← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 206

Sashe 81

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kuma ba wani abu ke cinta araiba face tsananin kishinsa tareda wani boyayyar insecurity daya cike brain dinta sai gani take kamar dan ita karama ce hala bata dace dashi ba, gashi batay makaranta me yawa,duk daga razian har simran din sun fita kudi, wayewa, da wayo,..ita duk sai take ganin kamar komi dayake fada, ko xai fada matan karyane kuma yaudarene hala kawai jikinta kawai yakeso dan ya more kuruciyarta ganin tunda tazo gidan nan bai taba kwana daya bai latsa mata jiki ba

aiko dacan ma bai neme yaje yawonsa da anty razia ba sai ita kawai gani take kamr ya raina mata wayone ita batada wani kkwaran amfani a duniyarsa face na kashe kishin ruwan sha'warsa.

da wannan tunanin aranta takoma dakin ta tana shiga ta samu na'ima ta gama komi saidai yau ko amsa gaisuwarta batay ba tace ta bata waje

...naimar na fita ta hau gadonta ta kwanta rif da ciki tadinga rabxa kuka kamr ranta zai fita dan bataga dalilin da javeed zai tara wasu mata masu aji da ilimi wanda daya yace xai aureta, daya kuma kmr side chick ne snn ita ya aurota yana duk yadda yake so da ita

gani take sabida kashe wutar jarabarsa kawai ya aureta,but who did he think he is? ko dan yaga yana da iko da uban kudi
..aikuwa sai ta nuna masa duk iko da kudinsa bai isa ya sake taba mata jikinta agidan nan ba....

ata bangaren dr simran kuwa yadda tafadi awajen ta suma babu wanda yasani face saida hajya zuby tay ta zaga gidan tana nemanta hanklinta a mugun tashe..

dakyar saida mr aqeel yaji ana kuskus cewa simran ta bata agidan sai yatuna ashe dazu yaga ficewar ogansa da matar sa amma baiga fitowar simran ba a gym din ba..

zuwa yay gym din ya bude ya sameta a rigingine baiko tabata ya fice yaje ya kira hajya zubaidan tazo da masu aikinta aka dauki simran din ruwa ruwa sukayi sama da ita batare da tabari kowa yagansu ba..

Ruwan drip aka saka ma simran duk da haka saida tay awa kafin tafarka ta dinga kuka tana bawa hjy zuby labarin abunda ya faru hankalin hajy zuby duk yabi ya tashi ta rasa abunda yake mata dadi...

acikin main house din kuwa anty suad da lady sid ne kadai suketa buga duniyar bushashar su wanda dama can su bawai sun damu bane da hjy zubaidar yanxu babbn matsalarsu agidan nur firdaus ce wanda rashin ganinta jiya da yaudin yaso yadan damesu bana kadan ba, dan sungama tunanin cewa hala zata sauko ta sake zuwa ta gaishesu ajiyan, toh bata zo sai gashi yau ma har ana neman wajajen karfe 9;00am babu wanda ya fito acikinsu..

doka lady sid ta bayar akan asaka shirya family breakfast a daily routine na tsarin gidan tunda sune manya kuma suna cikin gidan dama bai kamata ace kowa nacin abincinsa a sashensa ba, kai zaka dauka kodan batun kara dankon zumunci take buga wnn wa'azin alhali wann din wata hanyane kawai da zasu samu daman kafawa kowa kahon zuka da saka ido ma nur firdaus sosai tunda idan family breakfast ya zama doka dolene kowa zai fito waje.

lady sid tace ma chief cook marmaza afara hakan daga gobe, anty suad ta tuma tace sam ita yau yau take son afara cos she want to see everybody out on the dinning table inyaso gobe a dora girkin da wuri
9:30 for famly breafst

marmaza private chefs suka hau aiki snn aka aika sako wa private servants na kowa sashi dan su sanarma kowa akan ya shirya by 10am ake son ganinsu a dinning table.

nur na kwance akan gadon haryanzu da kyar zafi da kishin komi ya lafa mata sai ganan naima ta shigo mata da sanyin murya tadan rusuna tafara tambyatta ko lafya? nur tay murmusho tace mata bakomi kawai tahada mata ruwan wanka bamai zafi ba bamai sanyi ba

nan da nan naima ta mike ta hada mata ta shiga wankan tana fitowa ta mika mata towel na goshe jiki snn tafara sanar da ita cewa ana bujatat ganinsu a kasa dukan su for family break fast..wani irin takaici taji ya turnuketa dan ko kadan batason ta kara ganin fuskar javeed bare kuma na simran duk dai haushin komi takeji.

saidai tasan inhar zataje dole ne ta binne borinta akan komi a dakin nan sabida razia ta gaya mata karta sake kowa yagane akwai wani matsala tsakaninta da mijinta musmn ma family if not zai bude mata kofofin fitina kala kala daga wajen maqiya.

zama kawai tay agaban madubi tanata kallon kanta tareda kkrin danne komi cikin sauke ajiyan zuciya

naima ce take mata komi cikin kwarewa da nuna gata tanay tana mata hira kadan kadan sabida ta lura kamar nur din tana cikin damuwa..

sama sama take amsata but she feel like she will like naima sosai sabida tarin hikimar dake tafe da furucintan mai fita tareda ladabi da nitsuwa sosai.

tana gama kimtsata ta zauna tay kwalliyarta me mugun daukar hankali feline eye liner me kauri daya fito da shape din idonta tabi tashafa nude eye shadows me glitters da nude lip stick me wani irin shekin nan tabo da pink lip gloss ta kyalyale ko ina da sanyayyan countours kamar wacce zataje wani wajen show na huce takaici..

saida ta tabbata ta tsokalo wata iriyar nitsasiyar kyau kafin nan ta hakura suka je close tareda naima tana tayata zabar kayan daya dace ta sako ajikinta kafin lokcin sauka yayi.

ata fannin su simran kusan hakane dan ana kawo musu sanarwan maza maza ta dire kasa tahau shiri gata dama ta iya saibi haka ta saka ata tara mata maikata sunkai goma masu shiryata sabida kawai tafito wajen tay impressing dinsu anty suad tareda lady siddika.

hajya zubaida sai kitsa mata abubuwn da xatay awajen takeyi most importnly tace ma simran ta saki jikinta tay biyayya ma anty su'ad sosai tace mata duk wani abinda nur batay ita saitana lura tana yinshi koda na eye service ne dan da haka ake samun gindin zama...

tsakanin 9:00am to 9;50am gidan yadau wani irin shiru kowa na cikin shashensa yana shirin fitowa masu shirya abinci kuwa har sunfara shirya table dan ba wani abinci masu nauyi ake shiryawa ba.

bangaren javeed zuciyarsa bawani dadi ya fito daga wanka ko shiryawa baiyi ba sai ga video call na sultan wanda dama yace masa ya kirasa adede wnn lokacin.

zama yay akan couch
dinsa da hand towel yana goge ruwan dake kansa kafin nan ya kunna video call din suka fara maganan mission dinsa da sultan.

wani irin shiru yay yana jin sultan yana masa bayanin yadda komi ya sauya dan already target dinsu akan operation na nagaza brotherhood ya sauya zuwa nan da kwanaki biyar bcos they want to beat javeed at the game
tunda plan dinsu na kashe matarsan baiyu ba sunsan dolene zaizo nemansu.

gashi sunaso suyi kazamar business dinsu da wuri kuma aboye batare da sannin javeed din ba inyaso kafin yafara nemansun suna da makaman da zasu iya karawa dashi

sultan yace masa inde yanason yasha kwana akansu dolene sai ya shirya kansa within dis five days ya bar gida dan ata wajen sa already sun fara shirin su na back up plans da zasu turashi operation dasu.

javeed bai tabajin tashin hankli aransa ba sai wnn karon dan already ya gama yankewa aransa kawai yau zai gayawa nur firdaus komi dan yagaji da kallonta tana masa kuka da bori akan abinda bai taka kara ya karya ba abun yafara damunsa sosai yadda yaga take tunanin yana mata karya shi mayaudari ne snn jikinta kawai yake so ba ita din ba.

sai yaji dama baiyi waya da sultan din ba harsai bayan ya fada mata komi cos how will he even concentrate on both now, kuma within 5 days ace yajeshi aikin kasada da rayuwarsa.

yanacikin wnn lissafin sultan ya kuresa da kallo can yace guy yadai u look tensed did u wanna talk abt sumtimg? jin javeed yay shiru ya sharesa sai yay dariya da tsokana a muryan sa yace latest ango in town kenan kodai case dinku da babynmu ne bai kare ba?

fuskar javeed was looking emotionless adan gajiye kamr maganan be darasa yace
'..'simran is back.

sultan yace ohh dat squeming Bitch..sun hadu kenan..

javeed yace yeah, and my baby is just...

cikin katsesa sultan yace overeactive ko?

cikin kyabe baki javeed yace "possesive, jealous..angry
wainamata karya na yaudareta..hmm mata sai ahankli wai dama haka kuke fama da wnn rikicin?

sultan yay dariya mai dan karfi yace woooh welcome to the crew man..dacan dai inna gaya maka mata sai ahankli aibaka yarda so yanxu ya ake ciki ka kashawo kanta ko

yace hmm sultan kenan, u have no idea how dat tiny pretty creature is, wallh ji take kamar xatamin shegen duka.

dariya sultan ya fashe dashi...yana dariyar yace dude but dats just how much she loves you..inkaga mace na bori da kishi akanka wllh sonka takeyi na gaskiya

a tsime yace i know ..shiyasa abun ya fara damuna ynxu, she is hurting herself dayawa akaina gaskiya ina ganin dolene kawai nagaya mata komi ayadda xata fahimceni takuma san cewa ba yaudararta nayi akan auren nan ba tun kafin nan simran tafara taking advantage na situation din na shiga uku dan itama wata problem ce amma in baby taki jina bazan matsa mata ba aita mayi kokari dani, so zan bari saina dawon kawai since i have only five days to prepare frm now bana son muyi wani fadar da zaizo ya dagamin hanklina tarasa ni me gabaki daya.

sultan yace "yeah ure ryt..amma ka gwada gaya matan..inde har bazata fahimta yanxu ba toh gara ace kabari saika dawo din if not ur life my be in a more greater danger out der in ka fita da wani tension akanka.

suna cikin wayar sai ga knock din mr aqeel sai suka katse nan ya bashi izinin shigowa

janet ne ke biye abayansa idonta akasa cikin ladabi tahau gayamai cewa akwai family breakft and his presence is highly being requested.
Chapter 81 · 0% Book details