← Book details Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 206

Sashe 48

Nur Firdaus Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk yadda take mugun jin tsoron rasa shi da tsananin kishin javeed har yanxu wani bangare na brain dinta ce mata yake karyane badai javeed dinta bane zai mata haka saidai in wani javeed din ne daban koma hala yan biyu ne taya ma xata tabbatar da haka??

soyayyarshi ya riga ya mugun shigarta da har ynxu gani take duk wann batun karyane bazai ma taba yuwa javeed dinta yazaga ta snn ya auri yar uwarta razia ba.

sai can data gama kukan tareda nazarta komi acikin zuciyarta tareda da kin daukar komi aranta kafin nan tafara magana tace akira mata kawunta ita zataje gida..

hajya bilqi ne dama agefen gadon razia
tarafka tagumi sai ga nan hajy sa'a tashigo a harzarce tace hajya Billy kifito likita yace nur firdaus tafarka tana neman mu Alhamdullhi..

azabure hajy bilqin ta mike tsaye itama tana furta Alhamdullh nam tay marmaza taja mayafin ta tabiyo bayanta suka wuce dakin ICUn su uku anan suka samu nur akwance tana kuka ahankli..

ficewarsu keda wuya razia ta dirko kasa da ga kan gadon tabiyo bayansu saidai koda tazota bakin kofar dakin ICUn kasa iya budewa tashigo ciki tay dan batasan da wani irin emotions nur zata farka ba.

daga ciki kuwq rufuwa iyayane sukayi akanta kowa na mata sannu harsaida sukaso bata tausayi sai kallonsu kawai takeyi tanata gyada musu kai ahnkli hawayenta na sauka a fuskrta kamar ruwa.

da muryanta dake fitowa dakyar tace musu ina anty razia?

hajya bilqi tace mata ai razia nacen kwance dan tun da fito da ita a ruwan itama ta razana ta suma bata farfado ba..

jin hakan yasaka nur tafara kkrin zata mike

alhaj abbakr yakasa iya daurewa yarikota dam ajikinsa dan ya matsu yaji meyene ya faru snn ya akayi ta fado tun daga saman 3 storey bulding ta fado acikin wnn uban ruwan wnda shikansa ya tabbata da akasa tafado da saidai a dauki gawarta..

muryansa a raunace yace "Ina kuma zakije auta?? jikinki fa babu karfi dan Allah koma ki kwanta kinji..

cikin muryan kuka nur tace baba inaso naje wajen anty razia ne i knw she must be worried ni fa wallh bansan zan fadi acikin ruwan ba..

rukota yay ajikinshi araunace sannan ya rungumeta sosai jin ta kara fashewa da kuka me tsuma dan ita kadai tasan me takeji

but she want to deny everything and act like she is okay..danma kar ya zama mata gaskiya dan harga Allah ji take kamar bazata iya jure zafin rashin javeed a wann karon ba..

alhaj dake rike da ita yafara rarrashinta yana cewa karki damu razia will be fine and she did evrything a sister wud do, she saved ur life..

cikin kuka nur tace mishi i know she wll daddy shiyasa nake so naje wajenta i want her to knw i am fine.

Razia dake manne da jikin kofar tawaje kuka takeyi har tana jan zuciya very silently ruwan idanunta a lumshe sosai dan kwata kwata batay tsammanin da wann furucin nur zata farka ba,for a minute har tay tunanin nur zata iya jin ma ta tsaneta sabida tasan tagaya mata cewa zata aura mata saurayi, she tot ta kira iyayenne dan tagaya musu komi dayake faruwa sai kuma taji nur bata furta komi ba
face damuwa da ita datayi..

abun ba zallan mamaki kadai ya bata ba har daure mata kai yayi sosai...

jin anata rarrashin nur din aciki yasaka ta dan sassauto da nata kuka snn ta turo kofar ahankli ta shigo ciki

kusan atare iyayen suka jiyo suna kallon ta da mamaki suna hade ido da nur ta taho da sauri suka rungume junansu ahnkli suka fashe da wata ssanyar kuka ahankli take shafa kanta tanamai bata haquri wanda dagaji kasan razia ta tsorata

shiru iyayen sukayi suna kallonsu hajy bilqi da hajya saa duk sun raunanta sunata hawayen suma..

nan razia ta tallabo fuskr nur hawayenta na zuba tace litle sis dan Allah dan Allah kiyafemin i am really sorry i shudnt hav....

tun bata karasa ba nur ta girgiza mata kai tace "an razzy u did nothing,.. its all my fault, i just freaked out over nothing....wani irin kallo me cike da sakoni take ma razia alaman bata son suyi maganan javeed anan agaban iyayen nasu...

Koda alhaj yafara musu tambayoyi yawanci nur ce ke amsawa razia sai kallonta take tana mamakinta sosai..

ta rasa har yaushe yarinya karama haka take da irin wann karfin zuciyar danne komi a lokci guda
sai kuma ta tuna cewa zai iyayuwa kwakwalr nur firdaus da kuma zuciyarta ya saba da daukar ire iren wann pain da shock din shiyasa jikinta yay developing pain nd trauma control da kansa.

tanaji nur tace ma baban nasu cewa ai hira sukeyi sai jiri ya kwasheta shikenan bata san ya akayi ta fado ba she made razia look like a hero aka wuce wajen.

ranqr sunga gata a asibitin dan kuwa duk wani abu dasuke da bukata shi ake musu
banda ma nur da ta nace zata je gida da sai bayan kwana biyu za'a sallamesu..

a dakin nur din suka kwana cikin daren washe gari likitoci suka dubasu da snn aka basu wasu drugs wajajen 8:30 am na safiyar suka dawo gida kowacce ta wuce room dinta da nauyin abubuwan dake ranta

already alhaj abbkar har yasaka anyi pool drill anyi draining dika ruwan pool din an sake rufeshi.

nur tunda taje daki take bacci sabida allurai da aka mata bawai dan tana da niyyar baccin ba.

razia kuwa kasa yin komi tay tanata jeka ka dawo da tunani kala kala a cikin ranta
tarasa me nur take nufi da rufe maganan

tsabar damuwa dacan har zata kira molly ta gaya mata koda mata zata samu wani mafita tawajenta amma kuma data tuna yadda mollyn take da negative thinking akan nur sai kawai tariqe komi aranta da tsananin tausayin nur datakeji kamar zai fasa mata zuciya.

dakyar tay wanka ta sha ruwan zafi waidan ma su hajya saa sun sakota agaba da cewa tay harse nur ta farka kafin su saka wani abu acikinsu tare,

anan ma iyaye mata sunta mata questions akan hirar da sukeyi daya jawo har nur ta fada a ruwa amma haka razia ta musu wala wala tace musu hirar film ma sukeyi kawai jirine ya kwashi nur din ta fadi befr she cud catch her shiyasa ma ta tsorota sosai.

tun daga nan sai maganan ya mutu
suka fara tunanin yadda zasu kula da nur sabida shirin auren razia da mufasa cannot be stopd gashi basuda wani lkci.

ata dayan fannin kuwa
gabaki daya javeed ya rasa meke masa dadi
yana zaune shirune a room dinsa amma jininsa taciki tafarfasa takeyi musmn da aka kawo mai labarin cewa nur ta fado daga saman bene izuwa cikin ruwa ta suma..

sosai jikinsa ya bashi possible abunda zai iya faruwa,..

haka ya dingajin bacin rai da fusata taciki dan kamarma yaje gidan kawai ko ya saka men dinsa su dauko masa ita ya kula da ita dakansa haka ya dingaji, saidai kuma ba abune wanda zai iya risking yinshi yanxu sabida yasan safetyn rayuwarta is more important dan duk wani fushi da haushinsa da zataji yanxu.

haka sultan ya dinga satar kallonsa baice masa komi ba dan shikansan so yake yaga wacece nur fiedaus din nan ido da ido ganin javeed yake mata wani irin son da
shikansa bai isa ya kiyasace yawansa da zafinsa ba.

ranar gabaki daya daga kan sultan din har qurds din baya baya sukeyo dashi sabida mugun mood
swings da anger prblm dayake fama dashi,abu kadan sai ga ransa ya baci sosai akai, dan ji yaje kamar yay tsuntsu yaje yaga ya nur take, he almost cant bear to see her hurting tunma bai tabbatar da hakan ba.

bayan komi ya lafa
razia da kyar ta sake yin wanka tasaka wani dogon riga tanata kallon time sabida ta matsu nur firdaus ta farka suyi kyakkwan magana akan lamarin sede duk sanda ta lekata sai taga har yanxu tanata bacci

hanklinta dada tashi yakeyi idan tazo ta leka taga tears din ta na saukowa silenty ko acikin baccin, ga wani irin nannauyar jan zuciya da sheshhkar kuka datake yawan saukewa sosai razia tadamu dan tariga tasan dolene nur firdaus zata shiga wani irin mayuwacin hali akan javeed ganin bazata iya daurewa ba kawai tay deciding zataje room dinta ta dau waya ta tura ma javeed din sako game da halin da nur take ciki ata inda tasan hala zaigani cos she just cant bear to see her sister hurt.

tafice a dakin kenan bada jimawa nur ta farka da wani irin ciwon kai me tafe da zazzafar zazzabi ga wani irin ciwon ciki da azaban yunwa dake murdata.

ta jima akwance tanaji kamar ba ita bace for a moment tanamai dada tursasa brain inta da zuciyarta dan karma ya amince da gaskiyr lamarin.

kai koda gaskiya ne tasan bai dace ta dagawa razia hankali ba batare da taji zancen daga bakin javeed din shikansa ba.

wayarta tajawo tasake gwada lambarsa still baya zuwa, ta yi dialling lambr yakai sau goma gabaki har daya jikinta ya raunata hawayenta na zuba nan da nan ta hau rubuta masa sakonni ajere sai da ta rubuta masa sako yafi guda takwas amma duka babu wanda yaje bare tay tsammanin samun amsarsa.

jingine kanta tay da jikin gado ta dinga kuka danji take kamar kirjinta yana tafasa zai faso waje yay bombinh ya tarwatse dan ko kadan batasan zafin soyayya ba sai akansa ji take kamar yanxu ne tasan me akeji in za'a rasa masoyi..

she tried her best to convince herself cewa komi karyane bazata kuma yanke wani hukunci ma javeed ba har sai shi javeed din ya gaya mata da bakinsa cewa razia yake so zai aura ba ita ba..

daga haka tamike da kyar ta sauka akan gadon jin koinanta ya kage da rauni sau kuma takoma kan kujera tazauna ta dan jingina kanta kadan sann ta lumshe ido tafara tunanin last words dinsa da sukayi waya ranar birthdayn munayayya.
Chapter 48 · 0% Book details