← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 206

Sashe 122

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

har sai bayan sun daidaita kafin mr manny yace mata basu da wani option face suyi amfani da wann ciwon nasa dayaki warkewa suma su suka hannunsu aciki dan haka zai aiko mata da wani gari zataje ta aje adakin the more qamshin saiwar dake cikin garin na baza dakin the more rayuwar javeed yana karewa and he wll be dead in not less than 3 days

hajya zubby tace sam badai ita zataje ta amso aikan ba saidai ta aiki simran sai akai mata asibitinta da fake patient ta amso ta dawo.

mr manny yace toh idan ya shirya zai kirata ta shirya any moment sai ta saurare kirarsa amma inhar ta bata musu wnn daman toh saidai ita ta nemi hanyar kashe javeed bazai sake saka hannunsa akai ba kuma inhar batay ba wallh sai ya tona mata asiri

Duk dama hajy zubaida takan nuna musu ita jaan wuyace bata damuba da barazanarsun ba amma a boye bakaramin tashin hankali take shiga ciki ba, da kyar da wahala ta kwantar makanta hankli wanda ya jawo bata fito a dakin ba sai can wajajen karfe 10 na safiya snn tazo inda javeed yake kwancen ta samesu anty suad ta dinga gilla musu karyan cewa ai mafarkin mum din javeed tay da jariri a hannunta tana kuka haka tasa suka razana kowa yana ta jimamin ko hajy zubby taga kurwan mamansa ne nagaske a mafarki.

Nur ce kawai labarin baiwani je mata ba itade tay shiru tana lura da kowa awajen

can da yamma can still mr manny bai neme hjy xubby ba bayan anje cin abinci da sallah nur ta sallame likatan da su janet sann ta kunce ma javeed rigar asbiti da aka sakamai tacire masa har wandonsa tabarsa da yar ciki saboda tunda aka kawosa ba'a canza mai kaya ba face rigarsa da aka cire sabida jini ya lalata shi

nan tahada ruwan magaryan acikin kwarya ta karanta duka ayayon da alhaj attah ya gindiya mata dede yadda yace din snn tafara tsoma tsaftaccen towel aciki tana masa complte body bath da shi..

tafi rabi awa tana gogeshi har ta kansa ta wanke yau bakaramin dadi taji taga within 20 minutes har javeed yafara sauke faint numfashi irin na cikin nan kadan kadan ba sai taji abun ya mugun kara mata karfin giwa

bayan tagama wankensa ne ta leko waje tace ma janet taje ta kawo mata new pair of trouser da inner wear guda daya wanda marmaza janet taje ta dauko ta kawo mata saida ta rufe mishi waist dinsa snn tacire masa short din ta kara jika towel din tagoge masa gabansa dashi sosai ta tsaftaceshi tayi dry damping da wani set na towel kafin tasaka masa new white shot da hadadden dogon wandon da janet ta kawo ta saka masa ta dan fetsa masa turare sama sama ta taje mai kansa yay fess kafin ta sakamai rigar asibitin takara gyara mai kwanciyarsa da kyar dan bakaramin nauyi yake dashi ba

tana haki ta gama masa komi taje ta aje sauran ruwan wankn maganin agefe ta inda take sallah...

nan ne ta bada dama wa likitan da janet suka shigo sai gasu anty suad suma sun dawo suka zazzauna ganin ta canza masa komi wasu sam hakan bai musu dadi aransu ba dake sunso ace nur bata iya komi ba, snn bata da wannan kalar jajircewa da karfin zuciyar inyaso komi na javeed sai ya dawo hannunsu ya zamana su sukeyi anma kuma sai mamaki take basu aransu kowa na fadin albarkcin bakinsa akanta cikin habaici.

Barinma Dr simran datake mugun jin haushi, baqin ciki, tare da tsananin kishin sanin nur nada wnn uban access din da tsiraicin javeed, harma tafara tunanin ko sun fara kwanciyar aure ne sai wani irin mugun kallo kawai take ma nur din akai akai kamr wacce zata tashi ta cakka mata wuka a zuciya.

nur kuwa tunda suka shigo suka fara jefa mata habaice habaice ta tattara kayansa sikinini ta kai bathrum din dakin ta hada tare da wanda aka kawo shi aciki jiyan ta fara wankewa, wani irin baqi ruwan rigarsa yake fitarwa duk ta dauka ko kwana da yayine acikin jini sai bata damu ba ta wanke tsaf ta fito ta bawa janet tay sundrying dinsa sabida effect na prolong stain na jini.

tun anty suad tanajin kamar nur tay abun kirki har yawan korafin lady sid yafara shige mata kai yawan cewa datake nur na zakewa akan javeed yanxu sai aga kamar su bakomi sukeyi akan javeed din ba sai shan shayi da hira,..wanda haj zubby ma ta tsoma baki tana cewa inba aikin eye service ba aiko wankin ma zata iya bayarwa ma janet tay meyasa ita tay dakanta inba markici ba..simran ta fara burga irin tafi kowa sanin rayuwar san nan tana nuna musu anty suad cewa ai javeed ma baya memeta kaya kawai wahalar dakai ne yasaka nur ta wanke jinin waye waye...

hakanan suka dinga mata habaici a dakin tun abun bai dameta ba harya fara damunta koda taje alwalwa sai da tay kuka abun ya ragu mata snn ta dawo tay sallahn asr ta zauna shiru tana adduar Allah ya bashi lafiya, bayan isha kuma ta sake mai wankan snn ta cigaba da saukarta dan yau kwata kwata bataji dadi a zuciyarta yadda su anty suad da lady sid suka dinga gasa mata baqaqen magana acikin habaici ba.

farin cikinta guda daya shine numfashin daya fara wanda yasa vital dinsa yahaura with 4%
he is now at 34% which is still not soo encouraging to hope for life.

yaudin haka ya kare wani abu kwakwkara bai faru ba dake ana dai kan neman dr ruqayya da mother hauwa tunda da tafara karatun ta bayan isha matayen gidan suka watse tadan samu sarari

Hajy zubby ma lafya ta kwanta dan har dare ya rufa mr manny bai nemeta a waya kamr yadda yace ba.

9:30 pmm nur ta kammala hada suratul baqara ta fara karanta suratul ali imran takai kamar shafi biyu snn ta haqura ta hawo kan gadon tayi ma javeed aduaoin kariya masu yawa kai duk adduar da yazo bakinta inde na kariyane tamasa awann daren snn tadan kwanta agefensa da addua abakinta har bacci ya dauketa.

janet ne kawai dama ke watching dinsu ita bata samun bacci har sai nur ta farka yin sallahn dare sai ita takwanta tay baccinta zuwa safiya..

tunda nur ta kwanta agefensa tana bacci janet ta mike tanamai aikin duba security cameras recording tanamai lura da masu shige da fice musmn tasaka idonta akan dr simran da hajy zubby tanamai karantar yanayinsu tun ran da aka kawo javeed dakin zuwa nan..

downloading copy na video tay ta tura ma na'ima sabida tasan naima is witted nd very sharp minded hala zata tayata gane wasu abubuwn

har karfe 1;30 aikin datakeyi kenan tanayi tana duba nur da oganta for awhile ita dai taga nur na baccinta peacfully

can karfe uku na bugawa dede sai kuma taga nur din ta farka a mugun firgice tana salati da karfi ga wasu irin hawaye sharbe sharbe suna sauka a idanunta kamar wanda aka watsosu jikinta na rawa rawa ta sauka akan gadon ta tsaye asandare tanata kallon javeed da wani irin bugun zuciya

a hujajan janet tazo ta dan tabata sai taga ta tsorata taja da baya

hanklin janet atashe tace "ma'am lafya kuwa..ranki shi dade hajiya...kusan a rude nur ta fashe da kuka snn ta wuce wajen data ajiye maganinsam batare da ta kula janet ba tana daukar kwaryan kuwa taga ya cika da kumfa yay wani irin yauqi.

tsabar ta tsorata kiris ya rage ta sake kwaryan ya fadi akasa janet tay saurin karbewa taje ta zubar a sink snn ta dawo ta samu nur din a zaune tana kuka ahankli.

maganan duniya janet tay dan nur tagaya mata meya faru amma sai shiru sabida tasan babu kyau fadin mumman mafarki sai kuma tunda taga maganin ya lalace in reality ta gane cewa ba lallaine abunda ta gani ya zama mafarki ba..

sosai jikinta ya fara bata cewa koma miye aka cakke javeed dashi toh tabbas kmr blood oath ne akayi da jininsa da bakaken aljanu masu hatsari dan a mafarkinta gani tay tururuwa masu shegen yawa suna shigewa cikin ciwon bayansan sunata shan jininsa
da wani abu abakinsu kmar straw

janet harta gaji da lallashi da tambayr nur tay shiru dan dakyar nur ta dawo cikin hanklinta taje tay alwala tazo ta cigaba da sallahn darenta kamr yadda ta saba tanayi tana kuka dan a tsorace take sosai.

washe gari still ta tashi da azumi tun kafin kowa yazo taje ta sake nika ganyen guda bakwai tay repeating same process ta kara wankeshi dashi..

haka kuwa tay shiru bata gayawa kowa meyafaru jiyan ba janet ne tadan sulale waje ta samu ta gaya ma alhaj attah duk abunda yafaru wanda koda suka shigo sai baice ma nur din komi ba dake dasu anty suad suna dakin har saida ya fita ya kira hajya mammy yagaya mata
komi da nur ta gani

itace ta warware masa cewa bakaken aljanu ne suke bata ruwan wanka dan haka duk suyi hankli amma kar adena kulawa da wanka da kuma karatun qur'ani a dakin.

daga nan babu wani abu dayafaru javeed was stable, mr manny haryau bai kira hjy xubby ba sai cin karen su ba babbaka suke agaban su anty musmn da sukaga yau nur ta zama very quiet and alone tana yawan ware kanta da su duk damuwar datake dannewa sai ya fara nunawa ayanayinta sosai.

shide alhaj attah bai fasa neman mafita ba yayi nan yakira nan saidai komi na musu wahala ne sabida spritual prblems na famliynsu is compltely secretive koda ya samu masu taimakon ma bazai iya bude musu sirrin gidansu ba gashi mother hauwa datake daukar wann ragamar haryau bata fito ba komi ya taru ya masa yawa aransa ya tura sultan neman dr ruqayya but he is still feelling bad da yake ganin kamar nur tay karamar da zai sake mata komi duba da su anty suad yanzu sun fara muzguna mata awajen.
Chapter 122 · 0% Book details