← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 206

Sashe 43

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

alhaj attah yace “To, in hakane zamu bukaci haduwa dasu akan lkci,mother bazata hana auren javeed ba tunda har nay bincike kuma tunda Ba auren mutum daya muke yi ba idan muka aure diyarsu mun Aure ahalinsune gabaki daya sai mu tabbatar cewa an azurtasu ta inda zasu iya daukar nauyin sunan Mufasa azuriarsu kafin mu kulla alaqa.

cikin lumshe ido da budewa yadda zaka san maganan ya mugun kona mata rai muryanta ciki ciki tace
"'..another charity case?..dede nan javeed ya dago kai ya mata irin mugun kallo

....cikin rolling eyes tace toh toh toh naga danka yafara harara na nikaina ma na ciwo, tunda dama kunce gaskiya yariga yakashe sauran ahalin kenan da wanda yaran suke zaune a hannun sa kawai zamuji

..nan take ta zaro wani chechqe book ta yagi paper daya cikin kyabe baki tace since i am incharge of our finances here..lets see wat we can do..,

kai tsaye tahau rubuta cheque din sann ta kallesu tace this is 20 billion naira..

takalle javeed da kasar idonta snn tace "non negotiable price, aiya ishesu sutada kashin arzikinsun da akace suna dashi dn gaskiya iya abunda ahalin mufasa zasu iya rubuta musu kenan.

javeed baiko dago kansa sama ba yay shiru yanajin mahaifin sa yana yar dariyarsu ta manya...yace haba suad 20billion naira ma ahalin da zasu bamu mata?...ohhh pls u can do better. let make it 50-80.

dawani irin jiji dakai da giggiwa tace i am sorry but no, yaa wann din kawai ya ishesu, ahaka fa bawai baza mukai musu kudin sadaki dawasu abubuwan bane..

nan tafara kukkuni tabi taharde ranta muryanta kasa kasa tanamai cewa hmm aisune zasu moremu bamune zamu moresu ba kawaide dama yaaya kaine ka saba da bin bayan danka toh Allah yasaka dai kar ayo mana zaben tumun dare dan naji kace yan mata biyu a gidan.

alhaj attah baiwani kula shirmen kananan maganan tan ba yace kedai kawai Ki shirya sheik haidar da kuma khaleefa ko kamil maza susaka ranar ganawa da ahalin yaran nan a kaduna dan a tsaida maganan
abamu ranar daurin auren kawai.

snn ya kalle javeed yace kaikuma ka tabbata wannan ba soyayyar zuciyarka kadai bace Ka dauki girman sunanmu da mutuncin wannan ahalin.

ahankli javeed yace
“Insha Allah, Zan tabbatar da hakan.”

daga haka suka karkare maganan auren, hajy zuby dake musu labe tanajin motsin fitowarsu tay marmaza tabar wajen takoma sashenta taje takira yar uwarta Dr simran awaya tahau gaggaya mata abun da aka tattauna.

sede abun yau bae wani darasu sosai ba dake ma tun last week suka fara ganin haske, dan kamar yadda saratu volkner tafada musu hakanan kuwa ya faru, dan lady saddika sadik ce ta fara kirar hajy zubyn kwasam akan batun zancen dr simran, har yakaiga tahadasu da simran din awaya suna dan gaisawa kullum.

satikan da suka wuce sosai suke cikin farin ciki da annashuwar ganin sunsame kan lady saddika wacce ita tadingakai zancn simran din kunnnen anty suad mufasa

haka hjya zuby ta dinga kwantar ma Dr simran hankali da cewa aiyanxu kam ta zuba ido kawai ta gani
nasara kam kamar yazo hannunsu,tunda manyan matan ahalin mufasa sun dawo gefensu snn ma ai ahalin da javeed din zaiyi aure aciki ance talakawa ne basuda wani arzikin azo agani

wann bayanin sosai yadan faranta ma Dr simran rai yakuma cire mata tsoron razia dan atunaninta samun kan javeed ymxu zaizo musu dasauki sosai muddin sunada support din lady saddika da kuma anty suad mufasa...
[02/05, 21:37] BLUE💙: EPISODE 27🦋
Ata dayan bangaren kuwa gabaki dayane mrs haseena shariff takasa samun wata sukuni ackin zuciyarta musmn ma ta tabi diddigi tagane cewa asha duk zancen nur firdaus da yanjarida suka tsareta dashi ranar ba gulma bace tsantsan gaskiya ne da babu wata karya aciki.

tunanin duniyar nan tay saidai ita tafi aje hanknta ne akan ko abbakar na amfani da nur firdaus ne dan yay mocking din nata lalar tarbiyar wanda abune data mugun tsana ace tagaza akai kusan ma ince shine yake yawan hadata hatsaniya da mahaifin nur din tun kafin ya rasu.

ayadda ta zamo wata babbar jagorar kare haqqin mata da yara ta tsani ace mata ita ta gaza akan rayuwar y'ay'anta dan it is a very hard pill for her to swallow musmn ayanxu datake kara jin bayanan cigaba akan rayuwar nur sai takejin wani sabon baqin ciki na mugun mamayarta,

wai ace yau har da yar cikinta za ayi amfani dan a muzanta ta? tsaki taja tace toh wayasan ma abbkar dinne ya aiko mata yan jarida offishinta dan su gasa mata baqar magana aga me zatayi.

takitsa tunani kala kala aranta harsaida taga kamarma bazata iya daukar wann big public slap din ba gara kawai tashirya tanuna musu itadin wacece susan cewa itadin kainuwa dashen Allah.

shirya kanta tay cikin wani mayyar doguwar riga ta fito ranta a mugun cunkushe

bada son ranta ba ta yanke hukuncin zuwa gidan yarta layla dan tanaji aranta cewa hala idan layla taji irin cigaban da nur firdaus take ciki arayuwarta hala wani sokoncin soyayyar datakeyi ma adnab marar riba zai ragu snn ta dawo cikin hayyacinta su hadakai suyi abinda suma zaa abuga jarida dasu.

withim 45 min ta iso gida lokcin layla na zaune falo sanye da doguwar riga tay zugum cikin tunani
dan tunda ta tattara kayanta ta dawo gidan haryau ko cikanki bai hadata da adnan ba gabaki daya abun duniya yabi ya dameta fuskarta babu walwala..

tana cikin wann yanayn ne taji ƙarar bude ƙofar falon a cikin hanzari tadago kai da tunanin ko adnan din ne ya dawo

suna hade ido da mrs hasina jikinta ya fara rawa rawa ta mike da mamaki da kuma fargaba tace mummy?

wani bankadadden harara mrs Haseena ta shigo dashi cikin tafiya mai ƙarfi tana rike da jakarta har ta zo ta tsaya agaban Laylan tana kallonta da fuskarta daure

nan take idanun layla ya cila da ruwa tace ure welcome mummy

amasife tace dakata min laylah dama can baki daukeni uwa ba, shiyasa Kika gwamci kixo kizauna anan kamar wata yar prison ana gasa miki azaba ke kuma kina nan jiran soyayyar adnan ta sauko miki daga can sama kamar wani wahayi ko?"

Nan take Layla ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta batace komi..

mrs haseena tace“ layla duk dama kin xuba min kasa a ido bazan iya zuba ido ina kallo rayuwarki ya lalace ahaka na, ke ai Kinfi kowa sanin irin abinda muka fuskanta abaya Amma kin kasa fahimtar cewa ynxun lokacine na neman ci gaba ba nazaman jira soyayyar wani sokon yaro ba. Kinko san yadda Nur Firdaus ta tsaya da kafatta? toh bari na baki labari jiya aka gayamin cewa har ta mallake buildings nakanta datake running school, da charity harma da philatropic works

Tuni bar fama da ciwon son wani banza ta gina rayuwarta har gashi yanxu duniya na jin sunanta...layla kin cuceni..ba haka naso rayuwarmu ta zama ba..kece nayoma ruwa da tsaki snn na doraki amatsayin da zaki zama abar kwatance a duniya amma kika tsaya shirme gashi nan kawunku abbakar daya tsaneni ya fara aiko min munafakn yan jarida suna xuwa gayamin cigaban nur firdaus a ahannunsa

nan Layla tadago idanunta da sukayi ja sosai tace mummy dan Allah kiyi hakuri
ko saurareni cikin katseta da tsawa mrs haseena tace da Allah kimin Shiru Layla, bana son jin wani magana akan adnan, kawai Ki tashi ki tayar da rayuwarki. Ki zauna ki tsara abin da zai sa kowa yadaina jin tausayinki aa fara ganin kwarjini da aiyukanki ke kanki zaki sha mamakin yadda adnan din zai sauko miki da wuri
kowa yace miki wnnan duniya tamai jiran kuka ne. Ki zama macen da nake so mai burin kai kanta gaba wasu walkncin dakike fuskanta a gidan nan is all bcos u have nothing and ure doing nothing

Lumshe ido kawai layla tay tanata zubda hawaye ayayinda taji dirin masifar da mrs hasina take mata da kyar ta iya budar baki tacee mummy kiy hakuri Zan gyara.”

ko saurarar kukan ta mrs haseena batay ba itade yanxu babban damuwrta shine suyi suy abunda zai zarce na nur firdaus.....

tana gama mata masifar takama hanya ta fita tare da barinta acikin nannauyar tunani da baqin cikin nur firdaus me yawa wanda Allah ne kawai yasan iyakar yawansa aranta ynxu..

bayan kwana biyu..

daga kaduna rayuwae dadi kawai nur firdus takeyi dan akowani lkci take bukatar jin muryan javeed zata sameshi zasuyi hira sosai kuma koyaushe sai ya mata alkwarin cewa na bada jimawa magabatansa zasu zo

wanda hakan ne ya fara saka mata jin shaukin gayawa razia halin datekecikii dan batason ace harsai javeed yazo ya turo gidansun snn kowa ya sani gara dai kawai ta gayama razia komi koda bazata kama suna ba.

hakanan ta dinga shirya maganan aranta cikin kankanin lokci harta gama tantace wanda ya dace ta sanar da wanda bai dace ba

yau suna kammala breakfast ta jawo razia dakinta suna zauna daga bakin gado, she was very nervous at first amma data tuna cewa yace any moment zasu iya zuwa kawai sai ta fara
gayawa mata tun daga kan ranar da suka hadu a kaduna har ranar birthdaynta da duk abunda ya faru amma bata gaya mata cewa sunje hutu tare dashi a wani kasar ba gani take kamar raziar zata mata fada akan hakan sosai tunda aboye taje batare da sanin kowa ba..

ita kanta razia tasha mamakin yadda taji sun hadun da kuma yadda taga jininsu ya hadu sosai acikin sauki dan dama she kept wondering a ina ne nur ta hadu da javeed mufasa ashe a grave yard din mum dinsa ne.

yi tay kamar bata san komi akan labarin ba
tabada hanklinta sosai tanitsu ta gama jinta har tagama kafin nan tamata murna ta kuma nuna mata ai babu komi aciki, tunda tana sonshi shima kuma yana sonta kuma sun fahimce juna har yace zaixo gida shikenan.
Chapter 43 · 0% Book details