← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 206

Sashe 74

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wajajen karfe 8 saura na safiya nur tafarka tanamai juyi jin wani irin qamshi da sanyin iska me dadin gaske dake ratsawa tacikin dakin nata wanda ko ba ace mata komi ba tasan fresh breeze ne daga waje yake hurata tanajin dadi danhar wani sauke ajiyan zuciya takeyi me nauyi tana kuma mika, sai can ta tuna ashe akan sallaya tabingire da baccin tanadan bude idonta afirgit ta kalleta akan tsakiyar gadonta ita kadai har an kashe mata Airmores an bude mata labulen window clean iskar private garden dinta dake tabayan windon ke shigowa yana fmr hurata ga wasu irin qamshin furanni masu sanyayaya rai dake tahowa aciki.

tattaba jikinta tay jin kominta intact snn tamike zaune da mamakin jin yadda hadadden qamshin turaren javeed din ya mamaye mata jiki tasan duk yadda akayi shine hala ya shigo ya dauketa daga kasan ya dorata akan gadon snn yabude mata windon dakin..

sosai ta lura da yadda yake daraja natural breeze akan iskar Ac kmr dan kowani safiya inbe ji natural iskan dake kadawa da asubhi kmr baiyajin dadi...

sauka tay akan gadon acikin tanayin kasala ganin kmr ita dayane kawai a dakin nan ta zabge kayan jikinta ta fada wanka wanda tun anan tafara tunanin me zatay da rayuwarta yau dan ta fara gajiya da zama awaje daya duba da abunda yafaru jiya yasa taji kamr bata son taje kara yin wani gaisuwa acikin gida kuma.

kafin nan ata dayan bangaren hajiya suad jiyan ana kammala sallan ishai ta shirya ta taho sama ta same yayanta alhaj attah a sashensa dan taji me zaice mata akan nur duk ta dauka zai bata haquri ne yabi bayanta

hajy zubby dake famar
waina ma'aikata tun jiyan ake ta shirye shiryen side inda yar uwarta simran zata zauna itama ta fito dan tagama sawa aranta cewa wnn karon zatay duk meyuwa dan wallh yar uwanta simran bazata bar gidan nan batare da sunci nasarar aura mata javeed ba.

sabbin halayyar nur dataganin jiyan ya nuna mata cewa zasu sha fama da ita hala ma intay wasa nan gaba yarinyar saitazo tafi javeed yin musu baqin hali.

tsabar gulma na cinta arai hakanan tazo falon kasa itama tanata bulaye tar da lady siddika dake zaune ta hakimce tana jiran fitowar anty suad tafito musu da gurmi daga sashen alhaj attah mufasa.

kusan awa biyu sukayi a zaune kowa yana latsa wayarsa ana jiran jin kanun labari kowadai nayi nadan babbarsawa.

Kawar Dr simran din ne ta kira hjy zuby ta mike da sauri zata je ta amsa wayar sai kawai sukaga anty suad tana saukowa da wani irin huci garaf garaf take tafiya dan tsabar zafin kai duhu duhu ma take kalla agabanta tafiya take kamar wacce zata tashi sama tsabar bacin rai idonta har yay jaa.

kallo daya zaka mata kasan masifeta akayi tassss tana sakowa ko magana bata musu ba tawuce sashenta fuuuuu tana tafiya tana xuba kukkuni.

da kallo kawai suka bita lady sid tay maza ta bi bayanta ita kuma hjy xuby tafita amsa waya awaje dan tun jiya akace mata wai simran tanata aman jini ana tsammanin mata ciwon zuciya.

ita so ma take ahadata da simran din awaya ta tsigeta tass dan saida tasha jan kunnenta akan ta rage muguwar son nan datakewa javeed amma sam takiji duk da uban karyan data mata akan yarinyar toh yanzu yake nan zatay intazo taga yarinyar karama ce kuma ma tafita kyau hmmm

tunda ta dau wayar ruwan masifa kawai take zubawa kawar simran din tana cewa ita babu ruwanta da wnn shashancin ciwon soyayyr kawai in simran zata warware ta warware kawai tazo gidan suyi abunda yake gabansu inkuma bazatazo ba ita zata cire hannunta aciki kowama yahuta

anty suad kuwa tana zama akan gadonta tafara karkada kafa tana wani irin huci wai har itace yaa attah zai kirata daki ya ja mata kunne yay mata fada akan wata yar kwailar yarinya da batakai ta hadiyeta ba?????tou wallh wallh ta qudira agidan nan kam inhar tana raye saita ga abunda yay karshen yarinyar nan altho deep within her heart tasan gaskiya yayan nata yagaya mata

yace mata ta kama girmanta tafita acikin wnn yarintar sabida ta riga ta manyanta bai kamata tabari yar yarinyar nan tazo tafara rainata ba, ita babban abunda ya fi cimata rai baifi cewa dayayi wai inta bari nur ta rainata agidan toh shi babu ruwansa ba toh ita nur din wayece da baza'a gyara mata zama ba yo shkn sai ayi shiru a zuba mata ido...???

duk dai zafin kai da haukarta tasani sarai walakancin yaa attahn nasu yaci uban aljanun dake kanta shiyasa da lady siddka tazo kawai saita fara bambami tana kawo wasu maganganu na borin kunya da neman sassautawa gudirin da sukazo dashi.

tasani sarai idan sukayi wani hauka yaa attah zai iya korarsu agidansa dan tun akan mahaifyr javeed suke tufka irin wnn rikicin dashi harma ya taba mata korar kare agidansan dakyar ta rokesa yay haquri

gabaki daya daren zagin nur firdaus sukayi tayi tare da kitsa wata hanya da zasu saka mata kahon zuka tunda masifa ne dai ba aso amata gata agida gata yar gata hmmmmmm

yau da safen dukansu sukayi tawaye basu ko fito tea palor ba daga hajy zubby sai mijinta suka sha shayi dama shi javeed bai fiye zama acikinsu ba ita kuma saffa saffa take binsa yanxu sabida yaune take saka ran simran zata dawo dolene tabishi ahankli tanason ace yanajin tausayin simran agidan itama.

daga bangaren nur kuwa tana fitowa a wanka ta samu janet har ta iso, cikeda girmawa ta gaisheta kafin nan tagama shiri acikin dakin shiryawn ta har janet ta gyara mata dakinta tsaf ta shirya mata wajen karyawa.

yauma light make up tay tasako irin egyptin gowns din nan na ciffon fari kal dashi bata wani kama sumanta duka ba ta barsa yadan zubo mata har gadon baya sai tayafa shararar farar veil akanta.

har saida ta kammala breafst din snn janet ta gaya mata cewa ai javeed yazo lkcin tana bacci yabada sako ace mata zaije abuja amma anjima zai dawo yabada dama janet tay keeping inta company har sai ya dawo.

hakanne ya bada nur damar gayawa janet din abunda takeso
dan tagaji da jan akwatinta idan zata daka kaya tanaso ne kawai ayi mata arranging kayanta
kuma tanaso ta fita ta zaga estate dinta kofa zata dan sha iska dan zaman dakin sosai yafara gundurarta danko sanin fasalin harabar gidan batay ba harynxu.

nan janet ta kira mr aqeel ta gaya masa bukatun nur, shikuma ya gayawa javeed sai kusan bayan awa daya kafin nan javeed ya amince mata akan tayi duk abunda taga dama in zataji dadi.

nan danan kuwa janet taje private workers estate ta kirawo wasu mata guda biyu daya personal chef ne daya kuma servant din nur like personal maid da zata dinga mata komi da komi.

tun kafin isowarsu janet tafara bata brief intell akansu, personal maid NAIMA wacce ta kwarance wajen iya saka ido wanda kusan duk wani sirrin hjy xuby ta sani sabida tsabar lurarta, she is very soft spoken and respecful amma tana da special skills wajen iya CID work, har skills na iya harbin bindiga tana dashi shiyasa ma javeed dakansa ya zabeta as personal maid na matarsa tun ma bata iso ba.

itace zatana tashin nur abacci, zata shirya mata kayan sawarta gyaran gashi, ruwan wanka da duk abunda take bukata na kula da jiki.

snn aikinta ne ta tsaftace duk wani abu daya shafe sashen nur daga kan qamshi goge goge, rooms nd palors, shiryawa da gyaran wadrobes da canza mata tsarin daki komi aikinta ne

snn zata tabbata nur tanashan magani sabida already akwai supplemnts da ake sawa acikin tsarin abincin gidan wa zallan mata sabida inganta kwarin kwan haihuwa, snn she wll monitor in and out movement snn intaga wani daban yana wani abu da be qansheta a sashen nur ba to zata kai report akansa akan lokci.

dayar matar Faiza kuma itace private chef wacce aikinta zallan planning da dafawa nur abinci ne a sashen, she is older tayuma takai sa'ar javeed din, tazo gidan lkcin tana karama da mahaifyatrta wacce itama tay aiki sosai wa mahaifyar javeed din as private cook

itadin ma bata da tsoro amma tanada ladabi sosai kuma tay gadon iya girki daga mahaifyrta data jima tana dafawa mahaifiyr javeed mufasa abinci.

she is very proud of her cooking skills dan daga javeed sai kuma ubansa kawai take musu special girki, aikinta baifi ta tsara nutrition chat ma nur firdaus ba wanda zai kawo karin lfya da kuma kara ingancin kwayayen haihuwa

kowani rana zata dafawa nur 3 main meals da two optional light snacks ensuring evryhing is fresh nd healthy, they have strick security akan mai girki dan ba akai abinci wa kowa sai anyi veryifyng din abincin shiyasa babbn kitchen din nur din yake jone da estate din javeed sabida babu inda yafi sashen nasa tsaro a gidan.

janet tagama bata labarinsu kenan sai gasu nan sun iso..

light skin naima ce ta fara rusunawa kasa da murya me sanyi tace Assalaamu Alaikum Hajiya ina miki sannu da zuwa ni sunana Na’ima Brigadier General assigned me to you directly. I’ll be your personal maid, My duties are to keep your space in perfect order, attend to your comfort, and ensure you’re never left unattended duk sanda kike bukatar wani abu ina tare dake Rankishi dade.

ahankli ta sunkuyar dakanta in humility.

nur ta kalleta da kyau ta gyada kai calmly batace mata komi ba.

sai ga nan Fa’iza ta karaso itama ta rusuna, tay sallama tace ranki shi dade hajiya I am Fa’iza your private chef. I’ve been cooking in this estate for sixteen years,

General yace lafyarki shine kan gaba so everything that enters your mouth goes through my hands dan Allah idan akwai wani abincin da kika fi so zanso insani, haka ma in akwai wanda baki so zanso in sani ko kuma naima zata sanar dani.

fuska ba yabo babu fallasa nur tace its okay.. dan shiru tay kafin nan ahnkli tace "na'ima, zamu fita waje da janet pls do sumting abt my wadrobe. da sauri naima tace angama ranki shi dade..
Chapter 74 · 0% Book details