← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 206

Sashe 96

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tambayoyi kala kala nur kesha a hannun anty suad gameda iya girki wani tambayr ma kamar kayi mata kuka dan gabaki daya taraina zancen cewa wai nur ta iya girka abinci aganinta ai nur tay karama bazata iya komi ba.

ran nur sosai ya hargitsa ya baci da kalar rainin wayonsu shiyasa batako dago kanta sama ba dan in banda presence din alhaji attah da Allah kadai yasan kalar munanan amsar da zata bawa anty suad amma hakanan ta daure tay shiru jin alhaj attahn ma yana kareta.

shigowar hajya zuby wajen ko minti biyar baiyi ba saiga naima tazo, kowa acikinsu da mamaki ya kalleta sanin cewa basu da hurumin zuwa har nan. fadi tay harkasa tana miko musu gaisuwa, nur na juyowa tabaya taga jikin na'iman na dan rawa rawa itako sai wani irin kallon matsuwa take ma nur dan zuwa tay dama tace ma nur din taje ta hana javeed shan smoothie din sabida tay lissafinta kafffc ta gano cewa tabbas dolene akwai abinda simran tay wanda basu gane ba.

aka tambaye naima meyaka wota tace tana so tay magana da hajiyarta ne its very urgent..

Hajy zuby tama nur kallon sama da kasa tace toh hajya, tunda su anty sun gama ai saiki bita kije..

nur tay musu sallama fuskarta ba asake ba tawuce waje na'ima tay saurin biyota abaya.

suna fita tun a kofa jikin naima da bakinta har na rawa tace ma nur ita tana ganin kamar akwai wata matsala amma kafin tagaya mata kawai subar maganan tay sauri taje ta hana general shan smoothie din nan.

kan nur sosai ya kulle tafara ma naima tambayoyi amma haka naima ta dinga matsawa saidai suje sama da sauri.

a hujajan ta sako nur agaba suka wuce sama sashen javeed wani irin tashin hankalin da naiman ta taso dashi na cewa tana suspecting cewa anyi poisoning din smoothie din yasaka nur sai takejin kirjinta itama na bugawa da mugun karfi..

da matsanancin sauri suka haura suna isa kofar dakin yay dede da lkcin da Mr aqeel ya fito da wasu files a hannunsa kenan zai fita cikin sauri ganin tahowarsun yasaka ya tsaya bai kuma kulle kofar ba.

kirjin nur na bugawa sosai bata tsaya amsa gaisuwarsan ba tashiga dakin da wani irin sauri kamar zata ci da baki babu ko sallama tayo gabansa da niyyar dauke cup din sai taga wayam

ita kanta janet sai da ta tsorata dayanayin yadda nur ta shigo tafara cewa hajiya lafiya? naima ta tsaya da sanyin jiki kusa da janet din suna kallon ikon Allah

nur na kallon javeed dake zaune akan kujera sai kuma ta gwalo idonta wajee cikin matsanancin shock ganin wai harya shanye a mugun kangare take kallonsa jin bai mata magana ba da sauri ta karaso kusa dashi sai taga ya daga kansa da kyar ya zuba mata idanunsa anata wani karamin murmushin ya kufce masa cikin numfashi taji yace Baby..?????bakinta na rawa rawa tamiko hannu zata rike masa hannu tana tabashi kuwa sai taji mutum ya sulale ajikinta ya dauke numfashinsa cakkkk.

lkcin ji tayi kamar an cakketa da mashi a kirji dan batasan ma ta danna ihun sunan sa da bata taba kira in full ba. fuskansa ta dinga tattabawa a rikice waiko zai tashi tana ihun sunan sa javeed javeed javeed javeed pls cikin kukan da batasan ma daga ina ya fito ba ta rikesa jikinta na rawa sosaiii.

jikinsu janet na wani rawa rawa ita da naimar abayanta duk sun rasa nayi sabida komi ya farune kamar kiftawar ido..

dakyar janet ta daga wayarta tafara kirar private emergency doc na javeed din wanda ta kasance abokiyar mum dinsace na kud da kud layin nata ringing amma ba adaga ba.

kukan da nur take tana ihun sunansa tana jijjigashi ya rikitasu gabaki daya

a rikice mr aqeel ya sauka da sauri kafin kace wani abu ayarin gidan kaf sunzo dakin a rikice
simran ne kawai batazo ba

nan akafara kace kace anata tambayar nur meya faru ita kuma kuka kawai takeyi dan bata gane komi ba

ana kkrin dagashi zuwa private medics na gidan sai ya farka ya fara wani irin tari tari sai kuma ya fara zuba amai gabaki daya smoothie din dayasha ya fara fitar dashi waje daga jikin shin harna nur duk saida ya lalace dake duk ihun tambayan nan da su anty suad suke mata tana rike dashi tana kuka sosai bata sake shi ba

har saida ya gama aman kafin nan tacire dankwalinta da sauri tashare masa bakinsa tass da dan kwalintan snn tabashi clean ruwan gora yasha kadan cikin maida numfashi babansa ya tayata dagashi suka maidashi kan chair ya dan zauna tare da lumshe idanunsa sosai.

kowa na masa snnu sannu amma bai amsa ba yay shiruu
yana maida ajiyayyen numfashi

Dayan likitansu da mr aqeel ya kirane yafado dakin ya fara ayyana masa gwaje gwaje da tambayoyi janet tace ai baici komi yau ba banda protein shake da safe da sai kuma wann smoothie din. dake kwararen likita ne saiya daga cup din ya dubba sai kuma yace musu ai dolene akwai wani abu da yay irritating jinin javeed acikin smoothie din nan maybe is a case of fruit alleggies dan hakan ayi hankli san samu
ma kar asake bashi irin wnn smoothien. hankli tashe alhaj attah yace amma ai bawani matsala ko? with full assurance likitan yace masa ehhh bawano abu ai jininsa ne kawai bai karba ba shiyasa ya amayar tun ma bai zauna masa aciki ba.

likita na ficewa nur dake hawaye ta taho da sanyin jiki tadan tsuguna agaban javeed din tafara bashi hakuri tana dan kuka kanta akasa sosai zakaji tabaka tausayi.

dan dagowa dayay agajiye ya kalleta da murmushi ya shafa saman kanta gently snn yace mata babu komin...tuni ya hatsala anty suad wanda kamar an kunnata ne tafara ihu da masifa da zage zage tace sam nur tay komi ne acikin ganganci da mugunta zata kashe musu dansu da abincin shirmenta ai dama saida tace bata iya ba gashi tazo tana bashi food poisoining..

ta inda take shiga bata nan take fita ba .

nur ma tsugune agaban javeed sai kuka marar sauti kawai takeyi jin yarike hannunta cikin nashi dam dam yana murzawa ahankli saidai baicewa komi sabida koba komi ita kanta tasan aman yadan jigatashi tunda har ya dauke masa numfashi

lady siddika ma ta amsa caraf suka dinga zagin nur da wani irin baqaqen maganganu kamar dama wannan daman kawai suke jira a rayuwarsu...

da abun yay yawa ne jin sautin kukan nur din yafara fita sosai alhaj attah ya dago kai daga kallon lumsashen idon javeed din dayakeyi cikin mugun jin tausayin nur yahau tsawatar musu yace musu kawai su fita a dakin su basu waje ko wanka ma javeed din ya samu yayi tunda likita yace bakomi.

bada son ransu ba suka kama hanya fuuu suna fita hajy zuby tafara jefa ma alhj attan baqr magana cewarta aidama tafada masa yaqi ji nur sam bazata iya komi ba dama shegen zalama ne da makirici yasa ta amshi komina gidan ta rike, Allah ne ya sakawa simran, tadinga kukkuni baiko kulata ba har suka sauka kasa.

kai kace maganan ya kare amma ina su ukun hakan suka mamaye alhaj attah kowacce tana dirin buhun masifa da kalar zagi na tsana da suke furtawa akan nur dan sunsan alhj attah baiya wasa ko kadan da ran dansa.

a tunanin su ranting dinsu ma kadai ya isa yasakashi ya saka strict sanction ma nur a gidan amma inaaaa shikuwa kalamn su kawai yaketa aunawa ya lura da cewa dama tuntuni da wasu abubuwa aransu akan yarinyar

cike da taurin zuciya tareda basu mamaki yace musu shi a matsayin kuskure ya dauki food poisoining, dan kowa na iya fadawa akansa, snn yasan nur kam bazata taba bawa javeed abunda zai kashe sa ba bare ma aiyanxune suke sanin juna so is part of marriage experience dan haka kardama yasake jin wata acikinsu ta dago da wnm maganan snn nur will remain in her position shi babu ruwansa da wani rashin hankli.

tunda ya balbale su ya tashi ya fita,bacin rai yasaka anty suad kasa furta komi ta haura sama itama a mugun fusace dan gani take saboda hajiy mammy ne yasaka alhaj attah baison yaga laifin nur kwata kwata

mamakin furucinsan ne ya rufe hjy zuby da lady saddika suka tsaya a falon kamar gumaka daga mai uhmm sai uhmmm uhmmm.. dan dai iya zamanta dashi tasan ko awasa wani ya taba ran javeed toh tabbas nashi a gidan ya kare kenan.

da wani irin karayar zuciya tareda matsanncin bacin rai hajya zuby taja kafafunta da ke mata mugun nauyi ta koma sashentan itama

simran ce tay kamar batasan mayake faruwa agidan bama bare ayi suspecting inta da wani mugun abu dan tsabar tsoron abunda tay tanajin yunwa amma hakanan ta haqura da abincin taki fitowa.

Ata fannin su nur kuwa bayan angama ficewa a dakinne ta sallame su naima da janet tace suje kawai harsai ta nemesu.

suna tafiya dakanta ta tsaftace wajen lkcin kansa yana lafe akan kujera yana kallonta har ta gama snn tasamu ta shiga bathrum dinsa ta hadamai ruwan wanka tazo tacemai suje cikin yay wankan.

kirar sallahn magrib yasaka kawai yamike tsaye yana shiga wajen wankan tabi bayansa ciki tafara tayashi cire buttoran gaban rigarsa har ta gama shikuma yacire na dogon wandon kafin ya sauke kasa matsanancin tsoro da kunyar ganin gabansa yasaka ta dau kayansan da suka baci tay maza tafita dashi waje kafin ta dawo tasamesa harya shiga cikin bathtube din yazauna acikin ruwan data hada masa dagashi sai wata farar gajeren wandonsa da ko rabin cinyarsa batakai ba.

duk uban tsoron dake taba mata kwakwalwa intagansa zarr namiji babu kaya agabanta hakanan take danneshi snn ta taho gefensa basuce ma juna komi ba sabida yadda ya lunshe idanunsa sosai da alaman baison magana.

yanaji ta dau lallausar soson ta jikashi da gel din wanka me qamshi yay kumfa tafara goga masa ajikinshin ahankli ahnkli
harta gama wanke shi baice mata komi ba...
Chapter 96 · 0% Book details