← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 206

Sashe 94

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahaka daren ranar ya zame mata me daci dan gabaki daya baiyi mata dadi aranta ba daga ita har simran din datun da hajya zubyn ta shigo ta kwace komi na gidan ahannunta takai ma nur ta kwanta agado ta rike zuciyarta tana nishi nishi tana zage zage wai zazabbin high fever ya rufeta

gashi duk wann gurmin anyi shi ne adan kankanin lokci wanda kwata kwata harsu lady sidd ma basu ji labari ba bare su hana yuwar wani abu dake kawai oder ya bawa hjya zubaida yace mata with immidiete effect dan aganinsa samun waje ne ya jawo zubaida da yar uwanta suke masa mulkin kama karya a gidansa musmn akan surkuwan sa dan sun ganta karamar yarinya.

fannin nur kuwa ko ajikinta wai irin kaji dar dar kayi abuna makircin din nan bata kuma ko ji alamar ta girgiza da maganan hajya zuby ba.

yauma tajira ganin shigowar javeed da baizo ba kawai sai tay haquri ta rufe idonta ta kwanta, yau kam tay kkrin share abun danma tay disracting mind inta yasaka ta fasa baccin suka xauna a falonta ita da private servant dinta na'ima nan suka fara warware duk wani salon hauka da mugayen dokokin rashin hankli dana cuta da simran take zubawa akan sha'anin tafiyar da duk wani walfare na gidan

naima ne ka bata duk wani information suna dubawa wanda yakai su har wajajen one o'clok na dare kafin nan nur ta sallameta itama tay addua ta je daki ta kwanta bata jima ba bacci me nauyi ya dauketa.

bayan wann daren, dare daya da kuma wuni biyu ne kacal ya rage ma javeed agidan, dn haka goben ya yanke ranar hutunsa ne dan dokane basa training 2 days before a mission attack dan haka yaudinne kawai ya samu ya karkare duk wata shirinsa da duk wani training dinsa na karshe sabida goben ya samu isasshen bacci da kuma hutu..

bashida da gama shiri ba sai wajajen 2 oclk na dare, wanka kawai yay yasaka wata dark blue plain pyjams riga da wando dacan har zai kwanta saidai jin yakasa samun wata nitsuwa a
ransa saiya taho cikin dakin nur din yashigo queitly batare da yay wani motsin dayasan zai tashe ta ba.

yana daga tsaye ya kalleta yaga tay nisa abaccin sosai ahankli ya karaso ya zauna agefenta bai tabata ba yazuba mata mayun idanunsa masu cike da muguwar kaunarta yanata kallonta da tunanin inya tafi baida tabbacin zai dawo mata da ransa koko a muce..

kallon innocent figure inta yakey da dukkan imaninshi atake kuma sai yaji wani irin rauni na neman rufeshi da tunanin in yaje yamutu acan ribar soyyrsa kenan guda daya da ya auri macen dayake so aransa, saidai yasan zai iya saka rayuwar nur a wata matsala duba da gata karama batama san dadin auren ba bare kuma tarin soyayyar dake ransa akanta wanda har yau bai samu daman nuna mata yawansa ba.

tausayinta sosai ya rufeshi har kamar hawaye zai taru a idanunsa yana zaune awajen yafi awa daya yana tunani yasan lokci yagama kurewa nayin wata maganar fahimtar juna atskainsu dan baison yay zatay reacting ba kuma shi rayuwarsa yake dubawa sabida ya samu ya dawo araye saboda ita.

da wani irin tsumammen rauni a idanunsa ya manna mata kiss mai sanyi a saman lips dinta

ganin tafara motsi tana dan sniffing perfume dinsa yasaka yamike sikinini yabar dakin yakoma nashi kawai ya kwanta bai jima ba yafarka sallahn asubahi yana fita nan ma baijima ya dawo dakinsa ya kwanta abunsa yafara bacci tareda bada oder cewa baison ko kadan atadashi...

sassafe nur tay sallanta jikinta na ta bata cewa javeed yazo dakin jiya da dare dan haryanxu tana jin qamshinsa ajikinta da akan hannunta daya riken amma kuma sai tabarshi kawai a imaginations ne dan yadda ta masa rashin kunyar nan ta koresa a jiknta batajin hala zai taba takowa yazo
...

tun 6:30am na safiya naima tazo suka fita waje tare, nur ta saka dogon hijabinta har kasa daya killaceta kirif cikin takun ta na nitsuwa har suka je general workers estate nur tay paying ma ogogin maaikatn gidan unxpected visit.

already ta riga tasan yadda ake magana cike da confidence, nuna girma tareda sanyin dattako agaban mutane sabida abunda ma molly tafara koya mata kenan.

dan haka koda sukaje aka tara ogogin taga kowa na rawan jiki ana gaisheta duk dama ta san yawancin su sunkai su haifeta amma bata sake tay musu over sabi face ba.

yanayinta anitse kuma da isashen kamiya ta musu bayanin yadda ta tsara nata dokokin

snn ta basu daman ushering din opinions dinsu da wasu ra'ayoyinsu wanda abune da abataba musu agidan ba sabida simran ne take hawa kan komi dacan kuma hajya zubaida ne.

cikin 1hour sai gashi har sunyi resolving komi da komi anan ma takejin yadda simran ke mugun kakkara kudi akan abubuwan gida tana makewa..

ashe simran ba kulawa da business din babantan takeyi ba kawai wayann yan kudeden cutar data keyi agidan mufasa shitake rike kamfanin dashi har ake ganin kamar tanada wasu boyayyun investmts ne duk ba asan kudin sata bane datake mammakewa daga cikin kudin abinci da welfares na duka ma'aikatan gida

duk wani kayan masarufi ko karin kudin aiki ko ihsani sam ko kujerar macca da ake rabawa wokers simran ragewa takey acikin na wasuma takan tsakura kadan ta basu wasu kuma takan hanasu taba komi.

zagewa manyan cikin su sukayi suka hau gayawa nur komi dake faruwa agidan basu boye mata aya ba, dan tun bayan rasuwar mahaifyr javeed komi ya lalace musu amma kuma sabida hajya zubbyce agidan ya zamo basu isa sukai karar simran ba nan da nan sai kaga ta karyatasu ko tay musu mummn sharri.

nan komi akayishi cikin girmamawa da aminci snn ta ja kunnen kowa akan suyi aikansu da amana da gaskiya wasu haqqin su da aka tauye duk atake ta saukar, masu bukatar canji duk ta canza musu, har liyatu saida ta dawo da ita snn tay assingn ma simran din wata yar yarinya dede da aikin gida.

yau kamar sallahrsu hakanan sukejin dadi kowa na sambarka da nur firdaus atleast babu tsiwa ba tsawa babu gadara da mulkin kama karya kuma anji raayinsu akan abubuwan dake damunsu kuma an dau hanyar samar musu mafita..

wasu da akayi case din jiya dasu a kitchen yadda simran ta dinga cika baki agabansu yasa sukasha mugun mamakin yadda har nur takwace komi ovenight a hannun simran duk gadarar datayin nan.

masu yayata gulma akan hakan kuwa yasaka kowa yafara jin mugun shakkar nur din aransa ganin yadda alokci daya ta kifar da mulkin simran data jima tana nuna musu itadin wata kainuwa ce agidan

wasu dama sunsan basu isa su dama sutaba nur akowani siga ba saboda sunsan javeed baiya wasa da kowa.

sassafen kuwa ko wani bangaren wokers aka canza tsari aka fara abubuwa cikin salo me tsafta da sauki kafin 8am nur tay signing wasu pay cheques din su da simran take hanasu.

kai hatta chat table na abincin duk tasaka an sauyashi musmn na main kitchen da simran ta saka ake musu hauka kowani safiya..

janet da naima da faiza yau bakaramin jinjina ma nur sukayi ba saidai babu mai iya furta mata duk ana tsoron shiga gonan javeed amma daga fuskarsu zakasan suna mugun jin dadin yanayinta sosai

normal routine dinta na kullum sukayi, nur ta shirya tsaf yauma atmfa ta saka peplum stylish blouse me strght skirt grey colour tay lullumi da karamin veil abinta koda taje sashensa yaukam ko su janet din ma bata gani a kofa ba and once is locked frm the inside bamai iya budewa.

bata saka komi aranta ba tay zaton ko ya sake fita training ne as usual kawai sai ta danne zuctarta ta sauko kasa ita daya abunta taje main falon.

nan ma ta samu har angama kawo breakfast an shirya musu komi kuma akan lokaci anty suad sai yabawa da sabon tsarin girkin yau din takey amma tunda hajy zuby tace mata ai nur ce ta amshi ragamar komi sai ta tsime tana neman hadiye magananta

haka akaci abincin babu javeed babu simran dake kwance a dakinta tana kuka tun jiya da dare haryau tunani takei na me zatay ma nur ta rama wann uban cin mutuncin da rainin data mata agidan dan tasan yanxun kowani servants da maids zasuna mata kallon bata da iko snn nata ya kare.

wani tukukin numfashi taja akarsashe zuciyar ta na mata wani irin zafi tace "inaaaa...
wallh bazai taba yuwa ba saina ramaaaa ta mike zaune tana wani irin kukan yadda saka san abun yay mugun ci mata rai har wani sheshheka takeja ta ciki....

saida ta gama tunanin me xatay snn ta mike ta shiga ta wanke fuska tana fitowa tasha tea me kauri hade da magani tukunna ta fita wajen motsa jiki.

kazar kazar tareda walwalan dake wanzuwa a fuskan wokers din yasaka lady sidd tayita neman cikakken karin bayani akan lamarin daya faru jiyan har aka yanke hukuncin bawa nur firdaus keys, haka hajya zubaida ta dinga dunkule maganan tanamai gaya matashi a wata sigar me cike da hada gurmi.

tana nuna kmar komi bisa makirci kawai akayi cewarta ai ba a ma simran adalci ba dan tun bata kai haka ba ita take zuwa ta kula da komi na gidan dan kawai yanxu an kawo wata sai aci mata fuska bayan kuma ga trauma datake fama dashi na rasa javeed.

yau hajiya zubaida har hawaye tay agaban su anty suad tanamai fayyace musu irin secrifices din da simran tay agidan tun da jimawa. ..lady sidd sosai abun ya dan tabata saidai anty suad kuma aranta gani take dama hakan ne daidai kawai gara abawa nur in inyaso su suci ubanta dakan su kawai idan tay wani kuskure tunda sunsan ai rike hidimar gida bana yaro bane.

lady sid kuma was complaining bitterly tayi tayi tasaka anty suad ta furta cewa zataje tay ma alhj attah magana adawoa simran da komi amma sai taga anty suad din batace komi ba.
Chapter 94 · 0% Book details