikin nan gidan za'a fara rainonshi ko mace ko namiji.

nur tana ji tana gani aka fara kirarta da lady mufasa aka nuna mata filin da zaa binneta acikin family inta bar duniya da wasu few abubuwan daya kamata ta sani.

bankwana me dadi sukayi da hjy amira kafin anty suad ta jata gefe ta dan mata nasiha itade nur duk mamakin canzawar matar takeji aranta shiyasa haryau take kafa kafa da ita

anty suad tace mata idan ta huta sosai zata nemeta daga baga sabida akwai matsayi dayawa wanda zata dorata akai musmn game da harkan ajiyan kudi da ma'adanai.

haka nur tay sallama da kowa tay musu isasshen godiya komi ya zanca mata at once, ganin all the mufasas are now treating her like blood sister.

aranta tace kawai dan ta share abun duniya ta dauki adda?...

sai ta tuna hjy amira takan ce mata abu me wuya ne wani dan adam yazo cikinsu bai nuna kwadayin arxikinsu ba shiyasa da abun duniya suke kwajin initiations dinsu, and besides mother has already see it before dan badan sunsan Nur zata zama nasu ba, da tun farko mother bazata taba gayyatar su ba. babban misali shine akan hajiya zubaida duk years datay a matsyinta na amarya ko sau daya mother bata kirata moroco ba sabida already tasani basu cancanta ba kodaga hali.

kafin azhr duk akayi bankwana da kasar moroco hajy xubaida da kamil ne kawai suka wuce lagos dan ya aiwatar da abunda zai aiwatar akan simran kafin ya tafi.

alhaj attah kuma kaduna ya wuce domin ya sanar da hajy mammy cewa nur firdaus ta zama ahalin mufasa yanxu sann ya karasa tattaro wasu abubuwa na mahaifyar javeed wanda ayanxu nur din ce xata gada.

javeed da nur suka sauka agarin abuja kusan da daddare. wani karamin zazzabi ke sandan jikin nur dan haka bata wani jima ba tay bacci haka ma yau basuyi sex ba saida asuba daga nan sukay wanka yaje sallah tare da motsa jiki ita kuma bata wani jima tana karatun qur'ani ba tay bacci.

yau adnan yake cika kwana uku anan duk ya galaibaice inda ake daureshin har yay shati yay jaaa wajajen 8.30 am na safe bai jima da samun abun karyawa ba yana daga dauren yaga an shigo da wani katoton drum

dake kansa ne ke reto yana kalllon yadda suka juye ruwan acid aciki har saida ya cika wanda duk depresion mai yawa dake damun brain din adnan sai dayaji yana neman ceto ransa da karfi kuma atsorace dan sosai ya hau tuna inda shi da abokasan suka sullebe gangan jikin sadaat acikin acid a drum wanda ko bones dinsa ba asamu ba.

tun kafin javeed ya shigo dakin adnan ya riga ya kara sakin fitsari a wandonsa..

sai firgici yake musmn da suka hade ido da javeed.

ido kawai javeed yay aka bude masa baki, nan adnan ya zunduma ihu yana cewa oga kay hakuri, na tuba wallh
nabar maka nur, oga dan Allah karka kasheni kaya hkuri oga
nikadai mamana ta haifa, indan nur ne na baka ita, dan Allah kar ka konani acikin wnn abun.

javeed bai wani kulashi ba ya nemi waje akan chair ya xauna yana kallonsa sai rokonsa yake.

shi sam baida niyyar walakanta adnan but a murder crime is a murder crime.. dole ne shiya bashi wahala anan dan inhar ya mikasa wa hukuma yasan duk yadda akay nur dinshi bazata ji dadi aranta ba

shikansa tausayi yaron yake bashi and for the fact that yaso nur amma bai taba taba jikinta ba, kuma ya tsaya mata duk rintsi duk dama sultan ya gayamai a gagguce ne amma he can still feel the loyalty.

barazana kawai yay masa da matsayinsa dan yasan cewa shi bawai mijin nur bane kawai shi hukuma ne kuma yakamashi ne sabida kisan kai da sukayi.

yace masa his freinds are next duk sai yasaka an hange su shikuma daya kawo plan din zai konashi da wann ruwan acid din yadda sukama sadaat

adnan ya dinga kuka yana rokon javeed, tsabar ya firgita bai kuma boye masa komi ba, the pain of lost, and everything is still fresh in his memory kamr jiya abun ya faru da shi.

javeed yay kamar baijin tausayinshi amma sosai ya bashi tausayi dan ya lura abunda ya faru da nur din sosai ya taba masa lafyar kwakwala

suna cikin haka mr aqeel ya shigo ya bashi report dinsu da sukayi na wajen da akay kisan, authentic reports and evrything
saida yagama dubawa snn ya kalle adnan ya karkada kai. ya bawa mr aqeel file din snn shida kansa ya mike ya kwance adnan din ya saukar dashi

lokacin kuka kawai adnan yake ya gama cire ransa ga rayuwa

hakanan javeed yace ma gurds dinsa da kowa a basu waje

suna ficewa ya tsuguna agaban adnan ya umarcesa daya dago ya kallesa suna hade ido report din ya nuna masa yace duk wani abunda ya faru aranar yana cikin report din nan,. nan ya masa fada kamar shi ya haifeshi, musmn ma game da daukar qaddara da hakuri sa rabuwa da abokan banza, snn yace masa kar ya sake amfani da fushi da zafin abunda yakeji aransa yace zai dau ran mutum. he is just lucky cewa Duk DNA na abokansa aka samu ajikin stick din da aka nitsar da gangan jikin sadaat cikin acida din amma banda nashi badon haka ba da dolene zai mika shi wa hukuma sukashe shi sabida ba ai koda sadat baida gaskiya hurumin su bane daukar mataki.

duk da haka ma javeed yay masa alkwarin cewa zai saka ayi medical report na cewa he is under mental health and anxiety dan sabida yasamu afuwa da freedoom nayin rayuwansa in return zai masa alkwarin cewa zai dena duk wani halin banza da yakeyi wanda nur firdaus tace bata so.

sosai jikin adnan yay sanyi jin wai javeed zai rufa masa asiri dan ya samu chance yay rayuwarsa normal despite abunda ya aikata..bai yi masa girman kai ba yace ya amince zai canza halin sa zai dawo yadda yake dacan amma dan Allah kar yagaya ma nur cewa yay kisan kai baison ta tsaneshi.

javeed bai ce masa komi ba cikin bude ido da lumshewa ya kira gurds aka kai adnan yay wanka suka bashi kaya me kyau. snn aka ajesa a wani daki agidan yaci abinci har yay bacci.

chan bayan azhr Nur tagama shiryawa zasu je shan iska da su janet da naima a waje kenan sai taji anata magana da sunan mrs haseena a tv, da kamar bazata kalla ba wani abu yace ta dan zauna ta gani

taga hot topic nema 2 days ago wai har ansamu gawan likitocin kuma ana tunanin sadaat ne ya kashe su,..

yanzu haka hajy mairam ta saka yan jarida suna yayata labari karya na cewa sadaat bai mutu ba dan kawai mrs haseena ta bar idda ta fito aikin siyasa tay musu amfani da wann rubibin case din yaran tan ayi program dinshi na musmamn a media dan sukara samun dumbin mabiya tunda a idon duniya yanxu sune victim ba sadaat ba.tsaki kawai nur firdaus taja bata kara kallon tvn ba suka fita wajen shan iska su naima suna bata labarai tana dariya

she look soo happy duk takara cike fatarta tay bulbul jiikinta na sheqi babu shakka zaka san cewa sperm din javeed is very very powerful dan bakaramin buduwa tay ta hips da nono ta dawo babban mace ba.

tashuwr adnan daga bacci kenan ya tsaya daga windon dakin dayaken yanata kallonta daga nesa hawaye ya cika idonsa but now he is not sad at all, ganin nur ta samu farin ciki arayuwarta ma ya ishe shi, dama can baiy deserving inta ba
Hala Allah ne ya nuna masa wasu boyayyun halinsa wanda shine amsarsa na meyasa bazai taba bashi nur firdaus a matsayin matarsa ba.

baijima a tsayen ba mr aqeel yazo da medical report dinsa
dake nuna cewa adnan yana da wani irin chronic schzorprenic mental ilness dan haka dole ne ayi sparing dinsa on the base of health ground kafin case din ya mutu. javeed ya masa haka ne dan ya ceceshi daga zuwa prison ko mutuwa

snn ya bashi cheque, na diyya daban, na kyautar kulamasa da nur dayay alkcin da baiya nan daban, sedai bai gaya masa haka dan yasan yaron da taurin kai bawani karban kudi akan nur zaiyi ba but he feel dat the boy derseves it. nur tana zaune a harabar gidan amma har aka fita da adnan a mota bata sani ba dake motar sun tinted ne

straight aka ajeshi a kofar gidansa snn mr aqeel ya bashi full adress na gidan iyayen sadaat daga nan bai kara ganin walkiyansu ba.

Babu wani abu mafi muni da abun tsoro kamar kaci haqqin mutum bakajin ko dar dar aranka littafina ba kyauta bane kudi ake sawa ake karantawa ga wanda imaninsu yakeda saura chat me and pay via 08060712446
[02/07, 16:38] Ladysu: Babu wani abu mafi muni da abun tsoro kamar kaci haqqin mutum bakajin ko dar dar aranka littafina ba kyauta bane kudi ake sawa ake karantawa ga wanda imaninsu yakeda saura chat me and pay via 08060712446

#SURAYYAHMS
jikin adnan a sanyaye ya bude gate ya karasa cikin gidansa inda ya samu koina yayi shiru koda ya duba baiga budurwasa khaleesat ba yasan hala tabi kawayenta ne sunje dubai hutu dama kuma laylah ba damuwar sa bane dan haka ko duba gefenta baiyi ba ya wuce dakinsa ya kwanta.

tunanin rayuwarsa ya wuni yanayi a dakin awani yanayi yanajin baqin ciki,wasu kuma yanasa shi yay kuka ,ahaka hardai yay making up din mind insa firmly akan wasu abubuwa dazai kawo masa canji arayuwarsan nan gaba.
Chapter 182 · 0% Book details