← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 153 OF 206

Sashe 153

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

javeed yana ficewa a dakin nur ta dan gyara zamanta snn takure screen da ido, after like 3 minutes caraf sai ga fuskar Dr surayya ya bayyana tana kan gadon asibiti andan tallafo kanta da pillow....

da wani irin shock suka hau kallon juna muryan nur na rawa rawa tace "Anty?..

nan take hawaye suka fara tuntudowa idanunta kamar ruwa at same time tana murmushi ganin dr surayyan tana miko mata hannu cikin wani irin yanayin rauni da ragwabewa na mamkin ganin nur yadda ta wanku tay bul bul kamar ba nur din ba

kallon juna suke kamar a mafarki wanda ya zama babban surprise atsakaninsu duka ya kuma kara stimulating din kwakwalar Dr surayya dawani irin karfi ta kwaco speech dinta bakinta na rawa rawa tace n..nur..nu.. firdaus???.

a sulale cikin muryan kuka nur tace alhamd alhamdullh anty kin tashi??? da sanyin murya tace how are u feeling ya jikinki...i miss u soo much and i am very sorry mummy tacemin wai sandaniyata kika shiga cikin wnn halin Anty dan Allah kiy hakuri...

daga haka suka fara magana dr surayya tana ta rarrshin nur din cikinsu kowa na kuka dan nur harta mance da batun ciwo

jikinta duk yay sanyi dataga da kyar da wahala Dr surayyah take iya fidda magana asarari....

saida suka gama kukan snn dr surayya ta fara mata tambaya akan abunda yafaru cikin kuka nur firdaus ta soma bata labarin duk yadda sukayi da mrs haseena hartakai izuwa ga barinta abuja zamanta da kawunta da kuma aurenta da javeed mufasa, kiji tsoron Allah karki karanta abunda baki biyaba mutuwa koyau ko gobe dan haqin da kika raina saiya hanaki kwanciyat kabari 0806071224
chat me and pay

Arewabook@surayyahms
bangaren javeed kuwa
cikin sanyin nitsuwa tare da takunsa me cike da wata kalar tausashiyar kasaitar da bata fidda sautin hayaniya saidai na iko da kwarjini a idon duk wanda ya daga ido ya kalleshi a bugu daya ya sauko kasa lkcin just few minutes ne kawai ya rage su mother su karaso.

tun da yaji gidan ya dau wani irin shiru yay harsashen hala dukka anhallara ne a babban falon anata jiran lokaci.

tafyarsa yake anitse saida yaxo daf snn ya kalli daya daga cikin servant masu gadin kofar site din ya mika mata katon parcel din da bedsheet dinke ciki wanda akwai dan karamin note me dauke da handwriting inshi da kuma rose flower yace mata taje ta ajeshi akan gadon anty suad tabarshi awajen...

babu bata lokci servant din ta karba marmaza takai dakin anty suad ta bawa private maid inta daga kofa aka aje mata akan gado snn ta fito.

bata jima da fitowar ba sai ganan anty suad din ta bude kofar bathrum dinta tafito tana tafiya ahnkli fuskarta a mugun dore alaman kmr daga kashi ta fito..

gashi ta sha wani irin wanka da smooth designer saki material na manyan mata an mata wani irin classic bubu gown da aikin hannu yay mata kyau dan irin shiny golden colour din nan ne sai qamshi takeyi banda uban baxa capacity na wasu mayun diamond jeweries data sakasu tun daga kunne har wuya da hannu suna baza kyalli.

wani dan uban ciwon ciki ke neman ya sako ta agaba mehade da tsurewar ciki shiyasa duk abunda akeyi agidan itace kawai bata samu daman fitowa waje ba tukuna amma dake yau ranar korar nur ne she wont miss it for the world gashi ance mata mother suna daf da isowa tanata sauri sauri danta gama ta fito atarbe su duka atare.

hand cream ta dauka akan madubi ta shafa shi hannunta ya kara laushi snn takara fetsa turare har zata bar dakin agaggauce kenan idonunta suka sauka akan parcel dake kan gadonta kamar wanda aljanu ne suka aje mata shi.

wani rau tay da ido tana yatsina fuska cikin rasa uban waye yay tsaurin idon aje mata wann abun dan lady sid dai ba irin matan nan bane da suka saba da aje mata kyauta

a mind inta tace kode zubaida? kai kai tace a'a, basa wani shiri da zubaida, toh hala saidai marar kamun kai dinnan simran dan tasan yarinyar bata da aji ko kadan, gashi dai bata kaunar nur anma kuma tsanar datake ma simran aranta yafi yawa dan yarinyr bata mata ba kwata kwata saidai dayake ta lura simran din jakar mace ce yasaka dolene ta rufe ido tay amfani da ita yanxu dan kawar da wacce take ganin kmr zata iya bata ciwon kai a ahalin mufasa nan gaba.

aranta ta gama gane cewa nur yarinyace me farinjini, ilimi ga nitsuwa ga addini ga kamun kai gata yar karamar yarinya danya shataf kuma kyakkwar gaske wanda babu shakka ta cancanci zamowa mata agidan mufasa, saidai babban tsoronta shine daga zarar nur firdaus tafara xubawa javeed y'a'ya toh shkan fah ahalin mufasa ya dawo hannunta kenan na har abada saidai nasu yayan sucigaba da zama akarkashinsu kai dole ne fa yarinyar nan ta tafi....

ga nan simran who is age and career perfect figure wa javeed but she damn dull and classless saidai tunda ita tariga ta fara tsufa wayasan ma ko cikin javeed din bazata iya dauka ba shiyasa tasan plans dinta bazai fadi kasa inya aure simran din ba.

..da wani irin karamin tsuka tareda cigaba da saka abubuwa aranta takaraso kan gadon snn tasaka hannu tadauke parcel din tayaga seal din wanda tana budeshi idanunta ya sauka akan very fine hand writing din javeed da rose flower akai duk qamshin turaren sa ya kama jiki.

jikinta har na rawa tadaga paper dataga an rubuta"..Shame is heavier on the lips that accuse than on this sacred bedsheets you demanded from a virgin."

yatsina fuska tay a mugun jirkice tace what? a virgin? wa kenan...mtss this cant be

adame takara karanta note din da karfi lkcin rawa rawa ma hannunta yafarayi jin kanta ya kulle sosai da wani irin zafin kai ta fixgo bedsheet din waje tayi firo da parcel din snn tahau warwarewa agaggauce kirjinta harna bugawa.

tana cin karo da stain din jinin kuwa tarike bakinta dake bari-bari tare da saka salati me mugun karfi sai kuma tafara girgirza kai tana cewa no no no dis cant be da alaman bata amince ba atake kuma idanunta yay jaaaa sosai kamr wacce zata rushe da kuka taji ta rasa abunda ke mata dadi dan tasan javeed baya wasa da kowa dan haka zaiy wuya ya musu karya,..

he wont just say things just like that, kallon stain din dake kan bedsheet din ta dingayi tana girgiza kai tana fidda zazzafr numfashi sama sama kamar sabuwar kamu ahauka jin wani gullutun baqin ciki me radadi ya kama mata kirji yana neman ya shaketa

a ragwabe ta saki zanin gadon ya fadi kasa itama tun daga sama ta zauna agado dubuss tana jin inama ace da bata gayyato su mother da kowa da kowaba dan dai tasan tunda javeed ya aiko mata wann abun hala wani babban abun kunya da toxarci ne ya shirya mata agaban mutane saikuma taji ta rikice sosai duk da masifartan nan saida wasu zafafan hawaye suka cike mata cikin idanunta atake dan ta tsani ace ta fadi abu badaidai ba. gashi ta saka rai, hala mother zata saka baki a bawa danta kamil ragamar rike komi na ahali dake hannun javeed ko da na wucen gadi ne dan kawai ta samu access na debar wasu rare diamonds daga can kamfaninsu na congo tay wasu harkallnta da su.

jajayen idanunta dake fidda ruwan hawayen fushi da takaci tabi ta rafka uban tagumi ta zubawa bedsheet din ido cikin rasa ya akayi hakan yafaru yarinyar da aka mata ciki har ta zubar how she is now a virgin gaskiya hakan bazai taba yuwa ba,mikewa tay kamar wata soja ta share hawayenta tabi ta hade rai cos once beaten doesnt shy zataje taji wani uban makircin aka hada ake neman wanke nur dan bazata taba zuba ido yarinyar nan ta zauna musu agida ba.

bathrum ta koma dan ta wanke fuskrta

daga main falo kuwa cikin sanyin taku me tafe da kasaita javeed ya karaso da mamaki saiya samu babansa ne kawai anan yana waya shikadai..

baiko zauna ba ya tsaya babansa yana gama amsawa ya rusuna ya gaishe sa yabi ya hade rai baice masa komi ba shima baice masa ba sai da sukaji dirin isowar su mother a jirgi tare da convoys na fararen luxurie cars me shake da security da kuma sauran yan ahalin da basubi jirgi ba.

alhaj attah yanata mamaki da baiga fitowar yar uwarsa suad ba dama kuma su ukun ne zasu tarbe mother koda ya kira lambarta yaga bata dauka ba kawai sai suka fita wajen shida dansa javeed dake binsa abaya...

kusan lokaci guda jirgin mother ya sauka tare da convoys na RR da sunkai goma sha biyar..

hajy Amira mufasa, kamil mufasa, da khaleefa mufasa sune suka sauko daga motocinsu ayayinda da sheik haidar Ali ya riko hannun mother daga jirgi suka fito kan step na jirgin ahnkli

dake sheik Ali haidar mufasan ya fi kusanci da mother ya saka kusan koyaushe shine atare da ita..

they are all dressed in the most expensive and sophiscated modest haute wears hatta mazajen sun rufe jikin su kirif saidai kowa da design insa mother ce kawai ta saka fararen kaya.

suna karasa saukowa kasar step javeed da mahaifinsa suka isa gaban mother dake takawa ahankli sabida tsufa..

alhaj attah ne ya fara rusunawa kasa yahau gaisheta da hanya snn javeed ya dan haura saman step din yariko hannunta gently cikin nashi da tsananin nuna darajawa yana mata maraba da zuwa dan kamar kaka take musu mother ta tsufa sosai jikinta ne kawai yakeda sauran kyansa

tunda taga kowa yaxo ya mamaiyeta taketa murmushi dan kowa acikinsu yazo anty suad din ne kawai bata nan..

within few minutes suka doshi cikin gidan mother tadan jingina ajikin javeed dan harga Allah tafi jin kaunarsa aranta fiyeda kowa shiyasa ma tafi saka ido akan rayuwarsa harma tace zata zo...

they all look okay and normal kamar ba case din nur akazoyi agidan ba.
Chapter 153 · 0% Book details