← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 206

Sashe 98

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk wnn abun simran bata dena kuka ba kuma batay wani tsiwa ba tana mikewa tay kneeling bisa gwiwarta ta rike kafar hajy zubby ta fara wani irin rokonta akanta ta taimaka mata tanata kuka kamr ranta zai fita

cikin kukan ta bata labarin komi datayi har da abubwan da janet din tagaya mata ynxun word by word .

hajy zuby taki sam ta kulata ta hade rai sai mita take mata
"ba laifinki bane simran bakinga kina zama acikin mufasas bane kike tunanin normal mutane ne kawai masu kudi da iko?see, they are called "mafias"for a reason..su ba irin mutenen da kika sani bane, just make one mistake with them.. and ur life with dat of ur whole generation is wiped out kamar ma bakuzo duniyan nan ba dan basu da sanayyah bare sabo.

haka suka kwana azaune in banda zaginta babu abunda tadingayi har saida aka kira sallahn asubah kafin nan simran din tay collapsing tay bacci wanda shidin ma a bazata ya dauketa bawai dan ta shirya ma hakan ba.....

Ata fannin su nur kuwa cikin wani yanayin shaukin juna sukayi bacci dan kuwa duk yadda taso tadagamai hankli daga yafarajin zai tabata sai kuma ya fara tunowa da wasu abubuwan datake kallonsa dashi..

musamn ma cewa datake jikinta kawai yake so which is actually bruising him. duk yadda taso tadaga mai hankli yau hakanan ya kwana da ita ajikinshin amma bai sake yay wani wasa da jikinta ba har sukayi bacci.

sasssafe ana daf za'a tada iqama a masjid tafarka sai ganin wayam tay bata gansa akan gadon ba kuma bai tasheta sallah ba wani abun da ya kara daure mata kan ma kayanta ne datagani wai harya maidata matashi jikinta..

tagumi tay idanunta suka ciko tam da hawaye dan tafi minti biyar maikyau bata iya saukowa akan gadon ba sai can cikin lumshe da budewa kafin ta sauko..

ranta a mugun dagule ta bude kofarsa ta fice tana tafiya ahnkli hawayenta na sauka da irin feeling din nan najin kanason abu amma an hanaka saidai bazaka iya wani abu akai ba sabida kasan kaine ka jawo komi.

gashi dai jiyan bawani magana javeed yayi mata ba he was mostly quiete ta tuna har tagama mai wanka baice mata uffan ba amma kuma shirunsa da wasu dabiunsan sosai yake aika mata wasu sakonni masu nauyi

dan yaune karo na farko datajita kusan tsirara ajikinshi but after all the body contacts amma bai mata komi ba kuma shine harda mayar mata da kayanta jiki

tana son taji haushi amma kuma tasan duk lefinta ne itace tacemai jikinta yake so
...hartakai dakinta hawaye takeyi tana sniffing ahankli.

tana shiga ta fada cikin bayin tay kuka tanamai dada jin dana sanin wasu kalamn nata kai dolene ma ta sake lalubo littafai na Addini domin ta kara farfado da iliminta na zaman aure dan inba haka ba gani take kamr wasu dabiun nata zai rabata da javeed dinta kwata kwata.

bayan ta raya hakane tay wankan da plain ruwa snn ta hado da alwala tazo tafara sallah tana idarwa ta jawo qur'aninta ta bude tafara karantawa dan ta samu nitsuwa

hajy zubaida tana idar da Sallahn safiya ko sallamar ma atsaye ta karasashi da mayafin datay sallahn haka ta buguzomo waje da tarin maganganu a ranta data shiryashi zata gaya ma janet dan sosai tay nisan tunani akan yadfa zata kashe wnn maganan cikin ruwan sanyi.

kai tsaye inda janet din take kwana ta nufa tana shiga dakin ta tasamu bata ciki tay maza ta leka baya acan kusa da hanyar sashen nur ta baya ta ga janet akasa tana kan training idanunta yay jaaa wanda kallo daya zaka mata kasan cewa ko bacci batayi ba.

Cikin sauke ajiyan zuciya hajy zuby ta karaso fuskarta babu yabo babu fallasa ta same janet din wacce tun data hangota ta gane meyakawota

tana zuwa ko gaisawa basuyi ba hajy zuby ta haderai tafara wani irin tuhumarta akan cewa tay threthnig in simran cewa cikin dare batare da wani dalili ba..

nan da nan Janet tahau mata bayanin duk abunda ya faru amma ina saima ta maida ta kamar bata san metakeyi ba irin gaslighting da blame shifting innan atake ta juyowa da laifin komi dayafaru jiyan gabaki daya ta dorashi akan janet tace mata kawai tace tay sakaci da rayuwar javeed snn tana neman tay victimizing yar uwata simran dan anga basu da gata su ba mufasas bane shiyasa ake so a daura ma yar uwarta laifi.

hakanan tajuya kan maganan tass tass tace janet tanaso ne kawai ta kufce ma kuskurenta batason ta amshi gaskiyar cewa itace asalin babban me lefi..

snn tace mata inhar ta kara matsawa simran ita gaban uban javeed din zata kai kararta in sha Allah saita tabbata anmata horo me tsanani kuma ta dena aiki agidan kenan har abada.

Duk wann barazanar be damu janet ba, face wnn manipulation da gasligthing din da suka shiga kwakwarlta sosai suka hanata cewa komi har hajya zubaida ta gama maganarta ta tafi.

waje ta nema ta zauna ta dan dafe kanta, dan tun jiya take jin haushin yadda akayi tay wann saken har ta bari hakan ya faru shin wann abunda tayin kuskure ne ko kuma babban ganganci!??
..saidai ita tsohuwar soja ce, bazata tsaya kuka ba, kuma bazata tsaya fadawa cikin tarkon barazanar ko wacce mace agidan ba,mikewa kawai tay da taurin zuciya ta koma dakinta tay wanka da ruwan sanyi snn ta shirya tsaf acikin bakin suite dinta na aiki ta fito ta zauna ata sashen nur tana jiran fitowarta.

niyyarta ta gaya ma nur komi snn taje ta gayama javeed in zai hukuntata toh, inma zai yafe, ko zai koreta a aikin duk dai ta shirya ma wannnan aranta dan bakaramin guilt takeji aranta ba.

tana zaune shiru cikin tunani da haushin simran daya cikata taji an dafata ahnkli

tana juyowa suka hade ido da naima ganin inda idon janet din yay jaaa ya cikke da damuwa yasaka naima tace " miss janet lafiya kuwa pls dont tell me ure still thinking abt what happen yestade kiyi haquri mana ai likita ma yace food allergies

tsaye janet ta mike tace no, is not naima. ba food allergies bane shirmena ne da kuma sakacina ya jawo faruwar komi...i dont think zan taba iya yafema kaina da wani abu ya same general jiya..

cikin rage murya naima tace what happen taya hakan ya shafeki..altho i have my suspiscions too amma kuma likita yace....cikin katseta janet tace "mance da zancen likita naima, ni araina ina ganin kamr wancan matar has sumting to do with it

Na'ima tay wani irin muurmushin mugunta tace yess i knew it..amma ya akayi kika gane kema?

nan janet tafara bata labarin komi daya faru daga jiyan har izuwa abubuwan da suka faru da ita yau da safe wanda yasaka sosai jikin naiman yay sanyi musmn yadda taga janet tana blaming kanta sosaiii.

karfin gwiwa ta dinga bata amma inaaa janet saidada zurfafa takeyi tanajin kanta kamar ta tafka wauta jiyan sosai..

naima tama rasa me zatace mata tace toh muje ciki wajen hajiya i am sure zata fahimce ki sai mu roketa ita tay masa magana kinga hala ma saikici albarkacin ta cikin lallami tace but janet, no body is 100% ever careful a duniyan nan, manyan sarakuna da suka mulki duniyar ma da manyan sojoji da ke kwana cikin tsaro wallh poison da kuma

makircin mace yana iya kashesu. ke kuma tunda na sanki baki taba aikata kuskure da rayuwar general ba sai akan wnn matar but my dear this is just a proof that you are not a supernatural being ure simply a human being.

janet tace hmmmmm toh shikenan naji muje amma ke zaki fara magana nikuma sai na mata bayanin komi daya faru.

naima tace babu damuwa...

atare suka karasa cikin sashen nur da sallama abakinsu duka saidai jin sautin karatunta yasaka suka tsaya tun a falonta na biyu. bayan kamr minti goma sharp Nur ta kammala karatun ta ta fito falon ta samesu jikinta sanye da hijabi

duka suka rusuna suka gaisheta cikin ladabi sosai ta amsa su babu yabo babu fallasa.

kai tsaye cikin taushin murya naima tace Hajiya wata magana mukazo dashi muna neman alfarmanki ko zaki iya bamu dama??

Nur ta kallesu duka musmn janet dataga tamata daban jikinta duk yay sanyi cikin sauke karamar ajiyar zuciya tace toh bismillah, ku zauna dama ina da magana daku nima concerning abunda ya faru jiya

nur tana zama akan kujera suka koma kasa kai a tsunkuye na'ima tace ranki dade hajya maganan da mukazo dashi kenan saboda abubuwn da suka farun da akwai ayoyin tambaya aciki

nur tace inajinki go on..

nan naima ta fara fadin duk wani abunda ta sani da kuma wanda ta gani wanda ya dada razana janet ya karasakata cikin rudani dan duk bata lura da wnn ba.

Nur tasha mamaki jin wai harma simran ta taba smoothie din da bakinta

ta kalle janet da daurarren fuska tace and what do you have to say about this..

cikin gyaran murya janet ta fara nata bayanin idonta yay jaa kamar zatay kuka tafadi komi bata boye har zuwanta wajen simran da zuwan hjya zubaida ba.

Hankali tashe nur ta mike tsaye tana kallon su duka da wani irin yanayi a fuskarta wanda bazaka cemai bacin rai bazakace mai rudani ba.

da nai'ma ta fara saidai applauding dinta kawai tay na kkrin saka ido da ganowa

snn ta dawo kan janet da masifa, tace sam wann ganganci ne da rashin kula wanda dazai jawo mata rasa rayuwar mijinta dan haka ita babu ruwanta kawai taje ta gaya masa meyafaru aishi zai gano gaskiya kuma zai san kalar hukuncin da zai yanke

Janet batace komi ba face hakuri data dinga bawa nur bawai dan ayafeta saidan tasan tay ganganci da aikinta jiya

Tana mikewa zata fita naima ta juyo da fuskar tausayi tace Hajiya dan Allah kiyi hakuri ki duba lamarin nan..janet is one of the best workers wllh bata tabayin kuskure akan aikinta ba hajiya pls have mercy on her
duk wacce za'a kawo banajin zata kai janet wajen kkrin kare mutunci da kuma ran general...
Chapter 98 · 0% Book details